Kun san dalilin da ya sa bahayarku ke tsayawa a saman ruwa?

Wurin yin ba-haya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nagarajan Kannan ya yi ƙoƙarin gano amsar tambayar abin da ya sa ba-haya ke tsayawa a saman ruwa a wasu lokuta.
    • Marubuci, Richard Gray
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editor, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 3

Shin ba-hayarku na nitsewa ko kuma tsayawa a saman ruwa? Kun taɓa ganin ba-hayarku ya tsaya a saman ruwa?

Masu bincike sun ce amsar wannan tambaya na kunshe ne wasu sirruka na lafiya.

Tambaya ce bambara-kwai ga mutane, ko da a cikin sakon imail ne.

Sai dai buƙatar gano amsar wannan tambaya ta jagoranci wani darekta Nagarajan Kannan, a cibiyar ƙwayoyin halitta a Minnesota da ke Amurka, zuwa ga wani bincike na musamman.

Nagarajan, wanda ya shafe tsawon rana yana bincike kan ƙwayoyin halitta da kuma cutar kansar mama, ya fuskanci matsala a lokutansa na hutu.

Wannan shi ne matsalar da ta sa wani lokaci ba-haya ke tsayawa a saman ruwa.

A ƙoƙari na gano amsar, Nagarajan ya samu damar gano wasu abubuwan ban mamaki kan abin da ke faruwa a cikin jikinmu da kuma ƙananan halittu da ke rayuwa a can.

Masu bincike sun gano cewa rage yawan nau'in gas a cikin ba-haya zai taimaka masa wajen nutsewa.

Nagarajan ya mayar da hankali kan wannan ɓangare ne.

A shekarun baya-bayan nan, ɓangaren kimiyyar lafiya ya yi ta gano irin rawar da ƙananan halittu ke yi a ɓangarorin lafiyarmu da dama, dama yawan ƙiba da cutukan zuciya.

Ya bayyana cewa ƙwayoyin bacteriya da fungi da sauran ƙananan halittu, na cikin miliyoyin ƙwayoyin halitta da ke taka rawa yanda ba-baya ke kasancewa.

Mutum na ba-haya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu abubuwa kamar abincin da muke ci, shan sigari da kuma yawaitar amfani da magunguna kan janyo sauyi na ƙwayoyin bacteriya a cikin mutum.

Me bincike kan ba-hayar ɓeraye ya gano?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Abin da ya fi janyo tsayawar ba-haya a saman ruwa shi ne na abubuwa da ke kunshe cikin abincin da muke ci da kuma ƙwayar bacteriya," a cewar Nagarajan.

Domin gwada wannan bincike, Nagarajn da abokansa a asibitin Mayo sun yi amfani da ba-hayar ɓeraye.

Tawagarsa ta gano bayan saka ƙanana halittu a cikin ɓerayen cewa, ba-hayarsu na tsayawa a saman ruwa. Wannan ya ba su damar gano abin da ya janyo ba-hayar tsayawa.

Nagarajan ya ce ba-hayar ɓerayen da ba su da ƙanana halittu sun fi ƙarfi kuma suna nitsewa.

Don haka tawagarsa ta yi wa ɓerayen da ba-hayarsu ta ta nutse da kuma waɗanda na su ya tsaya a saman ruwa allurar ƙananan halittu.

Bayan nan, ba-hayar waɗannan ɓerayen ya tsaya a saman ruwa. Wannan na nufin masu binciken sun gano cewa sun ƙara musu ƙwayoyin bacteriya.

Daga bisani, lokacin da aka saka ƙwayoyin bacteriya na jikin ɗan'adam a ɓerayen, ba-hayarsu ta tsaya a sama.

Abin da ke nufin cewa ba-haya na tsaya a saman ruwa ko da waye ne mai ƙwayoyin bacteriyan, a cewar Nagarajan.

Tawagarsa ta kuma yi bincike mai zurfi kan ƙwayoyin bacteriya da ke cikin ba-hayar ɓeraye, inda suka gano nau'in bacteriya har guda goma da ke janyo sinadrin gas.

Wanda ya fi cikinsu shi ne mai suna Bacteroides ovatus, wanda ya ƙware wajen fitar da sinadarin gas.

Wannan ne dalilin da ya janyo ba-hayar ɗan'adam ke tsayawa a saman ruwa.

Wata mata tana tsalle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nagarajan ya ce akwai buƙatar gudanar da ƙarin bincike domin gwada binciken da aka yi kan ɓeraye kan ɗan'adam.

'Ba-haya na nutsewa idan aka yi amfani da magunguna'

Nagarajan ya yi imanin cewa ana buƙatar gudanar da ƙarin bincike domin gwada binciken da aka yi kan ɓeraye a kan ɗan'adam, kuma ƙarfi da ba-hayar ɗan'adam ke yi manuniya ce kan sauyin da ake samu a cikin na'ukan bacteriya da ke ciki.

Ya ce idan aka yi amfani da magungunan kashe cutukan da ƙwayoyin bacteriya ke haddasawa, ba-haya na nutsewa maimakon tsayawa a saman ruwa. Sai dai ya hakikance cewa babu wanda ya yi bincike kan hakan a yanzu.

Nagarajan ya ƙara da cewa ba abu ne mai sauki ba samar da kuɗaɗe don yin irin wannan bincike.

Wasu abubuwa kamar abincin da muke ci, shan sigari da kuma yawaitar amfani da magunguna kan janyo sauyi na ƙwayoyin bacteriya a cikin mutum.

Nagarajan yana da burin yin bincike don gano abin da ke janyo ƙwayoyin bacteriya masu ɗauke da sinadarin gas a cikin ba-haya.