Madrid na son Fernandez, Juventus na harin Ugarte na United

.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, ko ɗan wasan tsakiyar Ingila da ke taka leda a Crystal Palace Adam Wharton, idan ta gaza siyen ɗan wasan tsakiyar Manchester City Rodri, a kakar wasan nan. (Mundo Deportivo)

Sai Real Madrid ta yi wa Manchester City tayin fam miliyan hamsin sannan za ta ja hankalin City ta siyar mata da Rodri. (Football Insider)

Juventus na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Uruguay Manuel Ugarte. (Gazzetta)

Newcastle ta ƙarfafa aniyarta ta ci gaba da riƙe ɗan wasan tsakiyar Italiya Sandro Tonali a kakar wasannin nan, sakamakon gazawar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Seria A siyensa. (Talksport)

Newcastle ta amince da tayin siyen ɗan wasan gefen Independiente del Valle Johan Martinez. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan baya na Manchester City da Netherlands Nathan Ake na duba yiwuwar komawa taka leda a tsohuwar ƙungiyarsa ta Chelsea.(Sun)

Manchester United da Arsenal na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan gaban Barcelona Ferran Torres a wannan kaka. (Fichajes)

Chelsea da Liverpool ne a kan gaba wajen rige-rigen ganin sun yi nasarar daukar ɗan wasan tsakiyar Senegal Lamine Camara daga Monaco.(Caught Offside)

Bologna na duba yiwuwar siyen ɗan wasan Nottingham Forest Lorenzo Lucca, da ke matsayin dan wasan aro a Napoli zuwa ƙarshen kakar wasanni. (Gazzetta)

Tattaunawa don tsawaita kwantaragin ɗan wasan bayan IngilaTino Livramento da Newcastle ta zo ƙarshe, sai dai an gaza cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu, wanda hakan ya bai wa ɗan wasan damar barin ƙungiyar a kakar nan. (Football Insider)

Liverpool za ta fuskanci gogayya sosai daga Bayern Munich wajen siyen ɗan wasan bayan Faransa Maxence Lacroix daga Crystal Palace.(Teamtalk)

Babban cefanen da Barcelona ke son yi na siyen ƴan wasanta a kakar wasannin da ake ciki, shi ne siyen ɗan wasan Atlentico Madrid Julian Alvarez. (Mundo Deportivo)