Me ya sa jam'iyyu suke mayar da takarar zaɓen 2027 kudancin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
A daidai lokacin da guguwar siyasar zaɓen 2027 ke fara kaɗawa a Najeriya, tuni an fara tattaunawa ne kan ƴan takarar da za su wakilci manyan jam'iyyun ƙasar, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.
A ranar 24 ga watan Maris ne Jam'iyyar Labour wato LP ta sanar da mayar da takararta zuwa kudancin ƙasar, wanda hakan ke nufin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027 daga yankin kudanci zai fito.
Shugabar riƙon-ƙwarya ta jam'iyyar, Nenadi Usman ce ta bayyana haka bayan wani taron ganawa da ta yi da Hukumar INEC a Abuja.
Ta ce, "mun yanke shawarar cewa ba za mu tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga yankin arewacin Najeriya ba. Mun mayar da takarar zuwa kudancin Najeriya," kamar yadda ta bayyana.
Sai dai ta ce duk da cewa ba za su ba ɗan arewa takara ba, za su yi amfani da dokokin zaɓe da na ƙasa wajen tsayar da ƴan takara a jam'iyyar.
A game da ko suna da tsayayyen ɗan takara, Nenadi ta ce har yanzu ba su da wani wanda suka cire.
"A game da wane ne ɗantakararmu gaskiya ba zan iya faɗa ba, domin hakan zai zama tamkar ba zaɓe za mu yi ba. Don haka duk wanda ƴaƴan jam'iyya suka zaɓa, shi ne zai zama ɗan takararmu," in ji tsohuwar ministar.
Jam'iyyun da suka mayar da takara kudu
A babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023 ma dai LP ɗan kudancin Najeriya ta tsayar, inda tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya tsaya mata takara, kuma ya taka rawar gani sosai a zaɓen.
Yanzu haka dai za a iya cewa alamu sun nuna cewa jam'iyya mai mulki a ƙasar wato APC a kudancin ƙasar za ta tsayar da ɗan takara, ganin shugaban ƙasar mai ci a yanzu, Bola Tinubu ɗan kudun ne, kuma bisa ga dukkan alamu shi ne zai sake tsaya mata takara.
Haka kuma ana hasashen daga cikin abubuwan da suka ƙara ta'azzara rikicin cikin gida a PDP akwai batun tsayar da ɗan takara daga kudancin Najeriya, wanda hakan ya sa ake hasashen a zaɓen mai zuwa ma daga kudu za ta ciro ɗan takararta na babban zaɓen.
Jam'iyyar haɗaka ta ADC ce ake tunanin akwai manyan ƴan takara uku Atiku Abubakar daga arewacin Najeriya da Peter Obi da Rotimi Amaechi daga kudancin Najeriya.
'Dabara ce'

Asalin hoton, Kabiru Sufi Said/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A daidai lokacin da masana da masu bibiyar harkokin siyasar Najeriya ke ci gaba da tattaunawa kan tsarin tsayar da ƴantakara, Dr Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya ce kowace jam'iyya na da dabara.
"Ina gani suna ƙoƙarin kamaceceniya ne da jam'iyya mai mulki, ko kuma suna so ne su samu daidaito a yunƙurin da ake yi na karɓa-karɓa tsakanin yankunan ƙasar," in ji shi.
Ya ce wataƙila suna haka ne domin ya kasance bayan yankin kudu, sai duka manyan jam'iyyun su mayar da hankali arewa.
Sai dai ya ce ba za a rasa wasu jam'iyyun da za su tsayar da ɗan arewa ba, "saboda kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin zaɓe ba su hana ba. Lissafi ne kawai na jam'iyyu, amma wata jam'iyyar za ta iya fitar da ɗan arewa don neman cin moriyar ƙuri'un arewa."
Masanin harkokin siyasar ya ce yana ganin ba dabara ba ce mai kyau a ce an fi mayar da hankali kan kudancin ƙasar.
"Domin wasu na gani idan jam'iyyu da yawa suka fitar da ɗan kudu, duk wadda ta fitar da ɗan arewa za ta fi samun ƙuri'a, musamman na yankin arewacin. Saboda haka za a iya cewa wannan rashin dabara ce saboda za a iya raba ƙuri'un kudu," in ji Sufi.
Sufi ya ƙara da cewa kasancewar kowace jam'iya na da tsare-tsare da dabarunta, "wataƙila duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan kudu, tana da ɗan takara ne mai ƙarfi daga kudancin da take ganin zai fi taka rawar gani."
A game da yanayin yadda guguwar siyasar ke kaɗawa, Kabiru Sufi ya ce yanzu guguwar ta fara kaɗawa sosai, duk da a cewarsa, an yi zaton tun baya ne jam'iyyun hamayya za su fara motsin da ake gani yanzu.
"Yanzu dai kallo ya koma sama kan wane ƙoƙarin jam'iyyun hamayya za su yi wajen gyara gidansu wajen samu matsaya guda ɗaya, duba da jam'iyya mai mulki ta mayar da hankali kan ƙoƙarin ganin gwamnoni ne kan gaba wajen shiga zaɓe."
Ya ce ana ganin mafitar jam'iyyun hamayya ita ce haɗewa a inuwa ɗaya domin tunkarar babban zaɓen.
"Gamayyar jam'iyyun hamayya ta yi magana kan gyare-gyaren da suke so a dokokin zaɓe, sannan jam'iyyu sun fara magantuwa. Yanzu dai alamu na nuna cewa jam'iyyun su fara farkawa. Shi ya sa ake gani yanzu an fara ganin guguwar da aka yi tunanin a fara gani shekara biyu da suka gabata," in ji shi.











