Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Salon da ƴan Boko Haram suka yi amfani a harin bam a Maiduguri
Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da yadda wasu da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne suka kai hare-hare a wasu wurare masu muhimmanci a jihar Borno ranar Litinin.
Maharan dai sun tayar da bama-bamai a gab da asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da babbar kasuwar 'Monday Market' da kuma ofishin aikewa da saƙonni ko gidan waya duk a cikin birnin Maiduguri.
Hare-haren sun auku ne jim kaɗan bayan mayaƙan na Boko Haram sun kai wasu hare-haren a sansanonin sojin Najeriya da ke Ajari da Baga da kuma Damboa duk a jihar ta Borno.
Rundunar ƴansandan jihar ta Borno a wata sanarwa dai ta ce mutum 23 ne suka mutu sakamakon hare-haren.
"Sun jefo min bam a cikin kular abinci"
Wani mai gadin asibitin koyarwa da ke Maiduguri inda bam ɗin shi ma ya tashi ya shaida wa BBC yadda aka kai harin bam ɗin. Mutumin ya samu rauni a hannu da ƙafafunsa.
"NI ina zaune a bakin asibiti saboda ni mai gadi ne sai wasu mutane suka shigo a Keke Napep su uku a ciki kuma akwai wasu abubuwa a ciki da ni ban yarda da su ba. Sai na ce da su su koma baya. Sai suka koma.
Sai suka ƙara dawowa sai na hana su shiga. Da na hana su shiga sai suka sauko daga babur ɗin sai suka wurgo min kula (abin zuba abinci) ta bigi hannuna ta faɗi a ƙasa zai bam ya tashi. Na kwanta ƙasa sai na ji wata ƙara. Na tashi zan shiga cikin asibiti sai na ga wani wata kular shi ma sai ya tashi. Shi ne ya taɓa kafata.
Tashin bam ɗin a wajen asibitin kamar masu dabino da sauran su duk sun mutu". In ji mai gadin.
"Yadda ƴata ƴar shekara 12 ta rasu"
Ita ma wata baiwar Allah wadda ta samu raunuka sannan ƴarta ta rasu ta shaida yadda bam ɗin ya tashi da su.
"Mun zo daga gida muna wurin sikuriti sai bam ya tashi. Na faɗi, ita ma yarinyata ta faɗi ba rai. Kanta ya fashe...Daga nan sai aka ɗauke ni aka kawo ni nan wurin. Ina tambayar ina yarinyata? Sai su ce tana nan.
Ban ji komai ba bayan na fahimci ta mutu. Na riga na fawwala wa Allah...Allah ne ya ɗauke ta to me zan faɗa...marainiya ce. Mahaifinta ya rasu tana wata biyar...."
Ta kuma ce al'amarin da ya faru da ita tsautsayi ne.
"Ni ba ma na fita duk da ina da marayu."
Me ya sa hare-haren a watan Ramadan?
Wata majiyar tsaro da ba ta so a ambaci sunanta ta ce sun samu rahoton cewa mayaƙan sun ce za su zafafa kai hare-haren ne a goman ƙarshe saboda a daidai lokacin ne aka yi yaƙin Badar a zamanin Annabi Muhammad (SAW).
Majiyar ta ƙara da cewa wannan ne ya sa sojojin da sauran jami'an tsaro suka fara aikin kar-ta-kwana domin daƙile yunƙuri ko barazanar.
A cikin wannan watan na Ramadan dai sassan Najeriya sun fuskanci hare-hare masu zafi, daga na Boko Haram zuwa na ƴanbindiga da sauransu.
Malam Kabiru Adamu mai bincike a harkokin tsaro a yankin Sahel, kuma shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce akwai bayanai da ke nuna cewa asaliln uwar ƙungiyar ce ta buƙaci haka.
"Mun samu bayanan da ke cewa babbar ƙungiyar ce ta buƙaci su ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare."
Masanin tsaron ya ce asalin burin mayaƙan shi ne kafa daular Musulunci, "amma a fahimtarsu duk wanda ba ya bin aƙidarsu, ba Musulmi ba ne. Duk da yake akwai bambancin Boko Haram da Iswap. Amma haƙƙin gwamnati ne ƙoƙarin tabbatar da cewa mutane sun fahimci abin da ke faruwa kuma tabbatar sun yi tir."