Al-Ittihad na zawarcin Salah, Barcelona na neman Bastoni

A 2023 Al-Ittihad ta gabatar wa Liverpool tayin £150m kan ɗanwasan gaban Masar Mohamed Salah wanda ƙungiyarsa ta ƙi amincewa, amma ƙungiyar gasar ƙwallo ƙafan ta Saudiyya ta dawo da zawarcin ɗanwasan mai shekara 33, wanda zai iya barin Liverpool a kyauta a ƙarshen kakar wasan bana. (ESPN)
Liverpool na bibiyar tsohon kocin Real Madrid kuma tsohon ɗanwasan ta Xabi Alonso, wanda ya taɓa lashe gasar zakarun Turai a Anfield, kuma ana sa ran ɗan Sifaniyan zai maye gurbin Arne Slot a ƙarshen kaka wasan bana (Bild - in German)
Liverpool za ta cike gurbin Salah da ɗanwasan gefen Faransa Michael Olise amma Bayern Munich na jan ƙafa wajen yanke hukunci kan makomar ɗanwasan mai shekara 24 wanda kwangilasa shi da ita za ta ƙare a 2029. (Sport Bild - in German)
Manchester United na bibiyar ɗanwasan RB Leipzig da Ivory Coast mai shekara 19 Yan Diomande da ɗanwasan Newcastle United da Ingila mai shekara 21, Lewis Hall da kuma ɗanwasan Everton da Senegal mai shekara 26, Iliman Ndiaye (Sky Sports)
Ɗanwasan tsakiyar Manchester United da Brazil Casemiro, wanda ke shirin barin United a bana ya amince da wani tanadi da zai iya tsawaita kwantiraginsa da shekara ɗaya (Manchester Evening News)
Manchester United ta bayyana fatamn za ta samu wata ƙungiya da za ta sayi ɗanwasan gabanta mai shekara 28 da ke zaman aro a Barcelona, Marcus Rashford, idan har Barcelona ta zaɓi ƙin sayen shi. (ESPN)
Barcelona na fatan sayen ɗanwasan bayan Inter Milan Alessandro Bastoni amma za ta fuskanci hamayya daga Liverpool kan ɗanwasan mai shekara 26. (Football Italia)
Kocin Newcastle United Eddie Howe ya samu goyon bayan ƙungiyar duk da rashin jituwa da wasu masoyanta bayan rashin nasarar da ya yi a hannun Barcelona a gasar zakarun Turai da kuma wata rashin nasarar a hannun Sunderland a gasar Firimiya. (Times - subscription required)
Ɗanwasan Brazil Vinicius Jr ya ce baya da wani tunani da ya zarce cigaba da taka leda a Real Madrid har na tsawon lokaci














