Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 20 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Isiyaku Muhammed

  1. Ba ni da niyyar tozarta Yesu - Netanyahu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba shi da niyyar tozarta Yesu Almasihu a cikin kalaman da ya yi a wani jawabi da ya yi da aka watsa ta gidan tallabiji a jiya Alhamis.

    Hakan dai ya bayan ya fuskanci suka da Allah-wadai a shafukan sada zumunta bayan ya ce ta fuskar karfin iko, Yesu ba shi da wata dama ta samun galaba a kan Genghiz Khan.

    Genghiz Khan dai wani mayaki ne maras imani da ya kafa daular Mongol wadda ta kusa mamaye ilahirin duniya.

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, ya ce ga mutumin da ya dogara sosai kan agajin Kiristoci a Amurka, kyamar da Mista Netayahu ya nuna wa Yesu Almasihu abu ne mai ban mamaki.

  2. Trump ya bayyana kasashen NATO da matsorata

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya kira sauran kasashen mambobin kungiyar tsaro ta NATO da matsorata.

    Trump ya kira da su matsoratan ne saboda matsayarsu ta rashin goyon bayan Amurka wajen tursasa wa Iran bude mashigar Hormuz.

    A cikin wani sako da wallafa a shafinsa na True Social, ya ce mambobin kungiyar sun koka kan tsadar man da aka tilasta musu biya sakamakon yakin, amma ba sa son taimakawa wajen bude mashigar ruwan Hormuz.

  3. IEA ta nemi kasashen duniya su rage amfani da makamashi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da makamashi ta Duniya IEA ta bukaci gwamnatocin kasashe da su yi duk mai yiwuwa don rage bukatar man fetur, ciki har da karfafa wa mutane gwiwar yin aiki daga gida da kuma rage gudun ababe da kilomita goma a cikin sa'a daya.

    Shugaban Hukumar Dr. Fatih Birol ya ce cikas ga tsarin samar da makamashi na duniya da yakin Amurka da Isra'ila kan Iran ya kawo shi ne mafi girma a tarihin kasuwar mai.

    Hukumar ta IEA ta kuma bukaci mutane da su guji tafiye-tafiye ta jirgin sama a inda hakan zai yiwu.

    Farashin makamashi ya yi tashin gwabron zabo tun bayan da Iran ta mayar da martani ga hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai ma ta ta hanyar kokarin rufe hanyan jigilar mai mafi hada-hada a duniya wato mashigin Hormuz.

  4. Amurka za ta aike da sojojin ruwa kimanin 2500 zuwa Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu jami'an Amurka da ba a bayyana sunansu ba sun ce Amurka na shirin sake aikewa da dubban karin dakaru da jiragen yaki na ruwa zuwa Gabas ta Tsakiya.

    Jami'an na Amurka sun ce dakarun kimanin 2,500 za su bar sansanin USS Boxer da kuma runduna ta 11 da ke California zuwa Gabas ta Tsakiya.

    Wani jami'in ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reauters cewa aikewa da sojojin na zuwa ne makonni uku kafin bukatarsu.

  5. Zulum ya ce akwai 'yan kunar bakin wake a yanzu haka a Maiduguri

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo da sauraron gwamna Zulum
  6. Mojtaba ya zargi Isra'ila da kai hari kasashe domin raba kan Musulmi

    ..

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

    Jagoran addinin Musulunci na Iran, Mojtaba Khamenei ya musanta ikrari da rahotannin cewa Iran ta kai wa Turkiye da Oman hari.

    A wata sanarwa ta taya Iraniya murnar zagoyar bikin shekarar Nowruz, Mojtaba ya ce Iran tana matukar mutunta makwabtanta musamman wadanda ke gabashi, inda ya bayyana cewa kasar Pakistan tana da muhimmanci sosai a wurin mahaifinsa.

    Mojtaba ya kuma kara da cewa yana daukar matakan da suka dace wajen kulla alaka mai karfi da kasashen Pakistan da Afghanistan.

    Dangane kuma da hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kai wa kasashen Gabas ta Tsakiya, Mojtaba ya ce Iran "ba ta kai hari kan Turkiya da Oman ba kasancewar suna da kyakkyawar alaka. Rundunar sojojin juyin juya hali ba ta kai musu hari ba kwata-kwata."

    Ya kuma zargi Isra'ila da "yaudara" domin ta raba kan Iran din da makwabtanta.

  7. Muna son tattauna wa da Iran amma babu wanda za mu tattauna da shi - Trump

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce "muna son tattaunawa da Iran" to amma kuma "babu wanda za mu yi magana da shi," in ji Trump a wani kwarkwaryar taron manema labarai.

    Sai dai kuma Trump ya ce "muna jin dadin hakan".

