Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu ya yi kira ga Musulmai a jihar da su tuna da ƴan gudun hijira a lokacin bukukuwan Sallah, inda ya buƙaci masu hali da su ci gaba da taimakonsu har bayan Sallah.
Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙonsa na Sallah, wanda mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa ya sanya wa hannu.
Ya ce Musulunci na ƙarfafa son juna da taimakon juna, musamman ta hanyar taimakon marasa ƙarfi, sannan ya nanata cewa ƴan gudun hijira na buƙatar taimako daga masu ƙarfi domin taya ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da cewa suna rayuwa kamar kowa.
Gwamnan ya ce tun bayan ɗarewarsa karagar mulki ne yake da ta faɗi tashi domin magance matsalar tsaro a jihar. "Mun yi ƙoƙari wajen inganta rayuwar ƴan gudun hijira da gyara wuraren da suke zama. Mun raba gidaje guda 100 ga ƴan gudun hijira a ƙaramar hukumar Illela, kuma za mu ƙara gina wasu domin suma su samu sukuni."
Ya ƙara da cewa suna ba ƴan gudun hijirar abinci da sauran kayayyakin buƙata da ƴan gudun hijirar suke buƙata a faɗin jihar.
Gwamnan ya kuma nanata cewa gwamnatinsa na taimakon marasa ƙarfi, inda ya ce sun raba miliyoyi ga marayu da masu buƙata ta musamman da sauran mabuƙata a jihar, sannan ya ya jinjina wa taimakon da sauran masu hannu da shuni suke.
Gwamnan ya bayyana alfaharinsa ga tallafin gwamnatinsa ke ba limamai da mataimakansu da ladanai da malamai da sauran masu yi wa addini hidima, sannan ya yi alƙawarin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da ababen more rayuwa a faɗin jihar.