Yadda matasa a Gombe suka far wa malami kan kausasa harshe ga malamansu

An daɗe ana ta yin kiraye-kirayen sanya dokar wa'azi a jihohin Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar ƴansandan jihar Gombe ta ce ta ceto wani malamin addinin Musulunci na ƙungiyar jama'atul IIzalatul bidi'a Wa'iqamatus Sunnah ta tura zuwa garin Dirin Fulani da ke karamar hukumar Nafada a jihar ta Gombe.

Ƙungiyar ta dai tura malamin ne domin yin tafsirin shekara-shekara na watan Ramadan bayan da wasu matasa mabiya ɗariƙa suka yi yunƙurin farma sa.

An dai ce matasan sun rutsa Malamin ne a wani gida bayan zargin sa da yin kalaman da ba su kamata ba kan shehunansu na darika.

Harin da aka kai wa Malam Abubakar Mahmoud Puma ya faru ne a ƙarshen mako kamar yadda rundunar ƴansandan ta Gombe ta sanar.

Abin da ya faru

Bayan da baturen ƴan sandanmu wato DPO ya je garin na Nafaɗa abin da ya fara yi shi ne kwantar da tarzoma sannan ya nemi tattaunawa da matasan da suka tsare malamin a cikin gidan kasancewar wannan batu ne da ya shafi addini yana buƙatar a yi takatsantsan.

"Hakan ne ya sa shi baturen ƴansandan ya samu damar kuɓutar da malamin ba tare da salwantar rai ba ko kuma jikkata.

"Bayan samnun nasarar kuɓutar da malamin daga garin na Fulani, an kai shi cikin garin ƙaramar hukumar Nafaɗa domin a tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya sannan kuma a ji bayanai daga tambayoyin da aka yi masa dangane da abin da ya faru - wato a ji daga ɓangarensa. Sannan kuma daga bisani sai aka miƙa shi ga iyalansa."

Me ya janyo al'amarin?

Bayanai sun nuna cewa matasan sun far wa malamin ne a wurin wa'azi abin da ya tilasta shi shiga cikin wani gida sakamakon zargin da suka yi masa na yin kalaman ɓatanci ga shehunnai da malamansu.

Wani malamin addinin Musulunci da BBC ta tuntuɓa wanda kuma ba ya son a ambaci sunansa ya ce wannan ita ce babbar barazanar da Musulmin Najeriya ke fuskanta a wannan zamani.

"Wato mun sha faɗa cewa akwai matsala a harkar wa'azi a arewacin Najeriya. Da dama masu wa'azi suna barin mauru'in da suke magana a kai su koma suka da zagi da cin mutumcin waɗanda suke da saɓanin fahimta da su.

Lallai ba a ce idan gaskiya ta biyo ta kan kowane ne ko kuma kowane irin aiki ne a yi magana a kansa ba amma kuma cikin hikima ba tare da kama suna ba."

Dalilai uku da ke janyo rikici kan banbancin fahimta

Malamin addinin Musuluncin ya kuma zayyana wasu dalilai uku da ya ce su ne ke janyo irin wannan matsala waɗanda ya ce idan dai ba a magance su ba to za a ta samun afkuwar hakan a nan gaba.

  • Rashin sanin hanyoyin isar da saƙo: Da yawa malamai ba su san hanyoyin isar da saƙo ba a lokacin wa'azi. Ba zai yiwu ba ka zo kana wa'azi kana kiran sunan Shehuna ko malamina kana ci masa mutunci na zura maka ido ba. Wannan halayyar ɗan adam ce. Saboda haka dole ne masu wa'azi su nemi sanin hanyoyin isar da saƙo cikin hikima.
  • Rashin juriya: Su masu wa'azin da waɗanda suke yi wa wa'azin gabaɗaya ba su da juriya ga waɗanda suke da saɓanin fahimta da su. Misali shi mai wa'azi ya kamata idan karatu ya biyo ta kan wanda yake da saɓanin fahimta da su to ya yi cin hikima ba tare da cin mutunci ba. Shi kuma wanda ya ji an taɓa aƙidarsa to ba hari zai kai ba. Akwai hanyoyin mayar da martani cikin ilimi ko kuma su kai gaban hukuma.
  • Rashin dokokin wa'azi: Mun sha faɗa wa gwamnatoci cewa dole ne fa sai an samar da dokokin wa'azi a Najeriya domin sanya linzami ga bakunan malamai. A yau malamai sun mayar da mumbarin wa'azinsu da dandalin sauke fushi da takaici da ɗaukar fansa da mayar da martani da ma sukar gwamnati. Saboda haka muna kira ga hukuma da ta samar da dokokin wa'azi.