    Ya kuma kara da cewa Iran na da burin mamaye Gabas ta Tsakiya inda ya nanata cewa "idan da a ce suna da makamin nukiliya da za su iya amfani da shi."

    Ana dai yi wa kalaman na Trump kallon shiga tsaka mai wuya bayan kashe jagororin jamhuriyar da dama da Amurka da Isra'ila suka yi, na samun hakikanin jagoran da za a tattauna da shi.

    Da ma dai masana na cewa kawar da Khamenei da wasu manyan jagororin kasar babbar matsala ce kasancewar sabbin jini da ke da ra'ayin rikau za su iya tasowa su kuma ki saurarar kowa.

  8. Kusan jiragen dakon ɗanyen mai 100 ne suka wuce ta mashigar Hormuz bayan fara yaƙi

    Hormuz

    Asalin hoton, Reuters

    Kusan jiragen dakon ɗanyen mai guda 100 ne suka wuce ta mashigar Hormuz tun bayan ɓarkewar yaƙin Isra'ila da Amurka a Iran a watan Maris.

    Wasu alƙaluma da sashen bin diddigi na BBC ne ya tantance mashigar duk da yanayin hare-haren da Iran ke yi a jiragen da suke wucewa.

    Duk da cewa wasu makamashin na wucewa, an samu ragowa da kusan kashi 95 na hada-hadar ɗanyen man fetur na duniya.

    Alƙaluman da mai nazari kan sufurin jiragen ruwa, Kpler ya nuna, ya bayyana cewa jiragen dakon ɗanyen mai guda 99 ne suka wuce ta mahigar, kusan biyar ko shida ke nan a kullum.

  9. Harin Isra’ila ya kashe kakakin dakarun juyin-juya-halin Iran

    Iran

    Asalin hoton, Fars

    Dakarun juyin-juya-halin Iran sun tabbatar da kashe kakakin rundunar, Ali Mohammad Naeini, kamar yadda kakakin rundunar tsaron asar ya bayyana.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ne ya ruwaito labarin, inda ya ara a cewa an kashe Naeni ne a safiyar yau.

    Naeni ya kasance mai magana da yawun rundunar ne har lokacin da hare-haren Isra'ila suka kashe shi.

  10. Ba mu bai wa Amurka sansaninmu domin ta yaki Iran ba - Birtaniya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya ta amince ta kyale Amurka ta yi amfani da wasu sansasanoninta na soji amma kuma ta ce za a yi amfani da su ne kawai wajen "kariyar kai" dangane da kai hare-hare a cibiyoyin kere makamai masu linzami na Iran.

    Firaiministan Birtaniya, Keir Stermer ya ce Birtaniya ta dauki darussan daga "kurakuran da aka tafka a Iraqi" wanda shi ya sa ma ba ta shiga shirin kai wa Iran hari ba tun da farko.

    Babu dai tabbacin irin abin da Amurka ke shirin yi da sansanin RAF Fairford na Birtaniya amma kuma an ga yawaitar hada-hadar Amurkawa a sansanin sojojin sama na Gloucestershire inda ake ganin jirage masu jefa bama-bamai na sauka da tashi.

  11. Ina kokarin kamewa daga shiga yaki a Gabas ta Tsakiya - al-Sharaa

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya ce yana kokarin ganin kasarsa ta kame daga shiga rikicin Gabas ta Tsakiya.

    "Abu ne a fili cewa Syria ta kwashe fiye da shekaru 15 tana fama da rikici amma yanzu tana zaune lafiya da makwabtanta da ma kasashen duniya baki daya," kamar yadda ya fada a wani bikin sallar Idi.

    Ya kara da cewa abin da muke ganin yanzu haka na faruwa wani abu "sabo irinsa na farko tun bayan yakin duniya".

    "Muna yin lissafi na kokarin gujewa sake fadawa yanayin tashin hankali da rikici domin muna bukatar cigaban da muke samu ya dore," in ji alSharaa.

  12. Iran ta gargadi Birtaniya kan bai wa Amurka sansanoninta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta shaida wa Birtaniya cewa bai wa Amurka damar yin amfani da sansanoninta tamkar "shiga cikin yaki" ne, kamar yadda ministan harkokin wajen Iran din ya shaida.

    Abbas Araghchi ya yi waya da takwaransa na Birtaniya, Yvette Cooper inda ya shaida musu cewa duk wani taimako da Birtaniyar ta bai wa Amurka to zai iya "kara ta'azzara2 yanayin ne.

    Araghchi ya kuma zargi Birtaniya da sauran kasashen Turai da "nuna son kai" kan abin da ya kira "tsokana ta kurukuru" da Amurka da Isra'ila ke yi.

