Da wa Trump zai tattauna bayan da Amurka da Isra'ila suka kashe shugabannin Iran?

    • Marubuci, Kaine Pieri
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Marubuci, Kate Bowie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Marubuci, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 10

An ba sojojin Isra'ila umarnin kai hari kan duk wani jami'in Iran, ba tare da neman izini ba, in ji ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz.

Wannan na zuwa ne bayan da Rundunar Tsaron Isra'ila (IDF) ta kashe manyan jami'an tsaron Iran, ciki har da na baya-bayan nan, Ali Larijani, da kuma ministan tattara bayanan sirri Esmail Khatib.

"Ni da Firaminista Benjamin Netanyahu mun bayar da umarni ga dakarun IDF su kashe duk wani babban jami'in Iran, ba tare da sun nemi izinin aiwatar da hakan ba" in ji Katz.

To amma yaya muhimmancin waɗannan jami'an suke a gwamatin Iran, kuma wa ke da iko a yanzu? Ga yadda tsarin shugabancin Iran yake.

Ayatollah Ali Khamenei - Jagoran Addini (an kashe shi)

Kisan da aka yi wa babban jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khameni, ya ba mutane da dama mamaki, saboda an kashe shi ne a ranar 28 ga watan Fabreru, ranar farko da Amurka da Isra'ila suk ƙaddamar da hare-hare kan ƙasar.

Ayatollah Ruhollah Khomeini, mai shekaru 86 ya shugabanci ƙasar sama da shekaru 30, tun bayan juyin juya-halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979.

Khamenei shi ke da iko da yawancin muƙamai masu muhimmanci. Shi ne mutumin da ya fi kowa ƙarfin iko kuma babban kwamandan rundunonin tsaron ƙasar, ciki har da rundunar juyin juya hali.

Duk da yake bai cika tsanantawa wajen mulkin kama karya ba, amma yana da ƙarfin iko naɗa mutanen da za su riƙe wasu ofisoshi a ƙasar, a wasu lokutan ma ba ya bi ta kan manufofin siyasa ba.

Sai dai ba kasafar Khamenei ke bari wasu dokoki da bai amince da su, su yi tasiri ba.

Mojtaba Khamenei - Jagoran Addini (yana raye)

Har yanzu ba a ga Mojtaba Khamenei cikin jama'a ko samun hotunansa da bidiyo ba, tun bayan sanar da shi matsayin magajin mahaifinsa a ranar 8 ga watan Maris ɗin 2026.

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce, har yanzu babu wata hujja da ke nuna cewa sabon jagoran ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya, inda ya ce sun raunata shi a wani hari da suka kai a ranar 28 ga watan Fabreru a Tehran, inda aka kashe mahaifinsa da ɗan'uwansa

A jawabinsa na farko a matsayin jagoran ƙasar, da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar a ranar 12 ga watan Maris, Khamenei ya sha alwashin kulle mashigar Hormuz ga ƙasashen duniya, inda suka kawo tsaiko ga jigilar kaso 20 na man duniya, kuma ya ƙara da cewa ba za su yafe jinin mutanen da aka kashe ba a yaƙin.

A ranar 20 ga watan Maris, gidan talabijin na ƙasar ya karanto wani saƙo domin taya murnar sabuwar shekara ga al'ummar Fasha.

Ali Larijani - Sakataren majalisar ƙolin tsaron Iran (ya rasu)

An kashe Ali Larijani, mai shekaru 68, a wani harin da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran a yanki Pardis na birnin Tehran a ranar 17 ga wataan Maris, inda aka kashe shi tare da ɗansa da ɗaya daga cikin mataimakansa.

Shi ne jami'in gwamnatin Iran mafi matsayi da aka kashe bayan kisan Khamenei.

Da shi ne tsohon kwamandan rundunar juyin juya hali, inda ya samu ƙarfin iko a lokacin da ya shugabanci kafafen yaɗa labaran Iran na tsawon shekaru 10, kafin ya zama mai ba da shawara kan harkokin tsaro ga Khamenei a shekarar 2004.

Larijani ya kasance babban mai shiga tsakani kan makamin nukiliyar Iran da ƙasashen yamma, daga shekarar 2005 zuwa 2007, amma a cire shi daga muƙamin baya samun saɓanin ra'ayi da shugaban ƙasar na wancan lokacin Mahmoud Ahmadinejad.

Ya riƙe muƙamin kakakin majalisar Iran na tsawon shekaru 12, inda ya zama mutum na farko da ya fi kowa daɗewa a muƙamin.

Larijani ya kuma wakilci Khemenei a majalisar ƙoli ta harkokin tsaron ƙasar, kuma shi ke ba da umarni kan matakan muƙushe ƴan'adawa da dakarun ƙasar ke ɗauka kan masu bore, ciki har da abin da dakarun Basij suka yi kan masu zanga-zanga a Iran a Disambar 2025 da Junairun 2026.

