Man U ta ƙwallafa rai kan Lopez, Juventus na zawarcin Rudiger

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin Manchester City da Manchester United na son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Italiya Tonali mai shekara 25 daga Newcastle, duk da cewa tsohon ɗan wasan AC Milan ya fi son komawa ƙasarsa. (Talksport)
An ce White na iya komawa cikin tawagar Ingila, amma akwai yiwuwar ya bar Arsenal a bazara, inda Everton ke zawarcinsa. (FourFourTwo)
Aston Villa na cikin kungiyoyin Premier League da ke duba yiwuwar daukar matashin ɗan wasan gaba na Paris Saint-Germain, Ibrahim Mbaye mai shekara 18 a bazara. (Sky Sports)
Manchester United ta saka sunan ɗan wasan baya na Fulham, Antonee Robinson mai shekara 28 cikin jerin 'yan wasan da take son ɗauka (Football Insider)
West Ham United da Nottingham Forest za su fuskanci gasa daga AC Milan wajen neman ɗan wasan gaba na Bologna, Santiago Castro mai shekara 21. (Tuttomercatoweb)
Manchester United na shirye ta kashe har fam miliyan 86.5 domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Barcelona, Fermin Lopez, amma ɗan wasan mai shekara 22 ba ya son barin kungiyar. (El Chiringuito)
Ɗan wasan gaba na Faransa na Paris Saint-Germain, Randal Kolo Muani mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Tottenham Hotspur, na son komawa Juventus a bazara. (Gazzetta dello Sport)
Crystal Palace na tunanin ɗaukar kocin Bournemouth, Andoni Iraola, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara, yayin da suke neman sabon koci idan Oliver Glasner ya tafi. (Telegraph)
Manchester United ma na ci gaba da nuna sha'awa ga Iraola (Mirror)
Masu kungiyar Chelsea za su ci gaba da bai wa kocin kungiyar Liam Rosenior goyon baya ko da kuwa kungiyar ba ta samu gurbin gasar zakarun Turai ba. (Mail+)
Sai dai kocin Como, Cesc Fabregas, na cikin wadanda za su iya maye gurbinsa idan Chelsea ta yanke shawarar sauya koci. (Teamtalk)
Juventus na bibiyar halin da ake ciki kan ɗan wasan baya na Real Madrid da Jamus, Antonio Rudiger mai shekara 33, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara (Tuttosport)











