Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 10 da ya kamata ku yi kafin da bayan sallar Idi
Lokacin karatu: Minti 3
Bayan kammala azumi 30 da Musulmi suka yi, Idin ƙaramar sallah shi ne Ibada da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan a ranar 1 ga watan Shawwal.
Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin Musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla.
Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin.
BBC ta tattauna da Sheikh Nuru Khalid malamin addini ne a Abuja Najeriya inda ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi da bayan sallar.
- Fitar da zakkatul Fitr: Yana aya daga cikin wajiban ranar Sallar Idi karama a tabbatar an fitar da zakkar kono tun gabanin shirin tafiya masallaci, idan har mutum bai yi hakan ba a jajiberin sallar.
- Wankan Idi: Ana so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewa da sunnah. Mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan. Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na sauran wankan addinin muslunci, kamar na janaba, da na ɗaukewar jinin al'ada ko na biƙi, sai dai kawai niyya ce ta bambanta.
- Tsaftace jiki: Wannan ko ya haɗar da aske gashin hammata da na gaba da aske ƙumba ko farce ta yadda zai je masallaci ba tare da ya cutar da masallata, da warin jikinsa ba'.
- Sabunta Tufafi: Ranar sallah rana ce da ake son mutum ya sabunta tufafi, ya ci kwalliya da iyalansa, saboda ranar ce mai muhimmanci. Sai dai kuma malamai na gargaɗin mata da ka da su bayyana kwalliyarsu ga wasu mazaje musamman a filin Idi. An so mutum (namiji) ya saka farin tufafi domin tafiya masallacin Idi, sai dai idan mutum ba shi da damar sabuntawar, to sai ya tsaftace wanda yake da su''.
- Cin abinci: Idin ƙaramar salla da babbar salla ya bambanta ta fuskar cin abinci. A idin ƙaramar salla ba a so mutum ya tafi masallaci ba tare da ya ci wani abinci ba, domin ka da ya je Idi kamar yana azumi. Saboda haka ya kamata a samu wani abu a ci kafin tafiya masallacin idi ko da kuwa dabino ne, ko wani abu ko ruwa.
- Yawaita kabarbari: Ana so mai tafiya masallaci ya rinka kabarbari. Mutum zai riƙa fada, kuma da sauti mai ƙarfi ta yadda zai jiyar da na kusa da shi. Malamai sun ce hikimar yin kabarbarin cikin sauti mai ƙarfi shi ne don tunatar da waɗanda suka manta da yin kabarbarin.
- Ba a nafila kafin sallar Idi: Idan mutum ya isa masallacin Idi, abin da ake son ya yi shi ne ya zauna jiran ƙarasowar liman, tare da ci gaba da kabarbari.Sauraron huduba: An so mutum ya saurari hudubar liman bayan kammala salla.
- Sauya hanyar komawa gida: Haka kuma an so mutum idan zai koma gida daga masallacin idi, to inda hali ya sauya hanya, ka da ya bi ta hanyar da ya bi wajen zuwa masallacin, a lokacin da ya tashi komawa gida. An shawarci waɗanda gidajensu ke kusa da masallatan Idin da su tafi a ƙafa matuƙar yin hakan ba zai cutar da su ba.
- Sada zumunci: Bayan saukowa daga masallaci sai kuma a sada zumunci da kuma gudanar da bukukuwan Idi amma ba tare da wuce iyaka ba