Ina ne tsibirin Kharg na Iran kuma me ya sa Amurka ke son ƙwace shi?
- Marubuci, Robert Greenall
- Marubuci, Alys Davies
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, security correspondent
- Aiko rahoto daga, in Riyadh
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta ɗaukar mataki kan ƙaramin tsibirin Kharg da ke gaɓar ruwan ƙasar Iran - wanda nan ne rumbun man Iran ɗin da ake yi wa kallon maƙogwaron tattalin arziƙin ƙasar.
Rahotanni a ranar 13 ga watan Maris sun nuna cewa sojojin Amurka sun yi ruwan bama-bamai a tsibirin. Trump ya ce an "gama" da sojojin Iran da ke tsibirin. Sai kuma Trump ya kame daga barin kai wa cibiyoyin Iran ɗin na mai hari.
A ranar Juma'a, jaridar Axios ta Amurka ta rawaito wasu majiyoyi guda huɗu da ke da masaniyar yadda gwamnatin Amurka ke shirin mamaye ko kuma katse tsibirin domin matsa wa Amurka lamba ta buɗe mashigar Hormuz - ɗaya daga cikin hanyoyin sufuri mafi girma da ke a kudancin gaɓar ruwan Iran.
"Sojojin Amurka ka iya ƙwace tsibirin Kharg," wani jami'in fadar White House ya shaida wa BBC a wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa Trump ba shi da wani shiri na aikewa da sojoji zuwa ko'ina amma kuma "yana da dukkan damarmakin ɗaukan kowane irin mataki a matsayinsa na shugaban ƙasa.
A baya dai Trump ya yi gargaɗin cewa zai sake duba yiwuwar kai wa wuraren mai na Iran da ke tsibirin idan Iran ɗin "ta yi wani abun da" zai janyo tsayawar zurga-zurgar jirage a mashigar Hormuz. Tun bayan nan ne Iran ta ci gaba da yin barazanar kai wa jiragen dakon mai da ke shirin wucewa ta mashigar hari.
Aaron Maclean, mai hira a shirin kwalejin yaƙi sannan kuma mai sharhi kan harkar tsaro na gidan talbijin na CBS, ya ce tunanin Amurka shi ne na yiwuwar ƙwace tsibirin domin "tursasa" Iraniyawa su buɗe mashigar Hormuz.
Sojojin Iran sun ce za su lalata dukkannin wuraren mai da iskar gas mallakar kamfanoni da ke da alaƙa da Amurka, idan dai har Amurkar ta kai wa rumbun mai na Kharg hari.
Shin ko Amurka za ta iya ƙwace tsibirin?
Ana ta yada jita-jita na ɗan wani lokaci kan ko dakarun Amurka za su iya gwada ƙwace tsibirin na Kharg.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙwace tsibirin zai yi tarnaƙi ga man da Iran ke fitarwa amma kuma hakan zai iya haifar da yanayin da Amurkar za ta iya ƙaddamar da hare-hare zuwa cikin Iran ɗin.
Majiyoyi sun shaida wa kafar CBS cewa jami'an ma'aikatar tsaro ta Pentagon sun yi cikakken shiri na aikewa da dakaru zuwa cikin Iran.
Bugu da ƙari, bayanai sun nuna cewa dakarun na Amurka na shirin aikewa da dakarun yaƙi na ruwa guda 2,500 tare da jiragen yaƙi zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Ma'aikatar tsaro ta Pentagon da fadar White House sun ƙi yadda su ce uffan dangane da aikewa da sojojin amma kuma sun sha nanata cewa akwai batun a ƙasa.
Ƙwace tsibirin ka iya katse maƙogaron tattalin arziƙin rundunar juyin-juya hali ta Iran, IRGC wanda hakan ka iya nakasa rundunar wajen ci gaba da yaƙi kamar yadda masanin harkar yaƙi Mikey Kay ya shaida.
Maclean ya ce dukkan wani yunƙurin Amurka na ƙwace tsibirin zai zama ƙarami amma kuma mai cike da ƙalubale. Dakarun Amurka dole ne su matsa kusa ko dai ta hanyar ruwa ko kuma ta sama.
Muhimmancin tsibirin Kharg ga Iran
Tsibirin Kharg dai wani ƙaramin wuri ne mai cike da duwatsu da ke da tsawon kilomita a gaɓar ruwan Iran.
