'A gabanmu aka yi wa wata fyaɗe har ta mutu' - Yadda fyaɗe ya zama ruwan-dare a wasu sassan Sudan

Wasu mata ɗauke da itacen girki a sansanin ƴangudun hijira na Al Afad

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Cin zarafin lalata ya zama ruwan dare a Sudan har ma a yankunan da ba a rikici
    • Marubuci, Barbara Plett-Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani sabon rahoto da Ƙungiyar Likitoci ta MSF ta fitar ya ce fyaɗe da cin zarafin mata ya zama ''jiki'' a wasu yankunan Sudan.

Ƙungiyar ta ce lamarin ya kai matakin da ko da yaƙin ya ƙare da wahala a iya kawar da wannan matsala da wuri.

Cikin rahoton MSF ta kira matsalar ''mummunar makomar Sudan'' a yaƙin, tana mai cewa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ne ke assasa matsalar tare da amfani da cin zali da cutarwa.

MSF ta ce yawan cin zarafin mata da fyaɗe ya kai matakin ''zama jiki'' a rayuwar al'umomin yanmmacin Darfur, waɗanda a yanzu ba sa cikin rikici.

Rahoton ya tattaro bayanan cin zarafin mata a tsawon kusan shekara uku da aka kwashe ana yaƙin Sudan.

Gargaɗi: Wannan maƙala na ɗauke da bayanan cin zarafi na lalata ga mata, waɗanda ka iya tayar da hankali.

An gina labarin ne kan labaran wasu mata aƙalla 3,396 da aka ci zarafinsu, waɗanda ƙungiyar MSF ta yi wa magani a asibitocinta da ke Arewaci da Kudancin Darfur tsakanin watan Janairun 2024 zuwa Nuwamban 2025.

Ɓangarorin da ke yaƙi da juna - Sojojin Sudan da mayaƙan RSF - duka an zarge su da hannu a wannan matsala ta cin zarafin mata ta lalata da fyaɗe.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma Darfur ce matattarar mayaƙan RSF, kuma mafi yawan waɗanda ke aikata laifukan mayaƙan ne, a cewar waɗanda aka ci wa zarafin.

Mafi yawan cin zarafin da rahoton ya tattara sun faru ne a North Darfur, ɗaya daga cikin cibiyoyin rikicin Sudan a shekarar da ta gabata, bayan da RSF ta ƙwace sansanonin ƴan gudun hijira na Zamzam da na Abu Shouk da kuma birnin El-Fasher a watan Oktoba, wanda MSF ta kira ''ɗaya daga cikin lokuta mafiya tayar da hankali''.

Ƙungiyar ta ce fiye da kashi 90 cikin 100 na waɗanda aka ci zarafinsu, sun ce an aikata musu ne yayin da suke bulaguro daga waɗannan yankuna zuwa garin Tawila, wanda ke da kariya.

Hare-haren da ake kai musu a hanya sun ƙungiyar fyaɗen taron dangi da razanarwa ta hanyar dukansu ko ma kashe danginsu.

"Sun ɗauke mu zuwa wani fili," kamar yadda wata mace da rahoton ya ambato ke cewa.

"Mutum na farko ya min fyaɗe har sau biyu, mutum na biyu ya yi sau ɗaya, mutum na uku kuwa har sau huɗu, sai mutum na huɗu da ya yi sai ɗaya shi ma,'' in ji ta.

"Baya ga fyaɗen sukan zane mu da manyan bulali, sannan sun riƙa saka min bakin bindiga a goshi na'', a cewar wata yarinya mai shekara 15, wadda ta ce maza uku sun yi mata fyaɗe.

''Mun kwashe tsawon dare suna yi mana fyaɗen,'' kamar yadda ta yi bayani.

A cewar wata mata da ita ma aka yi wa fyaɗe "A gabanmu mayaƙan RSF suka yi wa wasu mata biyu fyaɗe a sansaninmu, mayaƙa huɗu ne zuwa biyar suka ci zarafin matan biyu, a nan ne wata budurwa mai shekara 22 ta mutu''.

Rahoton ya nuna yadda mayaƙan ke amfani da ƙabilanci wajen cin zarafin matan.

MSF ta ce masu aikata fyaɗen na far wa ƙabilun da ba na Larabawa ba, kamar ƙabilun Zaghawa da Massalit da kuma Fur.

Jagorancin RSF ya amince da cewar ''ɗaiɗaikun mayaƙan ƙungiyar sun saɓa dokoki'', a lokacin ƙwace birnin el-Fasher amma ƙungiyar ta ce tana bincike kan yawaitar cin zarafin, wanda ta ce ana zuzuta batun ne kawai.

Yawaitar labaran sanya ƙabilanci kan cin zarafin mata a Darfur ya jima a wannan yaƙi, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Rahoton ya lura cewa cin zarafi na lalata ba ya raguwa, ko kuma yaƙi ya ragu a wani yanki, saboda yadda aka mayar da shi ruwan dare a lokacin tsananin yaƙin.

Kamar yadda fyaɗe ya zama jiki a Darfur ta Kudu, wanda ba a yaƙi a cikinsa, a cewar rahoton na MSF.

Rahoton ya ci gaba da cewa fiye da mutum 1,300 na waɗanda aka ci zarafin su, wato kashi 56 cikin 100 na waɗanda suka nemi taimako a asibitocin MSF a jihar an yi musu fyaɗe ne a lokacin da suke gudanar da ayyukansu kamar neman itacen girki, ko aiki a gona ko ma a hanyarsu ta zuwa gonar.

"A kowace rana, idan mutane suka tafi kasuwa, akan samu labarai huɗu ko biyar na auka wa mata,'' a cewar wata mata mai shekara 40.

"Hakan na faruwa idan muka tafi gona. Maza ne za su rufe fuskokinsu, sannan su yi miki fyaɗe... kuma babu yadda za ka yi dole ka haƙura, hanya ɗaya da za ki kauce wa hakan shi ne ki zauna a gida.''

"Mu uku ne ke zaune sai gwaggonmu,'' a cewar wata budurwa mai shekara 20.

"Sai wasu sojoji uku suka zo mana. Sun ɗauki kowacenmu zuwa wani wuri daban, duka suka yi mana fyaɗe, yanzu haka yayata ta samu ciki sanadin wannan fyaɗen... na ji baƙin cikin wannan al'amari,'' in ji ta.

"Na ji takaicin wannan abu... Hakan na faruwa da ƴanmata , a kowace rana a yankinmu. Kullum ana yi wa ƴanmata fyaɗe.''

A Darfur ta Kudu, kashi 68 na wadanda aka ci zarafinsu sun ce masu riƙe da makaman sun riƙa dukansu, duk da cewa sun gane wasu daga cikin wadanda suka yi musu fyaɗen ciki har da fararen hula, da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma ƴan'uwansu na kusa.

Kashi ɗaya cikin biyu na matan da aka yi wa fyaɗe a wannan jiha ƴan ƙasa da shekara 18 ne, yayin da 41 daga cikinsu ƴan ƙasa da shekara biyar.

MSF ta ce alƙalumanta sun bayyana labaran da kawai ta samu daga matan da suka je asibitocinta, tana mai cewa

Ƙungiyar agajin ta ce akwai gazawar ayyukan agaji wajen taimaka wa mutanen da aka ci zarafinsu, inda ta yi kiran ɗaukar matakan da suka dace.