Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?

Hormuz

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke, sai maganar mashigar Hormuz ta fara faɗaɗa da jan hankali, inda mutane suke ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Birtaniya wato M16, Sir Alex Younger ya shaida wa BBC cewa daga cikin manyan matsalolin da yaƙin zai haifar akwai datse tekun. "Datse tekun zai haifar da matsalar tattalin arziki mai girma saboda yadda zai shafi farashin man fetur."

A ina mashigar take?

Taswirar da ke nuna mashigar
Bayanan hoto, Taswirar da ke nuna mashigar

Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne.

Taswirar tekun ta nuna ɓangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin ɓangarorin biyu.

Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb - inda ake takun-saƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa kan mallakinsa.

Masana sun ce yaƙi na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.

Muhimmancin mashigar

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.

Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.

Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.

Farfesa Ahmad Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur da iskar gas da ke jami'ar Philomath da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce hanyar ruwa ce da ba ta girma sosai, amma take da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

"Ita wannan mashiga hanyar ruwa ce wadda tsayinta bai wuce kilomita 33 ba, wadda ta a daidai ƙasar Iran. Kuma hanya ce da jiragen dakon ɗanyen man fetur ke wucewa a kullum."

Ya ce daga jiragen dakon man da ke wucewa ta hanyar, akwai na ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Iraqi da sauransu.

"Kullum ana wucewa da gangar ɗanyen mai kusan miliyan 20. Kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai da ake buƙata a duniya," in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa ƙasashen da aka hana fitar da su ne suka fi sayar da man fetur mai sauƙi a kasuwannin duniya, wanda a cewarsa hakan ke taimakawa wajen rage farahinsa.

"Su ne suka sayar da mai mai arha. Misali Iran, kowace ganga tana kashe mata dala 10 zuwa 15 ne, kuma haka sauran suke kashewa. Idan aka ce waɗannan ƙasashen ba sa fitar da mai, sannan kuma dama na sauran ƙasashen yana da tsada, sai farashinsa ya tashi."

Ya yi misali da ƙasar China, wadda ya ce kimanin kashi 90 na ɗanyen da take buƙata daga Iran take saye.

Farfesa Ahmad ya ƙara da cewa datse mashigar zai shafi duniya ne baki ɗaya, ba ma ƙasashen da yake yaƙin ba kaɗai.

"A duk lokacin da farashin mai ya tashi, tattalin arzikin duniya na girgiza, farashin kayayyaki na hauhawa. Wanda hakan ya nuna cewa kowa ma zai ji."

Ya ƙara da cewa ita kanta Iran da ta rufe mashigar za ta ji a jikinta, "saboda tana samar da aƙalla ganga miliyan huɗu a kullum wanda shi ne kashi biyar bisa 100 na ɗanyen man duniya," in ji shi, wanda ke nufin za ta samu ragowar kuɗin shiga.

Akwai wata hanya daban bayan tekun?

Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da suka gabata ne ya sa ƙasashen da suke dakon man fetur a yankin suka samar da wata hanyar daban.

Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.

A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi ɗaukar ɗanyen man fetur.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta haɗa gaɓar tekunta na tudu da gaɓar Fujairah da ke gaɓar Oma da bututun da zai iya ɗaukar gangan mai miliyan 1.5.

A watan Yulin 2021, Iran ta ƙaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gaɓar Oman. Yanzu haka bututun zai iya ɗaukar ganga 350,000 a kullum.

Rahoton EIA ta ƙiyasta cewa waɗannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum - kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.