Sheikh Abduljabbar ya buĆaci sa bakin babban alĆalin Najeriya a shari'arsa
Sheikh Abduljabbar Kabara ya yi kira ga babban alĆalin Najeriya da ya shiga lamarin shari'ar da yake da gwamnatin Kano.
Malamin addinin musuluncin ya bayyana haka ne a wata wasiĆar Ćorafi da ya rubuta zuwa ga babban alĆalin, inda ya yi zargin ana jan Ćafa da gangan bayan Éaukaka Ćara da ya yi kan hukuncin kisa da aka yanke masa bisa zarginsa da Éatanci ga Annabi Muhammadu.
A wasiĆar, ya yi Ćorafe-Ćorafe da suka haÉa da jan Ćafa da gangan hana shi samun cikakken bayanan shari'ar da zargin rashin daidaito da nuna son kai.
Haka kuma ya yi zargin ba a yi masa adalci a shari'ar, sannan ya dasa alamar tambaya da shakku kan ikon da kotun shari'ar ke da shi na sauraron Ćarar tun a farko.
A watan Disamban 2022 ne kotun shari'ar musulunci a Kano ta yanke wa malamin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin Éatanci ga Annabi a cikin wa'azinsa.
Bayan hukuncin ne malamin ya Éaukaka Ćara, inda ya bayyana cewa ba a masa adalci a Ćaramar kotun ba, sannan ya ce ba a ba shi damar bayyana nasa Éangaren ba, inda ya Ćara da cewa kalaman da ake magana daga littafai ya karanta su, kuma bai karanta da nufin cin mutunci ko Éatanci ga Annabi ba.
Ya Ćara da cewa bai aikata laifi ba, sannan ya ce idan har za a saurara shari'ar da adalci, yana da yaĆinin za a fahimce shi, kuma a wanke shi.