    Rahotanni na cewa Araghchi ya kuma yi kakkausan suka ga Birtaniya bisa kin sukar hare-haren Isra'ila a ma'adanar iskar gas ta South Pars na Iran.

    BBC ba ta samu martani daga gwamnatin Birtaniya ba dangane da kalaman na Iran sai ta nemi ta jin bakinta.

  13. Ƴan majalisar Kamaru sun kaɗa ƙuri'ar tsawaita wa'adinsu

    Rahotannin kafafen watsa labarai daga Kamaru sun ce ‘yan majalisar dokokin kasar sun sake kada kuri’a domin tsawaita wa’adinsu.

    Bisa doka dai wa'adin majalisar dokokin kasar ta yanzu zai kare ne fiye da shekara guda da ta wuce, amma yanzu za ta iya ci gaba da aiki har zuwa watan Disamba.

    Hukumomi sun ce an tsawaita wa’adin ne domin rage matsin lamba wajen kashe kudi, musamman bayan zaɓen shekarar da ta gabata wanda ya ga shugaban ƙasar da ya shafe shekaru a kan mulki Paul Biya, ya sake lashewa a karo na takwas.

    An samu kazamin rikici bayan zanga zangar nuna rashin gamsuwa da zaben.

  14. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 1,001 a Lebanon

    Lebanon

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Kafar watsa labaran Lebanon ta ruwaito cewa Isra’ila ta kai hare-hare a biranen kudancin ƙasar ta safiyar yau, lamarin da ya jikkata mutane da dama.

    Kafar ta ce jiragen yaƙin Isra’ila ne ya kai hari a biranen Bafliya da Hanin a yankunan Tyre da Bint Jbeil da asubar yau.

    Ma’aikatar lafiyar Lebanon ta sanar da cewa zuwa yanzu hare-haren Isra’ila sun kashe aƙalla 1,001 tun daga 2 ga watan Maris.

    Ma’aikatar ta ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kashe akwai mata 79, da ƙananan yara 118 da ma’aikatan lafiya 40, sannan an jikkata wasu 2,584.

  15. Shugabar rikon-ƙwarya ta Venezuela ta canja shugabannin sojin ƙasar

    Venezuela

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugabar rikon-ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta sauya manyan kwamandojin sojojin ƙasar, kwana guda bayan ta naɗa sabon ministan tsaro.

    Wannan shi ne sabon sauyi a matakin koli na gwamnati a Venezuela tun bayan da sojojin Amurka suka kama tsohon shugaban ƙasar, Nicolás Maduro, a watan Janairu.

    Tun daga lokacin ne Shugaba Rodríguez, wadda ita ce ita ce mataimakiyar Mista Moduro, ta rika ba wa gwamnatin Trump hadin kai.

    Wakiliyar BBC ta ce shugabar rikon ta ce sabon tsarin jagorancin sojojin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, da cikakken ikon ƙasa da kuma ‘yancin kan Venezuela.

  16. A tuna da ƴan gudun hijira a lokacin bukukuwan Sallah - Gwamnan Sokoto

    Sokoto

    Asalin hoton, Director General Media and Publicity Government House

    Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu ya yi kira ga Musulmai a jihar da su tuna da ƴan gudun hijira a lokacin bukukuwan Sallah, inda ya buƙaci masu hali da su ci gaba da taimakonsu har bayan Sallah.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙonsa na Sallah, wanda mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa ya sanya wa hannu.

    Ya ce Musulunci na ƙarfafa son juna da taimakon juna, musamman ta hanyar taimakon marasa ƙarfi, sannan ya nanata cewa ƴan gudun hijira na buƙatar taimako daga masu ƙarfi domin taya ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da cewa suna rayuwa kamar kowa.

    Gwamnan ya ce tun bayan ɗarewarsa karagar mulki ne yake da ta faɗi tashi domin magance matsalar tsaro a jihar. "Mun yi ƙoƙari wajen inganta rayuwar ƴan gudun hijira da gyara wuraren da suke zama. Mun raba gidaje guda 100 ga ƴan gudun hijira a ƙaramar hukumar Illela, kuma za mu ƙara gina wasu domin suma su samu sukuni."

    Ya ƙara da cewa suna ba ƴan gudun hijirar abinci da sauran kayayyakin buƙata da ƴan gudun hijirar suke buƙata a faɗin jihar.

    Gwamnan ya kuma nanata cewa gwamnatinsa na taimakon marasa ƙarfi, inda ya ce sun raba miliyoyi ga marayu da masu buƙata ta musamman da sauran mabuƙata a jihar, sannan ya ya jinjina wa taimakon da sauran masu hannu da shuni suke.

    Gwamnan ya bayyana alfaharinsa ga tallafin gwamnatinsa ke ba limamai da mataimakansu da ladanai da malamai da sauran masu yi wa addini hidima, sannan ya yi alƙawarin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da ababen more rayuwa a faɗin jihar.