Aƙalla masu zanga-zanga 6,508 aka kashe, tare da kama 53,000, kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam suka yi iƙirari.

Rear Adm Ali Shamkhani - Sakataren majalisar tsaron Iran (ya rasu)

An kashe Ali Shamkhani ne a hare-haren da aka kai ranar 28 ga watan Fabreru a Tehran.

Babban mashawarci ne ga Khemenei, kuma babban jami'i a shirin makamin nukiliyar Iran a tsara dokoki da tsaro, inda shi kaɗai ne mai muƙamin rear admiral a Iran.

Ya tsallake wani hari da aka kai a gidansa a watan Yunin 2025, a yaƙin da aka yi na kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila.

A lokacin yaƙin Iran da Iraƙi a shekarar 1980, Shamkhani na ɗaya cikin kwamandojin rundunar juyin juya hali da ake ji da su.

A cikin sama da shekaru 20 da suka gabata, ya riƙe manyan muƙamai, ciki har da ministan rundunar juyin juya halin musulunci ta IRGC, da kuma ministan tsaro, da kuma kwamandan sojin ruwa da kuma sakataren majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar, inda a shekarun baya-bayan nan ya taka muhimmiyar rawa wajen murƙushe masu zanga-zanga.

Manjo Janar Mohammad Pakpour – Babban kwamandan IRGC (ya rasu)

An kasar Manjo Janar Mohammad Pakpour ne a ranar 28 ga watan Fabreru bayan wasu hare-hare da aka kai Tehran, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Ya riƙe muƙamin kwamandan IRGC na tsawon shekaru 16, inda aka ƙara masa matsayi zuwa babban kwamandan rundunar bayan da aka kashe Hossein Salami, a lokacin yaƙin kwanaki 12 da Isra'ila.

Masoud Pezeshkian - Shugaban ƙasa (yana raye)

An zaɓi Masoud Pezeshkian ne a matsayin shugaban Iran a ranar 6 ga watan Yulin 2024, bayan da majalisar magabatan ƙasar mai mutum 12 suka amince da zaɓen.

Shugaban mai shekaru 71, tsohon likitan tiyata ne kuma mamba a majalisar Iran, inda yake da ƙudurin tabbatar da jami'an sanya ido ɗabi'un ƴanƙasar, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce, bayan alƙawarin da ya yi na haɗin kai da fito da Iran a idon duniya.

A ranar 11 ga watan Maris, Pezeshkian ya wallafa a shafinsa na X cewa, "Iran na son ɗorewar zaman lafiya a yankin".

Kwanaki biyar bayan hakan, ya nemi taimakon ƙasashen duniya game da hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran, inda ya ce: "Muna sa ran ƙasashen duniya za su yi Allah-wadai da hare-haren kuma su ja hankalisu da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

Mohammad Bagher Ghalibaf - Kakakin majalisar Iran (yana raye)

Kakakin majalisar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf, na da damar cire kakinsa na rundunar juyin juya hali ya koma sanya farin kaya amma ya ci gaba amfani da kaki domin nuna goyon bayansa ga shugabancin Iran.

Ƙwararren matuƙin jirgin sama ne, kuma ya yi takarar shugaban ƙasar sau huɗu.

Mutumin mai shekaru 64 yana taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ake yi.

Bayan hare-haren da aka kai kan cibiyoyin makamashin Iran, ya wallafa a shafinsa na X cewa: "an shiga sabon babin turjiya, za dauki fansa."

Yayin da yake maida martani game da rahotanni kan tattaunawa da Amurka, Ghalibaf ya ce: "Babu wata tattaunawa da muke da Amurka, ana amfani da labaran ƙanzon kurege domin a gyara kasuwar hannun jari da mai."

Birgediya Janar Gholamreza Soleimani - Kwamandan rundunar Basij (ya rasu)

An kashe kwamandan Basij Birgediya Janar Gholamreza Soleimani a harin da Amurka da Isra'ila suka kai a ranar 17 ga Maris 2026, kamar yadda kafar yada labaran Iran ta ruwaito.

Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan - Shugaban ƴansanda (yana raye)

Shugaban 'yan sanda Birgediya Janar Ahmad Reza Radan ne ke da alhakin aiwatar da tsauraran matakai da murkushe ƴan'adawa.

A shekarar 2023, ya sanar da shirin Noor, wanda ake amfani da kyamarori na sa ido da fasaha don ganowa da hukunta matan da suka karya dokar sanya hijabi, ciki har da kwace motoci da rufe kasuwanni.

A baya-bayan nan, Radan ya ɗauki tsattsauran ra'ayi kan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, kuma a farkon yaƙin, ya yi gargaɗim cewa dakarunsa za su dauki duk wanda ya hau kan tituna domin yin zanga-zanga a matsayin "maƙiyi" kuma "bisa umurnin maƙiya".

