Hanyoyi shida na karya lagon ƙungiyoyin ƴanbindiga

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, ana ci gaba da tafka muhawara kan ƙaruwar hare-hare, musamman a sansanonin sojin ƙasar, da ma dasa bama-bamai a kan manyan tituna musamman a ƴan kwanakin nan.

A kwanakin baya ne dai mayaƙan Boko Haram da ake zargi ƴan ISWAP ne suka yi shigar burtu suka tayar da bama-bamai a ƙwaryar birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa ta gabas.

An yi tunanin rikicin Boko Haram wanda aka fara tun a tsakankanin shekarar 2009 ya zo ƙarshe, ganin yadda jami'an tsaro da gwamnatin Najeriya suka riƙa iƙirarin fatattakar mayaƙan.

Sai dai an ɗan samu sauƙin hare-hare a ƙwaryar birnin na tsawon lokaci, inda ya kasance ƙauyuka da garuruwan bayan gari ne ke cigaba da fama.

A game da abin da masana suke gani kan yawaitar sababbin hare-haren ga tsaron ƙasa, Kabiru Adamu ya ce akwai alamu da ke nua cewa mayaƙan na Boko Haram suna so ne koma cikin Maidduguri.

"Wanda ya ke bibiyar hare-haren na baya-bayan nan zai fahimci cewa niyyarsu ita ce ta shiga ƙwaryar Maiduguri, wannan babban nakasu ne ga tsaron Najeriya," in ji masanin na tsaro.

Haka abin yake a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, inda a ƴan watannin baya mahara suka fara ƙoƙarin mayar da dajin Kainji wata matattarar ƴanbindiga.

Hanyoyin magance matsalar ƴanbindiga

Bayan nasarorin da hukumomin Najeriya suke iƙirarin samu a yaƙin da suke yi da matsalar tsaro, a gefe guda kuma rahotanni na cewa ana sulhu da maharan a wasu jihohi domin samun zaman lafiya.

Sai dai duk da haka ba a samu cikakken zaman lafiya da ake buƙata ba, inda ake cigaba samun hare-hare da kashe-kashe.

Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon security and intelligence limited, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro ya ce akwai wasu hanyoyi guda shida da suka fi dacewa wajen daƙile harkokin ƴanbindiga.

  • Kashe jagororin ƙungiyar
  • Tattauna domin shiga sulhu
  • Ƙungiyar ta samu nasarar cimma abin da take so
  • Ƙungiyar ta rasa cimma burinta
  • A murƙushe ƙungiyar
  • A wayar da kai ƴaƴan ƙungiyar su canja tunani.

Kabiru Adamu za a iya fahimtar nasarorin hanyoyin ta wasu hanyoyi ko alamu da ya bayyana kamar haka:

  • Kamawa ko kashe jagororin ƙungiyar
  • Shigar ƙungiyoyin siyasa ta dimokuraɗiyya
  • Ƙungiyar ta cimma burinta
  • Al'ummar su daina goyon bayan ƙungiyar ko ta watse
  • Ƙungiyar ta daina ta'addanci ta koma wau laifuka
  • Cin ƙungiyar da fatattakarta da ƙarfi

Masanin ya sha nanata cewa ƙarfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen matsalar tsaro ba, inda ya ƙara da cewa sulhu kaɗai ma ba zai bayar da abin da ake so ba, sannan ya ce dole a haɗa hanyoyi ko dabaru da dama domin nasara.

Shawarwari

A maƙalar da masanin ya aika wa BBC Hausa, ya ce binciken da aka yi kan ta'addancin ƙunar bakin-wake, an gano abubuwa.

"Bayan nazartar rahotanni aƙalla 41 daga sashen tsaron cikin gida na Amurka wato DHS, sashen ya bayar da shawarwari da dama. Daga ciki akwai:

  • Magance ƙorafe-ƙorafe ko matsalolin da yankunan mayaƙan ke fuskanta
  • Rage ƙarfin ƙungiyoyin ta hanyar daƙile masu ɗaukar nauyinsu
  • Tura masu kwarmato bayanai a cikinsu
  • Daƙile hanyoyin da suke samun kuɗaɗe
  • Sa ido kan jagororin siyasa da addini da ke da'awar shahada
  • Ƙulla alaƙa da ƙasashen waje domin yaƙi da ta'addanci
  • Sa ida ko matsa lamba kan masu goyon bayan ta'addanci
  • Fahimtar cewa yawan kai musu hare-hare na janyo ransu ya bushe.

Me ya sa aka samu ƙaruwar hare-haren?

Heni Nsaibia, babban mai sharhi kan al'amuran tsaron Afirka ta Yamma ya ce a shekarar da ta gabata ne JNIM ya ɗauki alhakin harin farko a Najeriya.

Sai dai ya ɗora alhakin karuwar hare-haren kan rashin haɗin kai da ke tsakanin ƙasashen yankin musamman bayan da Mali da Burkina Faso da Nijar suka fice daga ƙungiyar Ecowas.

Ya ƙara da cewa babban dajin da ya ratsa kan iyakokin ƙasashen uku ya taimaka wajen ƙaruwar ayyukan masu ɗauke da makaman a kan iyakar.

Binciken na kamfanin Acled ya kuma gano cewa masu iƙirarin jihadin na ƙarfafa kansu a yankin ta hanyar ɗaukar sabbin mayhaƙa daga ƙabilu daban-daban da ke yankin, kamar ƴanbindiga masu fashin daji.

Haka ma binciken ya ƙungiyoyin ne ke iko da hanyoyin safarar kayyaki, musamman man fetur daga arewacin Najeriya zuwa kogin Nijar da Benin.