Mene ne asalin yaƙin Pakistan da Afghanistan?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Sarah Hassan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Urdu
- Lokacin karatu: Minti 4
Aƙalla mutum 400 ne aka kashe a wani asibitin kula da masu shaye-shaye a Kabul, kamar yadda kakakin gwamnatin Taliban ya bayyana, wanda wani sabon babi ne a rikicin Afgahnistan da Pakistan.
Yanzu BBC ta samu nasarar ƙididdige komai da komai.
Cibiyar ta gyara hali, tana ɗauke da kusan mutum 2,000 ne, amma hare-haren suka tarwatsa ta.
Pakistan ta musanta cewa ta kai hari a cibiyar ne da gangan, inda ta ƙara da cewa, "ta kai hari ne kan wani waje na soji da taimakon ƴan ta'adda."
Mazauna kusa da cibiyar sune sun ji ƙarar fashewar wani abu da misalin 20:50 a ranar Litinin, 16 ga watan Maris.
A ranar 26 ga watan Farairu, Taliban na Afghanistan sun sanar da kai hari kan sojojin Pakistan da ke bakin iyaka duk da cewa ƙasashen biyu sun shiga yarjejeniyar tsagaita a watan Oktoba. Washegari ita ma Pakistan ta mayar da martani a biranen Kabul da Paktika da Kandahar.
Tun lokacin ne yaƙin ya ta'azzara kuma yake ƙara faɗaɗa. Amma shin mene ne asalin yaƙin?

Tarihi mai ɗaure kai
Kafin janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan a shekarar 2021, tsohuwar gwamnatin Kabul ta daɗe tana zargin Islamabad da taimakon Taliban wajen kai mata hare-hare, waɗanda ta ce daga Pakistan ake kitsawa.
A lokacin, Pakistan ta musanta zargin tana da alaƙ da Taliban, inda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan na wancan lokacin ya bayyana zargin da "abin ban dariya."
Pakistan ta taka rawar gani wajen shirya yarjejeniyar Doha, wadda ta taimaka wajen janyewar Amurka daga Afghanistan da mayar da mulki ga Taliban.
Tana kuma cikin ƙasashe kaɗan da suka fara amincewa da gwamnatin Taliban a lokacin mulkin farko na ƙungiyar tsakanin 1996 zuwa 2001.

Asalin hoton, Akhtar Gulfam/EPA/Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Pakistan ta ce ƙungiyar Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP) - wadda ake kira da Taliban ta Pakistan - na kai hare-hare a cikin ƙasar, kuma daga Afghanistan ake kitsawa, kuma gwamnatin Taliban na Afghanistan ɗin ba ta hana ba.
"Bayan Taliban ta karɓi mulki a Afghanistan, sai Pakistan ta yi tsammanin ƙungiyoyi irin su TTP za su daina samun goyon baya, sannan za su samu sukuni a bakin iyakoki, amma hakan bai samu ba," in ji tsohon jami'in diflomasiyya na Pakistan Masood Khan a zantawarsa da BBC.
"Ba kamar sauran gwamnati ba, Taliban tsarinta daban ne. Sun samu nasarar komawa mulki ne da taimakon TTP," in ji ɗanjarida Sami Yousafzai, wanda ke bibiyar alaƙar Afghanistan a Pakistan a zantawarsa da BBC.
"Idan har Pakistan na tunanin Taliban ɗin Afganistan za ta fatattaki TTP, kamar tana mafarki ne kawai."
A watan Oktoban bara, ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi ya ziyarci New Delhi domin gyara alaƙar da ke tsakanin Afghanistan da India, wadda ba ta ga maciji da Pakistan.
A watan Oktoban bara, ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya zargi Afghanistan da "taimakon Delhi a yaƙi" a wata tattaunawarsa da tashar Geo News.
Ita dai India ta sha nanata cewa ba ta da hannu a taimakon masu adawa da gwamnatin Pakistan a Afghanistan.
Masu bincike suna ganin India na so ne ta sa hannu a yankin, ita kuma Taliban na ƙoƙarin gyara alaƙa ne da ƙasashen yankin.
Amma Yousafzai ya ce zai yi wahala, "saboda India za ta sha wahala wajen taimakon gwamnatin Taliban domin suna amfani ne da fahimtar jidahi."
Wataƙila wannan ne zai daɗaɗa wa Islamabad.

Asalin hoton, Hussain Ali/Anadolu Agency via Getty Images
Me ƙasashe ke cewa?
Bayan wannan harin na baya-bayan nan a Kabul, China ta yi kira da a tsagaita wuta, inda ta buƙaci Pakistan da Afghanistan da su "ɗaga ƙafa wajen rikice-rikicen tare da tabbatar da zaman lafiya."
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya kuma tattaunawa da takwarorinsa na Pakistan da Afghanistan ta wayar tarho game da rikicin.
Wakili na musamman kan haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Richard Bennett ya wallafa a shafinsa na x cewa, "yana baƙin ciki kuma ya shiga damuwa na ganin hare-haren" da suka yi sanadiyar kashe fararen hula.
"Ina kira ga dukkan ɓangarori da suka yi haƙuri su mayar da zuciya nesa, sannan a duba dokokin ƙasa da ƙasa, ciki har da kare fararen hula da ababen more rayuwarsu ciki har da asibiti a sauransu," in ji shi
A baya ma Iran mai maƙwabtaka da ƙasashen biyu ta yi yunƙurin shiga tsakani domin samar da maslaha, inda ministan harkokin wajenta, Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce akwai buƙatar su samu maslaha a tsakaninsu ta hanyar zama a teburin tattaunawa.
Da Pakistan da Afghanistan akwai bakin iyaka da ya kai kusan kilomita 2,600, wanda ake kira da layin Durand.
Birtaniya ce ta shata layin iyakar a 1893, kuma ana takun-saƙa kansa tsakanin Afghanistan da miliyoyin ƴan ƙabilar Pashtuns da ke ɗaya ɓangaren.
Dubban mutane ne suke wucewa ta bakin iyakar a kullum. Duk da saɓanin da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu, al'umomin da suke kusa da bakin iyakar na ci gaba da gudanar da rayuwarsu a tare.











