Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Yaƙin Iran: MDD ta ce kayan abinci ya yi tashin gwauron zabbi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar ɗinkin duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin da ya daɗe bai yi ba tsawon watanni shida da suka wuce, kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da tashi idan yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ci gaba.

    Babban jami'in tattalin arziki na hukumar kula da abinci da noma na Majalisar ya ce hauhawar farashin mai ne babban abin da za a ɗora wa alhakin karuwar farashin abincin zuwa yanzu, amma ya yi gargaɗin cewa katse samar da taki da wasu muhimman kayayyakin noma na iya ƙara ta'azzara lamarin.

    Wakilin BBC ya ce kashi uku cikin ɗari na muhimman sinadaran da ake haɗa taki da su na bi ta mashigar Hormuz.

    Ƙasashe da dama sun baiwa ma'aikata umurnin yin aiki daga gida,kuma sun ƙara farashin man fetir, sakamakon yadda hana wucewa ta mashigar Hormuz ya hana su shigar da mai da iskar gas cikin ƙasashensu.

  2. Za a gudanar da gagarumin taron Musulmi a Paris

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a gudanar da wani gagarumin taro na Musulmi a Paris kamar yadda aka tsara, bayan wata kotu a Faransa ta ƙi amincewa da yunƙurin gwamnati na hana yin shi.

    Ƴansanda sun ce taron na kwanaki hudu da ake yi duk shekara na tattare da barazanar tsaro, kuma ƙungiyoyi masu tsatsaurar ra'ayi na iya kai musu hari.

    Masu shirya taron sun ɗaukaka ƙara cikin gaggawa, kuma sa'oi kafin lokacin da aka shirya fara taron, wani alƙali ya amince da cewa babu isassun shaidun da za su sa a hana gudanar da taron.

    A shekarar 2019 ne aka yi taron na ƙarshe, wanda dubban mutane suka halarta.

  3. Uganda ta ce ta karɓi rukunin farko na mutanen da Amurka ta kora

    Uganda ta ce ta ƙarbi rukuni na farko na mutanen da Amurka ta kora, ƙarƙashin yarjejeniyar da suka sanya wa hannu shekarar da ta gabata.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce mutanen su takwas waɗanda duk ƴan Afirka ne, sun isa Kampala a ranar Laraba, bayan wani alkali a Amurka ya amince da korarsu.

    Sai dai ƙungiyar lauyoyi ta Uganda ta bayyana hakan a matsayin abin da ya saɓa wa doka, kuma tana shirin kalubalantarsa a kotu.

    Tuni dai Amurka ta kori gomman mutane zuwa wasu ƙasashe, ciki har da Ghana, Sudan ta Kudu da Eswatini.

  4. Jirgin Faransa ya wuce ta mashigar Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin dakon kaya mallakin Faransa ya wuce ta mashigar Hormuz.

    Ana ganin wannan ne karon farko da wani jirgi da ke da alaƙa da Nahiyar Turai ya bi ta mashigar tun bayan da Iran ta hana jirage da dama wucewa saboda yaƙi.

    Zuwa yanzu masu jirgin basu ce uffan ba, kuma zuwa yanzu ba a tabbatar da yadda suka samu damar wucewa ba.

    Rufe mashigar da Iran ta yi ya kawo cikas ga fitar da danyan mai daga yankin Gulf, lamarin da ya sa farashin makamashi ya yi tashin gwuaron zabi a duniya.

  5. Ma'aikatan kamfanin Seplat Energy a Najeriya sun shiga yajin aiki

    Ma'aikatan kamfanin samar da mai da iskar gas mafi girma a Najeriya, Seplat Energy, sun shiga yajin aikin sai baba ta gani, wanda zai iya kawo cikas ga samar da mai da iskar gas.

    Jami'an ƙungiyar ƙwadago sun ce ba a yi nasara ba a tattaunawar da aka yi kan biyan ma'aikatan hakkokinsu da kuma walwala, wanda ya tilasta musu shiga yajin aikin.

    Kamfanin Seplat ne ke samar da kusan kashi bakwai na man da Najeriya ke buƙata.