Gholamhossein Mohseni Ejei - Alƙalin alƙalan Iran (yana raye)

A watan Janairu, babban alkalin alkalan kasar Iran Gholamhossein Mohseni Ejei, ya yi gargadin cewa ba za a yi "wasu sassauci ba" kan waɗanda aka samu da laifin tada ƙayar baya a lokacin zanga-zangar ba.

Birgediya Janar Eskandar Momeni - Ministan cikin gida (yana raye)

Shi ne ministan cikin gida tun daga watan Agustan 2024. Birgediya Janar Eskandar Momeni yana da ƙarfi a IRGC da Rundunar 'yan sanda ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Birgediya Janar Esmail Qaani - Kwamandan dakarun Quds na IRGC (yana raye)

Kafofin yada labaran Iran sun fi kiran shi da "Janar na Levant". Birgediya Janar Esmail Qaani ya zama kwamandan Rundunar Quds ta IRGC a shekarar 2020.

A shekarar 2012, ma'aikatar baitulmalin Amurka ta sanya masa takunkumi saboda tallafin kudi da makamai da yake samarwa ga dakarun Quds a Gabas ta Tsakiya da Afirka, musamman Gambia.

Esmail Khatib - Ministan leƙen asiri (ya rasu)

An naɗa Esmail Khatib a matsayin ministan tsaro na Iran ta hannun marigayi tsohon shugaban kasar, Ibrahim Raisi, a shekarar 2021.

Ya karanci ilimin fiƙihu a hannun manyan malamai da suka hada da Ali Khamenei, ya kuma riƙe muƙamai daban-daban a ma'aikatar leƙen asiri da ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran.

"Kisan gillar" da aka yi wa Khatib, a wani harin da Isra'ila ta kai ta sama, ya jefa Iran cikin "alhini", in ji Pezeshkian.

Manjo Janar Abdolrahim Mousavi - Shugaban ma'aikatan rundunonin sojin Iran (ya rasu)

Shi ma yana daga cikin waɗanda aka kashe shi a harin da aka kai Tehran a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Babban hafsan sojin na Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya maye gurbin Manjo Janar Mohammad Bagheri, wanda aka kashe a yakin kwanaki 12, a ranar 12 ga watan Yuni.

Sadegh Larijani - Shugaban majalisar malamai (yana raye)

Ɗan'uwan Ali Larijani, Sadegh shi ne shugaban majalisar malamai, wadda take a tsakanin majalisar ƙasar kuma ita ke sanya ido kan harkokin majalisar magabatan ƙasar.

Abbas Araghchi - Ministan harkokin ƙasashen waje (yana raye)

An ruwaito cewa an tattauna tsakanin ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araghchi da tawagar wakilin Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff - amma an ce tattaunawar sharar fage ce kawai.

A ranar 15 ga watan Maris, 2026, ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araghchi ya shaida wa CBS News cewa Iran ba ta taɓa neman tsagaita buɗe wuta ba a yaƙin da take yi da Isra'ila da Amurka.

Ya ƙara da cewa "Wannan yaƙin zaɓi ne na Shugaba Trump da Amurka, kuma za mu ci gaba da kare kanmu."

Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh - Ministan tsaro (ya rasu)

An kashe ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh a harin da aka kai a ranar 28 ga watan Fabreru a Tehran.

Mece ce ribar kai hari kan shugabannin Iran?

Burin Amurka da Isra'ila shi ne su "rusa gwamnatin Iran", kamar yadda Janar Dan Caine, wanda ke jagorantar hafsoshin sojojin Amurka, ya bayyana kwanaki kadan da fara yakin.

A farkon yakin, sauyin mulki ita ce manufar da shugabannin Amurka da na Isra'ila suka sa gaba.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Truth Social, shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Iraniyawa da su "hamɓarar da gwamnatin", kamar dai yadda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi a baya-bayan nan a ranar 19 ga Maris, lokacin da ya yi kira ga al'ummar Iran da su "tashi tsaye a wannan lokaci".

Amma a al'adance da suke kallon hakan a matsayin shahada da ke da ƙima a addini - da siyasa - ana hasashen mutuwar waɗannan manyan shugabanni a matsayin ci gaba maimakon rugujewa.

Alal misali, a gidan talabijin na ƙasar, an ga wani mai gabatar da shirye-shirye yana zubar da hawaye ya sanar da mutuwar Ali Khamenei da cewa ya yi shahada mai kyau.

Kuma bayan makonni biyu da hakan, SNSC ta bayar da rahoton rasuwar Ali Larijani, inda ta ce: "Ya yi shahida".

A tsawon rayuwarsa na gwagwarmayar ci gaban Iran da juyin juya halin Musulunci, daga karshe ya burinsa na tsawon lokaci ya cika, ya amsa kiran Ubangiji da ɗaukaka ta shahidi."