Duk da ƙanƙantar tsibirin, ya kasance ɗaya daga cikin wuraren makamashi da ƙasar Iran ke taƙama da su.
Saboda haka kai hari ɗan ƙaramin tsibirin tamkar riƙe maƙogaron tattalin arziƙin Iran ne.
Kaso 90 na ɗanyen man ƙasar Iran na zuwa ne daga rumbun tsibirin da ke sufurinsa ta bututu zuwa cikin Iran ɗin.
Trump ya fayyace cewa akwai yiwuwar kai wa waɗannan bututun hari amma kuma ya ce ya kame daga yin hakan ne domin guje wa matsalar da tattalin arzikin ƙasar Iran ɗin zai tsinci kansa a ciki a nan gaba.
"Za mu iya cimma hakan a cikin minti biyar. An kammala," in ji Trump a ranar 16 ga watan Maris. "Kalma ɗaya tak. Bututun sun gama yawo. Kuma za a ɗauki dogon lokacin sake gina su."
Manyan tankoki da ka iya ɗaukar kimanin galan miliyan 85 na mai za su iya zuwa tsibirin domin ɗaukar man. Gaɓar ruwan tsibirin na kusa da ruwa mai zurfi saɓanin gaɓar ruwa maras zurfi da ke cikin Iran.
Daga nan kuma sai tankokin su koma yankin su bar mashigar Hormuz zuwa China wadda ita ce babbar mai sayen man na Iran.
Rumbun fitar da man na Iran na samar da kuɗin shiga mafi yawa ga rundunar juyin-juya hali na ƙasar wato IRGC.
Me Amurka da Iran suka ce kan harin ranar 13 ga watan Maris?
A ranar 13 ga watan Maris Trump ya ce cibiyar yaƙin Amurka ta Centcom ta ƙaddamar da ɗaya daga cikin mafi girman hare-haren bam a tarihin yankin Gabas ta Tsakiya inda gabaɗaya aka kawar da sojojin Iran da ke tsibirin Kharg.
Ya kuma ƙara da cewa "saboda dalilan sanin ya kamata" ya zaɓi "ka da ya shafe ma'adar man da ke tsibiri."
Centcom ta ce dakarun Amurka sun farmaki sama da "sojojin Amurka 90 da ke tsibirin Kharge amma kuma ta ƙyale rumbum man fetur ɗin da ke tsibirin."
Har wa yau, cibiyar ta Centcom ta ce ta lalata ma'adanar nakiyoyin ruwa da wuraren ɓoye makamai masu linzami da kuma tarin cibiyoyin soji.
Kafar watsa labaran Iran ta rawaito cewa babu wata illa da aka yi wa rumbun man nasu da ke tsibirin. Kafar watsa labarai ta Fars ta ce hare-haren na Amurka sun faru a kan a sama ne da ruwa da cibiyar umarni ta filin jirgin sama da kuma wurin ajiyar jirgi mai saukar ungulu.
Ehsan Jahanian, mataimakin gwamnan lardin Bushehr da ke kudancin Iran, ya ce shirin fitar da mai daga tsibirin Kharg "na ci gaba" ba tare "da matsala", kamar yadda wani rahoton rundunar IRGC ya sanar.
Kuma tun bayan harin, sojin ƙasar ta Iran suka yi gargaɗin cewa za su lalata duk wani kamfani ko matatar mai da ke da alaƙa da Amurka, idan har aka hari rumbun man nasu na tsibirin Kharg.
Me ya hana Amurka kai hari kan rumbun mai a Kharg?
Ayyukan soji domin lalata rumbun mai a tsibirin Kharg zai zama abu mai illa ga ƙasar Iran.
Kuma hakan zai haddasa ruruwar wutar rikicin.
Bugu da ƙari, harin zai ƙara ta'azzara farashin mai a kasuwar duniya sannan zai janyo Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan kamfanoni da matatun mai da iskar gas masu alaƙa da Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.
Makonni uku da fara yaƙi, har yanzu Iran tana da ƙarfin harba jerin makaimai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan ƙasashen Gabas ta Tsakiya da kuma jiragen dakon mai.
Kuma alamu na nuna Iran ɗin ka iya faɗaɗa hare-haren da ka iya kai wa ga cibiyoyin da tashoshin tace ruwa da ke samar da ruwa ga miliyoyin al'ummomin yankin.










