Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Akwai ƴan ƙunar baƙin-wake biyu da ba a gano ba a Maiduguri'
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce sun samu bayanan sirri da ke tabbatar da cewa akwai sauran mahara biyu da ke cikin Maiduguri da niyyar kai harin ƙunar baƙin wake kan jama'a.
Gwamna Zulum ya ce a bisa bayanan da suke da su, mahara biyar ne suka shiga Maiduguri da niyyar kai hari, kuma uku daga cikin su sun mutu a harin ranar Litinin da ya kashe mutane fiye da 20, yayin da ake neman sauran biyun.
Maharan dai sun tayar da bama-bamai a gab da asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da babbar kasuwar 'Monday Market' da kuma ofishin aikewa da saƙonni ko gidan waya duk a cikin birnin Maiduguri.
Hare-haren sun auku ne jim kaɗan bayan mayaƙan na Boko Haram sun kai wasu hare-haren a sansanonin sojin Najeriya da ke Ajari da Baga da kuma Damboa duk a jihar ta Borno.
A hirarsa ta farko da BBC bayan harin ranar Litinin a birnin Maiduguri, gwamna Zulum ya ce jami'an tsaro sun duƙufa aikin nemo sauran ƴan ƙunar baƙin wake biyu daga cikin biyar ɗin da suka kai harin, domin ganin ba su kai ga aiwatar da mummunar aniyar ta su ba.
Ya ce dama sun saba shiga halin ɗar-ɗar a duk lokacin da bukukuwan salah suka ƙarato, yamna mai cewa ''duk wanda ke cikin Maiduguri yana da wannan tarihin, kowacce sallah in ta kusa, muna mayar da hankali saboda sai an tura mana masu bom-bom.''
Ya kuma bayyana cewa suna ɗaukar matakan da ya kamata, illa dai su ma maharan suna sauya salo ne a kowanne lokaci.
Gwamna Zulum ya ce ƙarin hare-haren ƴan Boko Haram da jihar Borno ke fama da su, abu ne da ke faruwa saboda yadda sojoji da sauran jami'an tsaro ke fatattakar maharan daga cikin daji.
''Kwannan nan ana yaƙi ne a cikin Sambisa, to duk lokacin da ake yakin, su ma za su fita su nuna cewa suna da ƙarfi saboda su ja hankalinmu, mu bar daji mu zo cikin gari.'' In ji Zulum.
Dangane da gano ko su wane ne suka kai harin na ranar Litinin a birnin Maiduguri kuwa, gwamnan ya ce ''mutane biyar ne suka shiga Maiduguri, su ƴan ƙunar baƙin wake, uku sun tada shi, biyu ba su tada ba... mutane su yi hankali ranar sallah nan,'' domin akwai sauran maharan biyu da suka shige cikin al'umma. Kuma har yanzu jami'an tsaro na neman su.
Gwamnan ya yi kira ga mutanen gari su sanya ido kan harkokin da ke gudana a kusa da su, domin kaucewa faɗawa tarkon maharan, su kuma tallawa jami'an tsaro da bayani game da su saboda .
Me ya sa hare-haren Boko Haram suka tsananta a cikin watan Ramadan?
Wata majiyar tsaro da ba ta so a ambaci sunanta ta ce sun samu rahoton cewa mayaƙan sun ce za su zafafa kai hare-haren ne a goman ƙarshe saboda a daidai lokacin ne aka yi yaƙin Badar a zamanin Annabi Muhammad (SAW).
Majiyar ta ƙara da cewa wannan ne ya sa sojojin da sauran jami'an tsaro suka fara aikin kar-ta-kwana domin daƙile yunƙuri ko barazanar.
A cikin wannan watan na Ramadan dai sassan Najeriya sun fuskanci hare-hare masu zafi, daga na Boko Haram zuwa na ƴanbindiga da sauransu.
Malam Kabiru Adamu mai bincike a harkokin tsaro a yankin Sahel, kuma shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce akwai bayanai da ke nuna cewa asaliln uwar ƙungiyar ce ta buƙaci haka.
"Mun samu bayanan da ke cewa babbar ƙungiyar ce ta buƙaci su ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare."
Masanin tsaron ya ce asalin burin mayaƙan shi ne kafa daular Musulunci, "amma a fahimtarsu duk wanda ba ya bin aƙidarsu, ba Musulmi ba ne. Duk da yake akwai bambancin Boko Haram da Iswap. Amma haƙƙin gwamnati ne ƙoƙarin tabbatar da cewa mutane sun fahimci abin da ke faruwa kuma tabbatar sun yi tir."