Arsenal da Man City da PSG na neman Olmo, Salah zai koma Saudiyya

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dani Olmo
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyar RB Leipzig ta sanya farashin fam miliyan 87 kan ɗan wasan gefe na Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 18, wanda kungiyoyin Liverpool da Manchester United ke zawarcinsa. (Sky Sports)

Kungiyoyin Saudi Pro League na ƙara ƙaimi wajen zawarcin ɗan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah mai shekara 33, kuma suna da ƙwarin gwiwar kammala yarjejeniya kafin gasar cin kofin duniya ta wannan bazarar. (Teamtalk)

Kungiyar Everton na ƙara samun kwarin gwiwa cewa ɗan wasan gefe na Manchester City da Ingila Jack Grealish mai shekara 30, wanda ke zaman aro, zai ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Daily Mail)

Kungiyoyin Manchester City da Paris Saint-Germain da kuma Arsenal duk suna sha'awar ɗan wasan Spain Dani Olmo mai shekara 27, yayin da Barcelona ta bude kofar sayar da shi. (Fichajes)

Kungiyar Atletico Madrid na dab da kulla yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Brazil daga Atalanta Ederson mai shekara 26, wanda kuma Manchester United da Manchester City ke sha'awa. (Fabrizio Romano)

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola mai shekara 55 ba zai yanke hukunci kan makomarsa a kungiyar ba sai karshen kakar wasa. (Telegraph)

Kungiyar Manchester United na shirin ƙara sabbin 'yan wasan tsakiya guda biyu a wannan bazarar, inda ake take duba yiwuwar daukar 'yan wasan Ingila Elliot Anderson na Nottingham Forest, da Adam Wharton na Crystal Palace, da kuma ɗan Italiya na Newcastle United Sandro Tonali. (Givemesport)

Kungiyar Arsenal na ci gaba da nuna sha'awar sayen ɗan wasan baya na Spain mai shekara 19 Victor Valdepenas daga Real Madrid, amma za ta fuskanci gasa daga AC Milan. (Caughtoffside)

Ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva zai bar Manchester City kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a watan Yuni, inda tuni yake nazarin zabinsa. (Fabrizio Romano)

Kungiyar Barcelona na shirin sayen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi mai shekara 24 a wannan bazarar. (Fichajes)

Ɗan wasan gaba na Netherlands da West Ham United Crysencio Summerville mai shekara 24 na cikin jerin 'yan wasan da kungiyoyi kamar Aston Villa da Everton da Tottenham Hotspur da Marseille da Napoli ke sa ido a kansa. (Teamtalk)