Ko yaƙin Iran zai razana Kim Jong Un kan makomar Koriya ta Arewa?

 Kim Jong Un

Asalin hoton, BBC / Andro Saini

    • Marubuci, Sangmi Han
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean
    • Aiko rahoto daga, Seoul
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wataƙila Kim Jong Un zai fara tunani kan makomar ƙasarsa tun bayan yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar a Iran.

Ƙasarsa na cikin ƙasashen da suke fara Allah-wadai da hare-haren, inda ta bayyana hare-haren da "haramtacce."

Sanna dama can akwai alaƙa a tsakanin ƙasashen biyu, inda suka haɗu "domin nuna adawa da Amurka" tun a shekarar 1979, sannan suka sake ƙulla alaƙa a kan ƙefa makamai masu linzami.

Haka kuma Iran kan gaba wajen sayen makamai daga Koriya ta Arewa, kamar yadda wani tsohon jami'in diflomasiyya da ba ya so a ambata sunansa ya bayyana.

Amma dai abubuwa biyu da suka ƙasar Koriya ta Arewa take fuskantar barazana babba sama da Iran, in ji wani masani. Waɗannan abubuwan su ne makamin nukiliya da ƙasar China.

A lokacin yaƙin Iraqi na 2003, tsohon shugaban ƙasar Kim Jong II ya yi ɓatar dabo na kwana 50 ba tare da an gan shi ba.

Hukumar tattara bayanan sirrin Koriya ta Kudu ta bayyana cewa ya ɓoya ne a wani rami a gidan Samjiyon, mai nisan kilomita 600 daga babban birnin ƙasar, Pyongyang.

Sai dai ba kamar wanda ya gada ba, ɗansa Kim Jong Un bai taɓa ɓoya ba duk da kashe tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei da aka yi.

Wannan ya nuna ƙari ƙarfin gwiwa da ƙwanji da Koriya ta Arewa ta samu, in ji Jang Yong-seok, wanda tsohon darakta ne kan Koriya ta Arewa a hukumar leƙen asiri ta Koriya ta Kudu.

Makamin nukiliya

Koriya ta Arewa ta kasance tana ta gwada makamai masu linzami a mulkin Kim Jong Un

Asalin hoton, AFP / KCNA VIA KNS

Bayanan hoto, Koriya ta Arewa ta kasance tana ta gwada makamai masu linzami a mulkin Kim Jong Un
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Koriya ta Arewa ƙasa ce da aka daɗe ana tunanin tana da makamin nukiliya, kuma shi da kansa Shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2025 ya bayyana ƙasar a matsayin wadda "take da alamar ƙarfin nukiliya."

Wani rahoton da cibiyar nazarin harkokin tsaro na Stockholm ta fitar a 2025 ya ce Koriya ta Arewa na da kayan haɗa nukiliya 50, sannan suna da ƙarin kayan aiki da za ta iya samar da guda 40.

A watan Yulin 2024 na Koriya ta Kudu ta yi gargaɗin cewa Koriya ta Arewa na matakin ƙarshe ne na ƙera makamin nukiliya.

Haka kuma a bara ma Shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung ya ce Koriya ta Arewa na gab da ƙera wani makamin ƙare dangi da zai iya kai harin makamin nukiliya har cikin Amurka.

Hukumar makamin nukiliya ta duniya IAEA ta ce Iran na da "buri mai ƙarfi na mallakar makamin nukiliya," amma ta ce babu tabbataccen hujja da ke nuna cewa "ƙasar na da shiri ingantacce domin fara ƙera makamin."

Bayan wata yarjejeniya kan taƙaita haɗa makamin nukiliya ta 2015, Iran ta amince ta taƙaita shirinta na inganta sinadarin uranium, wanda shi ne yake kaiwa ga haɗa makamin na nukiliya.

Bayan Trump ya fice daga yarjejeniyar a 2018, sai Iran ta taƙaita amincewa da take yi ga hukumomin sa ido suna shiga cibiyoyinta.

Sai dai ita Koriya ta Arewa ta fara gwajin makamanin na nukiliya ne a 2006, sannan bayan shekara uku ta hana jami'an IAEA ziyarar cibiyoyin. Sannan daga lokacin yanzu ta sake yin gwaji guda uku, na ƙarshe a 2017.

Trump da Kim sun gana a ƙasar Singapore a 2018
Bayanan hoto, Trump da Kim sun gana a ƙasar Singapore a 2018

A baya, Koriya ta Arewa ta so ta ga tattauna da Amurka, wanda hakan ya sa shugabannin ƙasashen biyu suka gana a shekarar 2018 da 2019. Shi dai Kim na so a ɗage masa takumkumai na ƙasashen duniya.

Ya yi alƙawarin zai iya haƙura da cibiyar makamin nukiliya ta Yongbyon, amma shi Trump na buƙatar ƙarin abubuwa da dama, wanda hakan ya sa tattaunawar ba ta kai ga nasara ba.

Koriya ta Arewa ta ƙara samun ƙarfin gwiwa saboda yaƙin Ukraine ya sa ta ƙara samun kusanci da Rasha, lamarin da ya sa ta ƙara samun alaƙar soji da tattalin arziki.

China da Rasha da batun nukiliya

Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa na da bakin iyaka da China, wadda ke adawa da Amurka, kuma idan ƙasar ta samu tangarɗa, baƙin-haure China za su kwarara.

Tun shekarar 1962, China ta ɗauki alwashin kariya ga Koriya ta Arewa idan aka kai mata hari.

Haka kuma Koriya ta Arewa na barazana ga Koriya ta Kudu da Japan, saboda kusancin da suke da ita, in ji Janga na cibiyar Asan.

Ƙasashen Koriya biyu sun rabu da wani yankin tudun mun tsira mai nisan kilomita 250 da faɗin kilomita 4, sannan babban biranen ƙasashen biyu na da tafiyar kilomita 200 ne a tsakaninsu.

Ita Japan na kusa da yankin tudun mun tsira na Koriya ta Arewa, sannan ta daɗe tana harba makamai masu linzami a tekun Japan a duk lokacin da take gwaji.

Ƙasashen biyu na Asia na ɗauke da dakarun Amurka kusan 80,000 ne, yayin da sojojin na Amurka 50,000 ne a Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.

Yaƙin Iran zai iya ƙara fahimtar da Kim cewa Ali Khamenei "ya rasa yadda zai yi ne saboda ba shi da makamin na nukiliya" sannan shiga yarjejeniya da Amurka ba tabbas ba ce ta tseratar da gwamnatin ƙasa, kamar yadda Ellen Kim na cibiyar nazarin tattalin arziki ta Korea-US.

Town ya ƙara da cewa, "Koriya ta Arewa ta sha wahala sosai a ƙoƙarinta na mallakar makamin nukiliya. Shi dai Kim Jong Un ya yi amannar cewa mataki mai kyau ya ɗauka, domin ya san cewa kai hari kan ƙasar da ke da makamin nukiliya na da wahala."

Akwai ƙarin rahoto da tacewa daga Grace Tsoi & Mark Shea