'Tun da Buhari ya yi shekara takwas, dole Tinubu ya yi wa'adi biyu'

Asalin hoton, Tinubu X
Daya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce dole ne a bar shugaban ya yi wa'adi na biyu a mulkinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da damar yin shekara takwas.
Mai bai wa shugaban na Najeriya shawara na musamman a kan yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana haka ranar Alhamis, a matsayin martani ga tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a kan kalaman da Atikun ya yi game da tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Onanuga ya ce, dole ne Shugaba Tinubu ya kammala wa'adi biyu a mulki, yana mai kafewa cewa dole ne Kudu ta ci gaba da rike shugabancin kasar har zuwa 2031.
''Tun da Buhari ya kammala shekara takwas dinsa, shi ma Tinubu dole ya kammala nasa,'' kamar yadda Onanugan ya rubuta a shafinsa na X, ranar Alhamis.
Ya kara da cewa: ''Abin da kawai Atiku ya kamata ya yi shi ne ya manta da batun sake yin takara, saboda har yanzu lokaci ne na Kudu a zaben 2027.''
Onanuga ya yi martanin ne kan kalaman da Atiku ya yi ranar laraba a lokacin hira da tashar talabijin ta Arise TV, cewa shi bai yarda cewa har yanzu lokaci ne da Kudu za ta ci gaba da rike mulki a 2027 ba.
A lokacin hirar Atiku ya yi watsi da ikirarin cewa akwai yarjejeniya ta kasa kan karba-karbar mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Ya ce: "A'a, ina ganin wannan kuskure ne, ba daidai ba ne ka ce akwai yarjejeniya a kan batun karba-karba a Najeriya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Bari na gaya ma, jam'iyyar kawai da take da tsarin karba-karba a tsarin mulkinta ita ce PDP. Dukkanin sauran ba su da shi.
''Saboda haka idan ma da wani abu, sai dai a ce dukkanin sauran jam'iyyun na kwaikwayo ne ko koyi da tsarin karba-karba na PDP,'' ya ce.
Duk da haka Atikun ya ce yana goyon bayan tsarin na karba-karba.
Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, na jam'iyyar PDP , ya ce Kudu ta rike mulki tsawon shekara18, tun 1999, idan aka kwatanta da Arewa wadda ta yi shekara 10, yana mai cewa wannan bambanci ya saba batun raba daidai na karba-karba da ake yi.
Ya ce: "To wanene, aka raga idan har za mu yi gaskiya ?" Yana mai kare matsayinsa cewa karba-karba ba tsari ne na dokar kasa ba, illa kawai zabi ne na jam'iyya.
A kan hakan Onanuga ya bayyana kalaman na Atiku a matsayin na son-kai, da kuma yunkurin rikita tarihin dalilin tsarin na karba-karba tsakanin Arewa da Kudu.
Ya rubuta cewa, "Wannan Atikun ba zai taba koyar darasi ba,'' yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya a baya ya taba watsi da tsarin na karba-karba a PDP, kuma wannan ne ya kai ga kayen da yake sha a zabe.
Kakakin na Tinubu ya kara da cewa takarar Atikun ta zaben shugaban kasa na 2023 ta saba da tsarin cikin gida na PDP, inda dan takarar Kudu zai yi shekara takwas, bayan wa'adin shekara takwas na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Mista Onanuga ya kara da cewa matsayin Atiku na yanzu ya saba da tsarin siyasar da ya biyo bayan mulkin Buhari, tsohon shugaban kasa daga jihar katsina a Arewa, zuwa ga Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagos daga Kudu.
Ya ce tsohon shugaban kasan yana da tarihin yin watsi da tsarin karba-karba wanda 'yan kasa da dama sun amince da shi, tsarin da ya bayar da dama a yi karba-karba a shugabancin najeriya a tsakanin Arewa da Kudu duk shekara takwas, wanda ba rubutawa aka yi ba.
Onanuga ya yi watsi da ikirarin Atiku cewa Kudu ta yi mulki fiye da Arewa tun 1999, inda ya bayyana hakan a matsayin lissafi na sonkai, wanda ya kawar da kai daga yanayin da ke tattare da rasuwar tsohon shugaban kasar, Umaru Musa 'Yar'adua a 2010, lamarin da ya kai ga tsohon mataimakin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gaje shi.
Ya ce, wannan sauyi da aka samu a sanadiyyar mutuwar ta 'Yar'adua bai bata tsarin na karba-karba ba a tsakanin bangarorin kasar biyu.
Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ne daga jihar Katsina, ta da ke Arewa a Najeriyar, yayin da Shugaba Tinubu yake daha jihar Lagos ta Kudanci.
Shi kuwa Atiku, wanda yake daga jihar Adamawa ta Arewacin kasar, kuma ake masa kallon wanda ke gaba-gaba wajen samun takarar shugaban kasa a jam'iyyar hadaka ta hamayya ta ADC a zaben 2027.