  6. Wane ne Alex Babir, Ba'Amurken da ake zargi da ingiza ƴan Najeriya su ɗauki makami

    Bayanan bidiyo, Wane ne Alex Babir, Ba'Amurken da ake zargi da ingiza ƴan Najeriya su ɗauki makami
  7. Abin da muka sani kan jirgin yakin Amurka da aka kakkaɓo a Iran

    • Rahotanni sun ce an kakkabo jirgin yaƙi ƙirar F-15E na Amurka a kudancin Iran
    • Kafar watsa labarai ta CBS ta ce dakarun Amurka sun kuɓutar da ɗaya daga cikin matuƙa jirgin wanda ke da mutum biyu da ke tuƙa shi
    • Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt ta ce an shaida wa Donald Trump batun jirgin da ceton matuƙin
    • Kafafen watsa labaran Iran sun rawaito cewa hukumomi sun sanya tukwicin fan 50,000 ga duk mutumin da ya kamo matukin jirgin da aka kakkaɓo ɗin da ransa.
    • Rahotanni sun nuna mutum ɗaya aka ceto amma babu bayani dangane da ɗaya matukin
    • Babu cikakkun bayanai dangane da kakkaɓo jirgin
    • Ba mu ji daga Trump ba ko kuma hedikwatar tsaro ta Pentagon
  8. Kakakin majalisar dokokin Iran ya yi wa Amurka sha-guɓe kan jirgin da aka kakkaɓo

    ..

    Asalin hoton, Mohammad Bagher GhalibafImage source,NurPhoto via Getty Images

    Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi wa Amurka ba'a a shafinsa na X bayan rahotannin da suke cewa an kakkaɓo wani jirgin yaƙin Amurka da ke shawagi a Iran.

    “Bayan samun nasara a kan Iran sau 37 a jere, yaƙin da ba su san yadda zai ƙare ba ya koma daga kururuwar sauya gwamnati zuwa cigiyar matuƙan jirgi," kamar yadda Ghalibaf ya wallafa.

    Galibaf ya kuma yin sha-guɓe cewa "Kai. Ana samun gagarumar nasara. Mutane masu basira."

    A baya-bayan nan dai shafin na kakakin na yawan wallafa sakonni da suka haɗa abubuwan dariya.

  9. Yadda aka gicciye Yesu Almasihu a mahangar Kirista

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.

    Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma'a a kuma kammala a ranar Litinin ta gaba.

    A tattaunawarsa da BBC, Rabaran Murtala Mati Dangora, mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kano ya ce bukukuwan Easter sun kasu kashi biyu; akwai wanda ake kira Juma'a mai Tsarki wato ''Good Friday'', da kuma Easter Monday.

    Rabaran Dangora ya kara da cewa "Juma'a mai Tsarki ko kuma ''Good Friday'' rana ce ta saduda, rana ce ta komawa ga Allah, rana ce ta tunani domin wahala da Yesu Almasihu ya sha a ranar."

    "A ranar ne aka zartar masa da hukuncin kisa a bisa umarnin sarkin Pontius Bilatus a wancan zamani, a ranar ne sojojin Romawa suka gicciye shi, a ranar ne kuma ya mutu, a ranar ne kuma aka saka shi a kabari bayan da aka yi jana'izarsa," in ji shi.

  10. Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan wurare fiye da 3000 a Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wurare dubu uku da ɗari biyar a Lebanon, tun bayan soma yaƙi tsakaninsu da ƙungiyar Hezbolla a watan da ya gabata.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce tun bayan soma yaƙin hare haren Isra'ila sun kashe mutum fiye da dubu ɗaya da ɗari uku, ciki har da yara ɗari da ashirin da biyar, da ma'aikatan lafiya fiye da hamsin.

    A cikin wannan makon Hezbollah ta yi ta kai wa Isra'ila hari da rokoki, yayin da Isra'ilar ta tsananta hare harenta, inda ta kai hari har wuraren da Hezbollah ba ta da iko da shi.

  11. Mun kakkaɓo jirage marasa matua 6 - Sauydiyya

    Ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa shida da suka shiga sararin samaniyarta.

    Kakakin ma'aikatar ya bayyana a ranar Juma'a cewa an kakkaɓo jiragen da safiyar ranar

    Sai dai ma'aikatar ba ta bayyana daga inda jiragen suke ba.

    Tun da farko a jiya Alhamis, Saudiyya ta ce ta kakkaɓo wasu jiragen marasa matuƙa huɗu.

  12. Tinubu ya sabunta wa'adin Injiniya Abdul'azeez a matsayin shugaban TCN

    ..

    Asalin hoton, TCN/WEBSITE

    Shugaba Bola Tinubu ya sabunta naɗin Injiniya Sule Ahmed Abdul'aziz a matsayin shugaban kamfanin dakon wutar lantarki na ƙasar, TCN a wani sabon wa'adi na shekara huɗu wanda shi ne na ƙarshe.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce an sabunta naɗin Injiniya Abdul'aziz ɗin ne sakamakon ƙwazon da ya nuna a tsawon lokacin da ya kwashe yana jagorancin kamfanin a wa'adinsa na farko.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Injiniya Abdul'aziz ya samar da cigaba na a-zo-a-gani dangane da wutar lantarki inda ya yawaita wutar da zamanantar da tsarin da kuma tabbatar da tsarin dakon wuta a Najeriya.

    Wannan sabunta naɗin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin wuta duk kuwa da yadda suke kokawa suna biya da tsada.

