'Hanyoyi huɗu na kawo ƙarshen yaƙin Iran'

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da yaƙin Iran ya doshi mako uku, wasu na ci gaba da kiraye-kierayen tsagaiatw wuta a yaƙin.

Tuni dai yaƙin ya shafi duniya musamman ta fannin makamashin man fetur da iskar gas.

Musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi.

Haka ma a ƙasashe maƙwabta hare-haren da Iran ke kai musu sun janyo asarar dukiyoyi a ƙasashen, musamman yadda take kai wa cibiyoyin makamashi da sansanonin sojin Amurka hare-hare a ƙasashen.

Yaƙin dai kamar yadda aka yi hasashe ya shafi kusan duka yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan ne dalilin da ya sa ake ta kiraye-kirayen kawo ƙarshen yankin.

Jaridar New York Times ta lissafo wasu hanyoyi huɗu da take ganin su ne za su kawo ƙarshen yaƙin da suka haɗa da:

Kawar da gwamnatin Iran

Hanya ta farko da sharhin jaridar ya bayayan ita ce samun canjin gwmanati a ƙasar Iran.

Tuni dai aka kashe jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei a yaƙin tare da wasu manyan kusoshin gwamnatin Iran.

Sai dai kwanaki bayan kashe jagoran addinin tuni aka naɗa ɗansa, Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar, wani abu da ke alamta cewa ba abin da zai sauya ta fuskar tsarin gwamnatin ƙasar.

Jaridar New York Times ta ce za a samu sauyin gwamnati ne kawai idan aka samu gagarumar zanga-zangar buƙatar hakan daga ƴan ƙasar - sannan kuma su samu goyon bayan sojojin ƙasar da ƴansanda.

Zanga-zangar za ta samu goyon bayan Amurka da isra'ila musamman don kifar da gwamnatin Iran.

A cewar New York Times "wannan hanya za ta kawo ƙarshen yaƙin, amma ba lallai ba, domin gwamnatin Iran na da ƙarfin juriya.''

Jaridar ta ce kifar da gwmanatin Iran shi ne babban muradin Isra'ila, kuma abin da take son aiwatarwa kenan, amma Amurka ta ƙasashen yankin Gulf ba za su amince da hakan ba.

Domin ɗaukar matakan soji da Iran za ta yi zai haifar da gagarumin rikici ta tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sauya alƙiblar gwamnatin Iran

Hanya ta biyu da za a iya kawo ƙarshen yaƙin Iran ita ce ta samun sauyi a alƙiblar gwamnatin ƙasar.

Hakan na nufion gwamnatin za ta ci gaba a yadda take, amma kuma manufofinta za su sauya ta yadda za ta biyayya ga muradun Amurka ta Isra'ila.

To sai dai wannan hanya, na da matuƙar wahala, domin abu ne mawuyaci gwmanatin Iran ta bi muradun Amurka da Isra'ila a wannan lokaci, musamman matsayin da sabon jagoran addinin ya ɗauka.

Zai kuma yi wahala a iya sanin ko sabon jagoran addinin zai yarda ya haƙura da manufar ƙasar kan mallakar makamin nukiliya da ci gaba da ƙera makamai masu linzami da daina bai wa ƙungiyoyin masu riƙe da makamai tallafi irin su Hezbollah.

Ayyana nasarar kowane ɓangare

Hanya ta uku da yaƙin zai kawo ƙarshe ita ce kowane ɓangare ya ayyana samun nasara.

A cewar New York Times shugaba Trump na Amurka, da Benjamin Netanyahu na Isra'ila ba su cimma manufofinsu a yaƙin ba.

Kodayake sun samu nasarar kisan jagoran addinin Iran, amma manufofin ƙasar ba su sauya ba.

"Da wuya a yi tunanin kawo ƙarshen yakin kafin Amurka da Isra'ila su kai hari kan sauran cibiyoyin nukiliyar Iran, kuma hakan na iya haifar da sauyi a harkokin shugabancin ƙasar," a cewar New York Times.

Kwace tsiribin Kharg na Iran

Hanya ta ƙarshe da za aiya kawo ƙarshen wannan yaƙi ita ce Amurka ta ƙwace tsibirin Kharg na Iran.

Ta tsibirin ne kashi 90 cikin 100 na man Iran ke bi domin fita kasuwannin duniya.

Don haka ƙwace shi zai tsohe kuɗin shihgar da gwamnatin Iran ke samu ta hanyar man fetur.

Wanda kuma hakan zai sa gwamnatin Iran ta durkushe ta yadda ba za ta iya gudanar da al'amuran gwamnati ba, ta kuma kasa ɗaukar ɗawainiyar sojojinta har da albashinsu, wani abu da zai sa sojojin su gajiya.

A ƙarshen mako ne dai Amurka ta sanar da kai hare-hare kan cibiyoyin sojin Iran da ke tsibirin, amma ta ce ta kauce wa kai hari kan cibiyoyin mai da ke tsibirin don bai wa Iran damar sauya tunanin matsayarta kan mashigar Hormuz.

A jawabin da ya gabatar bayan harin, Shugaba Trump ya ce idan har Iran ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz to Amuka za ta iya duba shawarar kai hari kan cibiyoyin man tsibirin.