Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru bayan ƙwace kofin Afcon daga hannun Senegal?
A duniyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ana ci gaba da tafka muhawara ne kan hukuncin da Caf ta ayyana na ƙwace nasarar Senegal a gasar Afcon ta 2025.
Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirika (Caf) ta ayyana Morocco a matsayin ƙasar da ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afcon ta 2025 bayan sauya sakamakon wasan ƙarshe na gasar, inda aka ƙwace nasarar da Senegal ta yi kan Morocco bayan sama da wata uku.
Senegal ta doke Morocco da ci 1-0 a wasan ƙarshen da suka buga a ranar 18 ga watan Janairu, a wani wasa mai cike da taƙaddama wanda ya kai ga ƴanwasan Senegal suka fice daga fili cikin fushi, a lokacin da aka bai wa mai masaukin baƙi Morocco bugun daga kai sai mai tsaron gida ana dab da tashi, yayin da ake kunnen doki a tsakanin ƙungiyoyin.
Ƴanwasan Senegal sun fusata da matakin, kuma suka fice daga cikin fili har na tsawon minti 17, amma daga baya suka yanke shawarar komawa kuma ɗanwasan Morocco Brahima Diaz ya buga finaritin da ya ɓarar, yayin da ɗanwasan Senegal Pape Gueye ya ci mata ƙwallon da ta kai ta ga lashe gasar, a cikin ƙarinn lokaci.
Sai dai a yanzu hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afirika ta soke wancan sakamakon kuma ta bayyana Morocco a matsayin wadda ta lashe gasar.
Sanarwar da Caf ta fitar ta ce an ayyana Senegal a matsayin "waɗanda suka fitar da kansu daga wasan ƙarshe na gasar" kuma da haka an bai wa Morocco nasara a wasan "da ƙwallo 3-0".
Matakin na Caf ya biyo bayan ƙorafin da hukumar ƙwallon ƙafa ta Morocco (FRMF) ta yi, wanda kuma mahukunta suka gamsu da shi.
Caf ta ƙara da cewa "saboda ɗabi'ar ƴanwasan Senegal" Senegal ta karya sashi na 82 na dokar cin kofin Afirika, lamarin da ya sa aka yi amfani da sashi na 84 wajen hukunta ta.
FRMF a wata sanarwa ta ce ta yanke shawarar shigar da ƙorafin ne ''ba da niyyar ƙalubalantar ƙoƙarin da tawagar Senegal ta yi ba, sai domin neman a yi amfani da tanadin da doka ta yi game da yadda ake gudanar da gasar''.
"Hukumar ƙwallon ƙafan Morocco na jaddada tsayuwar ta kan mutumta doka da oda, da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a gasar Afirika,'' in ji FRMF.
Mene ne mataki na gaba?
Tuni dai wasu suka fara tambayar yaushe za a karɓe kofin daga hannun tawagar Senegal a miƙa ga tawagar Morocco.
Ita dai Caf ta ce Senegal ta yi karan-tsaye ga sashe na 82, wanda hakan ya sa dole a ɗabbaƙa hukuncin da sashe 84 ya ayyana.
Sashe na 82 ya yi tanadin cewa idan wata ƙungiya ta ƙi buga wasa ko ta fice daga fili ana tsaka da wasa ba tare da sahalewar alƙalin wasa ba, ta hakan zai sa a ayyana cewa ta yi rashin nasara a wasan, kuma za a fitar da ita daga gasar baki ɗaya.
Shi kuma sashe ya yi magana ne a kan hukuncin tawagar da ta saɓa tanadin sashe na 82.
Sashen na 84 ya yi tanadin cewa duk ƙungiyar da ta karya sashe na 82, za ta fuskanci hukuncin kora daga gasar kuma za a ayyana cewa an doke ta da ci 3-0 a wasan.
Abin da Caf ta yi ke nan, inda ta ce Senegal ta karya dokar sashe na 82 wajen fita daga filin wasa, sannan ita kuma ta ce ta ɗabbaƙa hukuncin sashe na 84 saboda samun tawagar da karya dokar sashe na 82.
Sai dai ba fa nan gizo ke saƙar ba, domin ba hakanan kawai za a miƙa kofin ga Morocco ba.
To abin da ke nan dai yanzu shi ne, tuni Senegal ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli ta harkokin wasanni wato Court of Arbitration for Sport, kuma kotun ce za ta yi hukunci na ƙarshe game da makomar wannan kofi.
Me ya faru a wasan ƙarshe na gasar Afcon?
Wasa na ci gaba da gudana a kunnen doki 0-0, alƙalin wasa Jean Jacques Ndala ya bayar da bugun daga kai sai mai tsaron gida, ana dab da tashi wasa.
Alƙalin wasa mai kula da na'urar VAR ya shawarci Ndala da ya duba bidiyon na'urar naɗar bayanai kafin yanke hukunci kan ƙetar da ɗanwasan baya El Hadji Malik Diouf ya yi wa Diaz.
Kocin Pape Thiaw, wanda bai huce daga fushin da yake yi ba kan maakin alƙalin wasan na soke ƙwallon da Ismaila Sarr ya ci ya umarcin ƴanwasan shi su fice dga filin.
Ɗanwasan gaban Senegal Sadio Mane ya tsaya a filin inda ya riƙa ƙarfafa gwiwar ƴanwasan Sengal su tsaya domin kammala wasan.
Bayan minti 17 sai ƴanwasan Senegal suka koma kuma wasa ya ci gaba.
Ɗanwasan gaban Real Madrid, Diaz ne aka bai wa damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma ya ɓarar da ƙwallon bayan ya yi ƙoƙarin cin ƙwallon a cikin salo da ake kira 'Panenka' kuma nan take alƙalin wasa Ndala ya hura tashi.
Ɗanwasan tsakiyar Villarreal Gueye ya zura ƙwallo a minti na hudu na ƙarin lokaci, kuma ƙwallon ce ta bai wa Senegal nasarar lashe gasar a karo na biyu a tarihi, a cikin shreekaru biyar.
A wajejn taron manema labarai a ƙarshen wasan, kocin Morocco, Walid Regragui ya ce ɗabi'ar da ƴanwasan Senegal suka nuna abin kunya ne, wanda bai mutumta al'adar Afirika ba. said Senegal's actions were "shameful" and do not "honour Africa".
Shi kuwa shugaban Fifa Gianni Infantino ya yi Allah wadai da harin.strongly
Amma Thiaw, bai yi wa manema labarai jawabi ba, duk a cewa haka aka tsaron tun da farko.
Amma a wasu tarukan manema labarai na daban da ya yi daga baya, ya amsa cewa bai kamata ya dakatar da wasan ba