    Sai dai Injiniya Abdul'azeez ya ce yana sane da ƙarancin wuta da ƙasar ke fama da shi kuma zai yi duk iyawarsa wajen ganin an samu sauyi.

  13. Halin tsaka-maiwuya da China ta shiga tun bayan ɓullo da tsarin taƙaita haihuwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Miliyoyin al'umma a China na bikin sabuwar shekarar Gargajiya ta Lunar, inda za a yi bukukuwa da abinci, shagulgula da kuma addu'o'i. Sai dai ga waɗanda ba su yi aure ba lokaci ne na raɗaɗi, saboda iyayensu na ware kwanaki don sukar su da yin alawadai da su saboda kasa aure ko kuma haihuwa.

    Rashin samun ɗa batu ne da ya daɗe yana jawo cece-kuce a China (da kuma wasu wurare a gabashin Asiya) kuma yanzu lamarin ya tsayawa hukumomi a zuciya.

    Batun ya sake tashi a watan da ya gabata, yayin da gwamnati ta fitar da sabbin alkaluma da ke nuna yadda aka samu raguwar haihuwa matuka a ƙasar.

    Alkaluman sun nuna cewa an samu haihuwa kashi 5.63 cikin mutum 1,000 wanda ba abu ne da ba a taɓa gani ba tun kafa Jamhuriyar China a 1949 - kuma abu ne da hukumomin ƙasar ba su taɓa tsammani za a samu ba.

  14. INEC ta yi watsi da kiraye-kirayen cire shugabanta

    Josh Amupitan

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi wa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa.

    Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta fitar ta bayayna kiraye-kirayen da hari kan dokokin da suka kafa hukumar.

    A ranar Alhamis ne jam'iyyar ADC mai hamayya a ƙasar, ɓangaren David Mark ta buƙaci Mista Amupitan ya sauka daga muƙaminsa bayan da ta zarge shi da nuna ɓangaranci a aikinsa.

    Matakin jam'iyyar na zuwa ne bayan da INEC ɗin ta sunayen shugabannin jam'iyyar ɓangaren David Mark, saboda umarnin kotu kamar yadda ta bayyana.

    INEC ɗin ta ce kiraye-kirayen ba su da matsuguni, kasancewar doka ce ta naɗa shugaban nata.

    “Dokar Najeriya ce ta samar da hukumar INEC. Kuma doka ce ta tanadfi naɗa shugabanninta kuma wa'adinsu,'' in ji sanarwar.

    “Shugaban INEC ba yana aiki ne ga kowace jam'iyya ko wata ƙungiya. Don haka duk wasu kiraye-kirayen cire shi daga wajen doka cin zarafi ne ga tsarin zaɓen ƙasa,'' kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

  15. 'Amurka na neman matuƙin jirginta da aka kakkaɓo a Iran'

    Jirgin yaƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labaran Iran, Tasnim, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin ƙasar, ta yi iƙirarin cewa Amurka na neman ɗaya daga cikin matuƙa jirgin yaƙinta da aka bayar da rahoto kakkaɓo shi a Iran

    A ranar Alhamis da daddare ne, rundunar sojin Amurka mai kula da mayaƙan ƙasar, US Central Command ta yi watsi d rahotonnin da IRGC ke yaɗawa cewa ta kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen yaƙin Amurkan a tsibirin Qeshm da ke mashigar Hormuz.

    Babu tabbas ko wannan sanarwa na nufin rahotonnin baya-bayan nan, kuma BBC ta tuntuɓi rundunar Centcom domin ƙarin bayani.

    Tasnim ya bayar da rahoton cewa jiragen Amurka masu saukar ungulu da jiragen sama da jirage marasa matuƙa na cikin waɗanda suke neman matuƙin jirgi.

    Wani mai karanta labarai a wani gidan talbijin na ƙasar ta bayar da rahoton cewa za a bayar da lada ga duk wanda ya kama matuƙin jirgin da ransa.

    BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin ikirarin ba, amma muna ƙoƙari domin tattara ƙarin bayan bayani.

  16. Fafaroma Leo ya buƙaci Shugaban Isra'ila ya buɗe ƙofar tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙin Iran

    ,.

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran ɗariƙar Katolika na duniya, Fafaroma Leo ya sake yin kira ga shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya buɗe ƙofar kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato shugaban fadar Vatican ɗin na bayyana haka a lokacin tattaunawar waya da mutanen biyu suka yi.

    Fadar Vatcian ta ce Fafaroma Leo, wanda ya yi fice a sukar yaƙin Gabas ta Tsakiya, ya buƙaci Mista Herzog ta kare fararen hula tare da martaba girmama dokokin duniya da na jin ƙai.

  17. Farashin kayan abinci ya tashi saboda yaƙin Iran -MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin da ya daɗe bai yi ba tsawon watanni shida da suka wuce, kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da tashi idan yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ci gaba.