  17. Mu yi amfani da Sallar bana wajen yi wa Najeriya addu'a - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga, OON, CON @aonanuga1956

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci jagororin addinin Musulunci da su yi amfani da su yi amfani da ranar Sallah domin yi wa ƙasar addu'a samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.

    Tinubu ya bayyana haka a saƙonsa na Sallah, wanda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, inda a ciki ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen ƙaunar ƙasar da son juna.

    Ya kuma buƙaci Musulman Najeriya da su ci gaba da koyi da abubuwan da suka koyi a watan mai tsarki, wanda ya ƙarfafa "imani da tausayi da haɗin kai a tsakanin al'umma."

    "Akwai darussa da yawa da za mu koya daga watan Ramadan, musamman a wannan lokacin da muke ciki. Ya kamata mu ci gaba da amfani da darussan da muka ɗauko na taimakon juna da juriya da tausayi har bayan azumin na watan Ramadan," in ji shi.

    Tinubu ya kuma buƙaci Musulman ƙasar da su nuna ƙauna da son juna ta hanyar taimakon marasa ƙarfi ba tare da la'akari da bambancin addini ba, domin a cewarsa, hakan ne zai ƙara haɗa kan ƴan ƙasa.

  18. Ba za mu sake kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran ba - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, AFP

    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa, ba za ta sake kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran ba. Yana magana ne bayan wani gargadi da shugaba Trumo ya yi masa kan sake yin hakan.

    Wani harin da Isra’ila ta kai kan cibiyar iskar gas ta South Pars ta Iran a ranar Laraba, da kuma martanin da Iran din ta mayar, sun haifar da tashin gwauron zabin farashin gas da man fetur a kasashen Turai.

    Da yake magana a wani taron manema labarai, Netanyahu ya yi watsi da zarge-zargen cewa shi ya yi wa shugaba Trump angiza mai kantu ruwa, wajen kai wa Iran din hari.

    Ya ce yanzu har akwai wanda ke tunanin cewa wai wani ne zai cewa shugaba Trump ga abun da ya kamata ya yi?. haba mana. Ya ce shugaba Trump na daukar mataki ne kan abun da ya ke ganin shi ne dai dai ga Amurkawa da kuma gobenmu baki daya.''

  19. Sanata Barau ya buƙaci Musulmai su ci gaba da addu'o'in neman zaman lafiya

    Sanata Barau

    Asalin hoton, Ismail Mudashir

    Mataimakin shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya yi kira ga musulmai a faɗin duniya da su ci gaba da addu'o'i domin zaman lafiya a duniya.

    Sanata ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismail Mudashir, inda ya taya muslman Najeriya murnar Sallah, tare da addu'ar "Allah ya karɓa mana ibadun da muka yi, ya amsa mana addu'o'inmu."

    Ya yi kira ga Musulmi a faɗin duniya da su ci gaba da addu'o'in, sannan su ci gaba da koyi tare da ɗabbaƙa halayen ƙwarai da suka koya a watan Ramadan.

    Ya kuma yaba wa shugaban Najeriya Bola Tinubu, bisa abin da ya bayyana da ƙoƙarinsa ya inganta tattalin arzikin Najeriya, da yaƙi da matsalar tsaro.

    A ƙarshe ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa ƙarfi domin suma su samu damar gudanar da shagulgulan Sallah cikin nishaɗi.

  20. Iran ta yi luguden wuta cikin dare a Isra'ila

    Iran

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Iran ta ci gaba da yin luguden wuta cikin dare kan Isra'ila, inda rahotanni ke cewa an ji karar manyan fashe fashe a sassan kasar da dama.

    A birnin Jerusalem, na'urar gargaɗi ta yi ta ƙuwa ba ƙaƙƙautawa, yayin da gidan talabijin ɗin Iran ya bayar da rahoton kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

    Hakan na zuwa ne bayan matakin Iran na kai hari wasu matatun man fetur biyar na ƙasashen Larabawa a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai kan wata cibiyar iskar gas ɗinta.

    A Qatar harin na Iran ya lalata cibiyar iskar gas mafi girma a duniya ta Ras Laffan, inda shugaban kamfanin ya ce ƙiyasin da suka yi, ya nuna za a shafe shekara biyar kafin kafin a iya gyara matsalar.

    Ya ƙara da cewa a cikin waɗannan shekaru, za a samu yankewar kashi 17 ciki 100 na gas ɗin da cibiyar ke bai wa duniya a kowacce shekara.

    A gefe guda, suma ƙasashen Saudiyya da Bahrain sun ce Iran ɗin na ci gaba da harba masu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Trending Now