Yadda Lakurawa suka yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna suka kashe 11

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan bindiga da aka kyautata zaton Lakurawa ne sun yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna, inda suka kashe guda 13 tare da jikkata da dama a jihar Kebbi.

Bayanai sun nuna cewa harin ya faru ne a daren ranar Talatar da ta gabata a garin Giro Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga, inda dakarun sojin Najeriya ke ƙoƙarin kai ɗauki bayan samun kira da suka yi daga al'ummar garin.

Hukumomi na cewa sojojin da aka kashe 11 ne sai kuma jami'in ɗansanda guda ɗaya sai kuma sauran waɗanda suka rasu da samun raunuka da suka haɗa da fararen hular da suka kasance tsakanin sojoji da Lakurawa yayin musayar wuta.

Kakakin ƴansandan jihar ta Kebbi ya shaida wa BBC cewa ba zai iya cewa uffan ba kan farmakin kasancewar abin da ya faru aiki ne na sojoji.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya kai ziyarar gani da ido zuwa wurin da al'amarin ya faru tare da zuwa asibiti domin duba wadanda suka samu raunuka.

Gwamnan ya bayyana al'amarin da aikin "rashin hankali da dabbanci."

Nasiru Idris ya ƙara da cewa abin takaici ne cewa bayanin da aka bai wa sojojin domin su kai ɗauki ba daidai ba ne.

A yanzu haka dai al'ummar yankin na dora alhakin harin kan dandazon ƴan ta'adda da ke aiki a sassan jihar ta Kebbi da jihar Sokoto mai maƙwabtaka, inda rahotannin ke nuna cewa a baya-bayan nan ƴan bindigar sun tsaurara hare-harensu kan al'umma da gonaki da hanyoyin sufuri.

Ma'aikatar tsaro ta Najeriya ba ta ce uffan ba kan batun sai dai kuma rahotanni na cewa sojojin Najeriya sun ruɓanya hare-hare a yankin na ƙaramar hukumar Shanga, inda sojoji ke bi lungu da saƙo na dazuka domin neman mayaƙan na Lakurawa.

Daga ina Lakurawa suka ɓullo?

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa 'yan ƙungiyar sun shiga yankunan na Sokoto ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.

Sukan yi wa'azi tare da aiwa jama'a cewa su ba su tare da 'yansanda da sojoji, da ma duk wani jami'in gwamnati na siyasa kuma ba su yarda da karatun boko ba.

Majiyar ta ƙara da cewa mutanen waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, sukan yi wa mutane jawabi cikin harsuna daban-daban.

Bayanai sun nuna cewa idan mutanen suka yi wa'azi ko faɗakarwa sukan fassara da Hausa, da Fulatanci, da Abzinanci, da Tubanci, da Barbarci, har ma da Ingilishi.

''Suna da yawa sosai, idan suka zo gari da mashin 10 ko 15, sai su ajiye mutanensu a nan su ƙara gaba zuwa wani garin,'' in ji majiyar.

Haka kuma bayanan sun nuna cewa ƙungiyar na kafa wa mazauna garuruwa dokoki, har ma suna bayar da jarin kuɗi na Sefa (CFA) ga matasa idan suka ga wanda ba shi da ƙarfin jari domin bunƙasa sana'o'insu.

Sannan kuma suna karɓar haraji da zakka. Idan ba a bayar ba sai su kwashe dabbobin mutum har sai ya biya kafin su ba shi dabbobinsa, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC.

Wani mazaunin yankin ya ce daga cikin ƙananan hukumomi biyar na wannan yanki na Sokoto, sun fi ƙarfi a biyu daga ciki wato ƙaramar hukumar Gudu - wadda ya ce in ban da hedikwatar ƙaramar hukumar babu inda mutanen ba su zuwa.

Wasu bayanai sun tabbatar wa BBC cewa ko a kwanakin baya 'yan kungiyar sun yi arangama da jami'an tsaron Najeriya, inda suka kashe hudu, kuma su ma 'yan ƙungiyar ya ce sun yi asarar mutanensu a lokacin.

Barazanar da Lakurawa ke yi ga Najeriya

Masana harkokin tsaro na ganin cewa ɓullar wannan ƙungiya ba ƙaramar barazana ba ce ga ƙasar idan aka yi lakari da cewa wuri ne da fitacciyar kungiya mai iƙirarin jihadi a duniya take – Ansaru - kamar yadda Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, mai bincike a kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya shaida wa BBC.

Ya ce wannan zai ƙara ta'azzara yanayin da ƙasar ke ciki na fama da matsalolin musamman yankin arewacin ƙasar ke ciki.

Lamarin ya bai wa irin waɗannan ƙungiyoyi dama ta samun gindin zama inda suke tara makamai da ƙara ƙarfi, harma suke iko a yankin, a cewar Kabiru Adamu.

"Kusan a ce babu wata hukuma ta gwamnati da ke kalubalantarsu da kyau, kasancewar yanki ne da ke da iyaka da ƙasar Mali, wadda an san irin yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke yaƙi da gwamnatocin ƙasashen." in ji shi.

Masanin ya ce, abin zai iya kai Najeriya ga yaƙi da ƙungiyar kamar yadda take fama da wasu ire-irensu, waɗanda ke iƙirarin jihadi.