    Babban jami'in tattalin arziki na hukumar kula da abinci da noma na Majalisar ya ce hauhawar farashin mai ne babban abin da za a ɗora wa alhakin karuwar farashin abincin zuwa yanzu, amma ya yi gargaɗin cewa katse samar da taki da wasu muhimman kayayyakin noma na iya ƙara ta'azzara lamarin.

    Ƙasashe da dama sun baiwa ma'aikata umurnin yin aiki daga gida,kuma sun ƙara farashin man fetir, sakamakon yadda hana wucewa ta mashigar Hormuz ya hana su shigar da mai da iskar gas cikin ƙasashensu.

  18. NBC ba ta da hurumin cin tarar gidajen radiyo da talbijin a Najeriya - Kotu

    Hukumar NBC

    Asalin hoton, NBC

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da hukumar kula da gidajen radiyo ta Najeriya NBC ta shigar gabanta, tana neman kotun ta rusa hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi na hana ta cin tarar wasu gidajen radiyo da talbijin a faɗin ƙasar.

    Yayin da yake gabatar da hukuncin, babban kotun Mai shari'a Oyebiola Oyewumi a madadin alkalan kotun uku ta amince da hukuncin babbar kotun tarayya, wanda ya hana hukumar NBC cin tarar gidajen labari 45 a ranar 1 ga watan Maris na 2019 saboda zarginsu da saɓa ƙa'idar dokar yaɗa labarai ta Najeriya.

    Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukumar NBC ba ta hurumin cin tarar gidajen labarai a ƙasar.

    Mai Shari'a Oyewumi ta ci gaba da cewa a ƙarƙashin dokokin Najeriya ana cin tara ne ga waɗanda aka samu da laifin saɓa doka, kuma kotu ce kawai ke da hurumin yin hakan, ba mutumin da aka yi wa laifi ba.

    Tun da farko babbar kotun tarayyar ta ce matakin na NBC ya saɓa wa dokokin Najeriya.

  19. 'Ƴanbindiga sun sace fiye da mutum 150 a Zamfara'

    yanbindiga

    Asalin hoton, Daily Trust

    Al'ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara sun ce ƴanbindiga sun yi sace fiye da mutum kusan 150 a wani hari da suka kai cikin dare.

    Mazauna yankunan sun ce ƙauyuka da dama ne ƴanbindigar suka tarwatsa, inda ɗaruruwan mutane suka yi gudun hijira.

    Hon Sulaiman Abubakar Gumi, ɗanmajalisar wakilai na tarayya mai wakilar Gumi da Bukkuyum ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mazauna ƙauyukan Kurfa Ɗanya da Kurfan Magaji sun kwana cikin tashin hankali.

    Ya ƙara da cewa kawo yanzu duka mutanen waɗannan garuruwa sun guda sun bar gidajensu, yayin da suke gudun jira a cikin garin Bukuyyum.

    Ya ci gaba da cewa dama yankin Bukuyyum da Gumi da Anka ya jima yana da fama da matsalar hare-haren ƴanbindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.

    Hon Abubakar ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta mayar da hankali domin magance matsalolin tsaron jihar Zamfara.

    ''Mun ga alamun gwamnati yanzu ta mayar da hankalinta a Borno, saboda barazanar dawowar Boko Haram, amma muna kira a gare ta cewa Zamfara na fama da matsalar tsaro'', in ji shi.

  20. Tinubu ya ce za a saka kyamarorin tsaro fiye da 5,000 a Filato

    Kyamarorin tsaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta saka kyamarorin tsaro masu amfani da fasahar AI fiye da 5,000 domin taimaka wa jami'an tsaro yaƙi da matsalar tsaro a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar.

    Shugaba Tinubu ya bayyana matakin yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Alhamis.

    Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da wasu mahara suka kai hari ƙauyen Angwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa tare da kashe mutane.

    Shugaba Tinubu ya ce minsitan sadarwar zamani da tattalin arziki, Bosun Tijjani ne zai kula da saka kyamarorin tare da hadin gwiwar gwamnatin Filato da jami'an tsaro.

    ''Za a fara saka kyamarorin ne daga birnin Jos sannan a faɗaɗa aikin zuwa sauran sassan jihar, kamar yadda aka saka jihohin Legas da Enugu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Shugaban na Najeriya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da alƙawarta farauto maharan.

    “Na yi muku alƙawarin cewa irin wannan al'amari ba zai sake faruwa ba,'' in ji shi.

    Shugaba Tinubu ya kuma umarci ministan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da babban hafsa sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu da kuma babban sifeton ƴansandan ƙasar, Olatunji Disu, su “tabbatar da kamo waɗanda suka aikata kashe-kashen” na waɗanda ba su ji ba su gani ba.

Trending Now