Tsauraran matakan da Amurka ke shirin ɗauka kan Iran

Asalin hoton, Getty Images/COLLAGE
- Marubuci, آنتونی زورکر
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, خبرنگار آمریکای شمالی، بیبیسی
- Lokacin karatu: Minti 4
Mako uku tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, rikicin ya yi munin gaske tare da haifar da barazanar rashin tabbas a duniya.
To sai dai ana ganin a daidai wannan lokaci, sakonnin da shugaban Amurka ke fitarwa sun saɓa haƙiƙanin abin da yake a ƙasa.
Ya ce yaƙin "ya kusa zuwa ƙarshe," amma a daidai wannan lokaci, dakarun Amurka, ciki har da dakarun sojin ruwa, na kan hanyar zuwa yankin na Gulf.
Ya kuma ce yaƙin na "raguwa." Amma Amurka da Isra'ila na ci gaba da jefa bama-bamai da makamai masu linzami zuwa Iran, yayin da ita ma Iran ke ci gaba da kai kare-hare cikin Isra'ila da wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
An bayyana Buɗe mashigar Hormuz - wani mihimmin wuri da kashi 20 cikin 100 na man duniya ke bi da wuri - a matsayin ''cuwa-cuwar soji''.
Kawo yanzu jiragen da Iran ta amince wa ne kawai ke wucewa da mashigar.
Mista Trump ya ce an ''ruguza'' rundunar sojin Iran, amma har yanzu jiragen Iran marasa matuƙa da makamai masu linzami na ci gaba da faɗa wa wuraren daban-daban a yankin Gabas ta Tsakiya da Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma shugaban na Amurka ya yi barazanar faɗaɗa rikicin cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya yi gargaɗin cewa idan Iran ba ta buɗe mashigar Hormuz ''duka ba tare da barazana ba'', cikin sa'a 48, sojojin Amurka za su ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin lantarkin Iran, yana mai cewa za a fara hare-haren da ''mafi girmansu''.
Haka kuma Mista Trump ya sake bayyanawa cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin nasa cewa Amurka ta yi ''tattaunawa ta gaskiya- da -gaskiya'' da Iran kuma hakan ne ya sa ya bayar da umarnin ɗage hare-hare kan lantarkin Iran da makamashinta da kwana biyar
A ranar Juma'a, ya sake wallafa jerin manufofin sojojin Amurka a yaƙin Iran a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa Amurka ta ''kusa cimma muradunta''.
Manufofin sun haɗa da lalata ƙarfin sojin Iran, da tsaronta da kuma shirin nukiliyarta da kuma kare ƙawayen Amurka a yankin.
Sai dai kare mashigar Hormuz ba ya cikin jerin, inda shugaba Trump ya ce alhakin hakan ya rataya a wuyan ƙasashen da suka dogara da man yankin Gulf.
Shugaba Trump ya sha nanata cewa Amurka mai fitar da makamashi ce kuma ba ta dogara da man Gabas ta Tsakiya ba.
Amma wannan ra'ayi ya saɓa wa yanayin kasuwar man fetur ta duniya, kasuwar da canjin farashin ke shafar farashin mai a gidajen mai na Amurka kai tsaye.
Sabon saƙon da Trump ya wallafa a shafinsa bai ambaci sauyin gwamnati a Iran ba.
Sakon bai ambaci amincewa ko rashin amincewa da sabon jagoran addinin ƙasar ba, sannan bai yi batun ''miƙa muya ba tare da sharaɗi ba,'' wanda a farkon yaƙi ya kafe kansa.

Asalin hoton, Getty Images
A cikin sabon jerin manufofin na Trump, akwai yiyuwar Amurka za ta kawo ƙarshen ayyukanta yayin da shugabancin Iran na yanzu da ke adawa da Amurka ke ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki, ta ci gaba da fitar da manta, sannan ta ci gaba da aiwatar da iko da mashigin Hormuz.
Idan har kawo ƙarshen yaƙin bai yi wa Trump daɗi ba, yaƙin da shugaban da mashawartansa suka ce ya faro ne tun daga juyin juya halin Iran a shekara ta 1979, kuma gwamnatin ke ƙoƙarin kawo ƙarshensa, akwai wata hanya ta daban da ta shafi amfani da ƙarfin sojojin Amurka, waɗanda yanzu hake ke kan hanyar zuwa Gabas ta Tsakiya.
Tsawon mako guda da ya wuce, kafofin yaɗa labaran Amurka, sun bayar da rahoton cewa ''sojojin ruwan Amurka'' kusan 2,500 da jiragen ruwa na yaƙi da da na sama sun nufi yankin Gabas ta Tsakiya daga Japana, kuma ana sa ran za su isa yankin cikin kwanaki masu zuwa.
Akwai wata kuma tawagar makamnciyar wannan da a baya-bayan nan ba tar sansanonin sojin California da ake sa ran za ta isa yankin zuwa tsakiyar watan Afrilu.
Masu sharhi na cewa Amurka na shirin ƙwace tsibirin Kharg, mai faɗin murabba'in kilomita 21, wadda ta ƙunshi rumbunan man da Iran ke fitarwa.
Irin wannan mataki, zai iya katse yawan man da Iran ke fitarwa, da hana ƙasar samun kuɗin shiga da take buƙata, da kuma tilasta mata amince wa da buƙatun Amurka domin kawo ƙarshen rikicin.
A ranar Juma'a Mista Trump ya faɗa cewa ba shi da niyyar tura sojojin ƙasa zuwa cikin Iran, amma sai ya sake cewa ''idan da buƙatar yin hakan zan faɗa muku''. Manufarsa a yaƙin ba a bayyane take ba.
Wannan barazana ta sanya kafofin yaɗa labaran Iran suka bayar da rahoto a ranar Asabar cewa duk wani hari kan tsobirin Kharg, zai sa IKran ta haifar da ''tashin hankali'' a Tekun maliya, wata muhimmiyar hanyar fiton kayayyaki, tare da ''cinna wuta'' kan cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Gargaɗin na Iran ya nuna irin hatsarin da bazuwar yaƙin da Amurka za ta haddasa, wanda zai sa sojojin Amurka su fuskanci martani daga Iran.
Kwanaki kaɗa da suka gabata, kafofin yaɗa labran Amurka sun bayar da rahoton cewa gwamnatin Trump na shirin neman buƙatar dala biliyan 200 daga asusun gaggawa daga majalisar dokokin Amurka don ci gaba da ayyukan sojin Amurka a Iran.
Kuma wannan buƙata na nuna cewa Fadar White House ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshenyaƙin ba, hasali ma tana shirin tsawaita yaƙin da yawan kashe kuɗi.
To amma martanin farko daga majalisar, ciki har da abokansa na Jam'iyyar Republican ta Mista Trump, sun nuna alamun taka tsan-tsan game da matakin.
Da alama yaƙin Iran ya kai wani matakin da ya kamata a dakata, sai dai babu tabbas game da makomarsa har yanzu.











