KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye dangane da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 25/03/2026.

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Yadda aka tono kabarin yara domin gwaji a Kenya

    Yanzu haka hukumomi a yammacin Kenya sun ce an tono gawarwaki talatin da biyu da suka haɗa da ƙananan yara daga wani kabari da ke gundumar Kericho.

    A baya dai an ruwaito cewa adadin gawarwakin kusan rabin hakan ne. Tono gawarwakin ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu, wanda ya sa ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike.

    Yanzu haka dai an kai dukkan gawarwakin asibiti domin a yi musu gwaje-gwaje don sanin ko su waye, da kuma musabbabin mutuwarsu.

    Binciken dai ya haifar da damuwa ga jama'ar ƙasar, da ya sa su tuna wani lamari makamancin wannan da ya faru a baya na Shakahola, ɗaya daga cikin ifta'ili mafi muni da ke da alaƙa da ƙungiyoyin asiri a Kenya, inda aka gano ɗaruruwan gawawwakin da aka binne a wani daji.

  2. MDD ta amince da ayyana safarar bayi a matsayin laifi ga ɗan'adam

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da matakin ayyana safarar bayi a matsayin laifi ga ɗan'adam.

    Ƙudurin, wanda Ghana ta gabatar ya samu goyon bayan ƙasashe Afirka da na yankin Caribbean, wanda a ƙarshe ya samu ƙuri'a 123, sai ƙuri'a uku suka ƙi amincewa, sannan wakilai 52 ba su kaɗa ƙuri'a ba.

    Amurka ta ƙi amincewa da ƙudurin, inda ta ce bai kamata a yi amfani da dokokin zamanin yanzu ba wajen hukunci a kan abin da ya faru a baya, sannan ta yi tambayar shin wane ne zai ci moriyar diyya idan za a biya.

    Tarayyar turai ba ta shiga ƙuri'ar ba, inda ta kafa hujja da shari'ar da ake yi a game da batun, amma ta nanata cewa ba ta sha'awar bauta. Mambobin majalisar dai na ci gaba da bayani kan ƙuri'ar da suka kaɗa.

  3. Kotu ta kama Google da Meta da sakaci kan "tasirantuwar mutane da kafofin sadarwa"

    Meta

    Asalin hoton, Reuters

    Kotu a Amurka ta yanke hukuncin cewa kamfanin Meta da Google na da laifin sakaci, a wata gagarumar shar'ia da ta shafi jarabtuwa da amfani da shafukan sada zumunta.

    Wata mata mai shekara 20 da haihuwa, mai suna Kaley, ce ta shigar da karar, inda ta alakanta matsalar tabin hankali da ta samu da yawaitar amfani da kafafen sada zumunta, tun tana ƙarama.

    Kotun ta bayar umurnin a biya diyyar dala miliyan uku ga matar.

    Ana dai ganin wannan shari'ar da aka yi a birnin Los Angeles, za ta yi tasiri ga sakamakon dubban shari'oi makamancin wannan, da aka shigar a kan kamfanonin fasaha, saboda gazawa wajen kare masu amfani da su daga jarabtuwa da amfani da dandalinsu.

  4. Me ya sa jam'iyyu suke mayar da takarar zaɓen 2027 kudancin Najeriya?

    Zabe

    Asalin hoton, Getty Images

    A daidai lokacin da guguwar siyasar zaɓen 2027 ke fara kaɗawa a Najeriya, tuni an fara tattaunawa ne kan ƴan takarar da za su wakilci manyan jam'iyyun ƙasar, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.

    A ranar 24 ga watan Maris ne Jam'iyyar Labour wato LP ta sanar da mayar da takararta zuwa kudancin ƙasar, wanda hakan ke nufin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027 daga yankin kudanci zai fito.

    Shugabar riƙon-ƙwarya ta jam'iyyar, Nenadi Usman ce ta bayyana haka bayan wani taron ganawa da ta yi da Hukumar INEC a Abuja.

  5. MDD ta gargaɗi Iran da Isra'ila kan kai hari a kusa a cibiyoyin nukiliya

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta kai wasu sabbin hare hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka da ke Kuwait da Jordan da Bahrain.

    Jirage marasa matuka sun afkawa wani tankin mai a filin jirgin saman Kuwait, lamarin da ya haifar da tashin gobara. A gefe guda kuma Isra'ila ta ce ta kai hari wasu wurare biyu da ake amfani da su wajen kera makamai masu linzami masu cin dogon zango a Tehran.

    Hukumar sa ido kan ayyukan Nukuliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA, ta ce Iran ta sanar da cewa wani makami mai linzami ya kai hari kan wata tashar makamashin nukiliya a birnin Bushehr da ke kudancin kasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren da Iran da Isra'ila ke kai wa a kusa da wuraren nukiliyar na da mummunan hatsari.

  6. Iran ta yi watsi da buƙatun Amurka, ta gindaya nata sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙin

    Iran da Amurka

    Asalin hoton, Getty Images/COLLAGE

    Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito cewa ƙasar ta yi watsi da buƙatu da sharuɗan da Amurka ta gindaya na kawo ƙarshen yaƙin.

    Tashar ta ruwaito hakan ne daga wata majiyar tsaro da ba ta bayyana ba, amma majiyar ta ƙara da cewa, "Iran za ta kawo ƙarshen yaƙin ne a lokacin da take so, ko kuma aka cika mata sharuɗan da ta gindaya."

    Hukumomi a Iran dai sun sha nanata cewa ba tsagaita wuta suke so ba, yaƙin baki ɗaya ne suke so a dakatar.

    Haka kuma kafar ta ruwaito cewa Iran ta gindaya nata sharuɗan guda biyar kamar haka:

    • Dakatar da hare-hare da kashe-kashe a ƙasarta
    • Fitar da tsari mai kyau da zai tabbatar ba a sake ƙaddamar da yaƙi a Iran ba
    • Tabbatar da tsarin biyan diyya
    • Kawo ƙarshen yaƙi a ƙasar da sauran ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita a yankin
    • Ƙasashen duniya su tabbatar da iko da Ć´ancin Iran wajen gudanar da mashigar Hormuz

    Kafar ta ƙara da cewa Amurka na ƙoƙarin ganin an shiga tattaunawar, amma Iran na nuna cewa buƙatun na Amurka sun yi "tsauri."

  7. An shafe kwanaki 26 babu intanet a Iran

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    An shiga rana ta 26 tun bayan da aka katse intanet a Iran, sama da sa'o'i 600 kenan, kamar yadda kamfanin Netblocks da ke lura da intanet a faɗin duniya ya bayyana hakan.

    Netblocks ya ce, matakin da gwamnatin ta ɗauka ya take haƙƙoƙin 'yan ƙasar da 'yancin faɗin albarkacin baki a lokacin yaƙin.

    Sai dai duk da haka, wasu Iraniyawa na iya samun intanet, inda BBC ta samu damar zantawa da wasu daga cikinsu.

    Wata mata daga Iran ta bayyana cewa, "burinta bai wuce ta kulle idonta ta buɗe ta ga komai ya koma daidai ba."

  8. Isra'ila ta ce da wuya Iran ta amince da daftarin sulhu da Trump ya gabatar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tattalin arziƙin Isra'ila ya shaida wa BBC cewa da wuya Iran ta amince da wani shirin zaman lafiya da ya ƙunshi abubuwa goma sha biyar da rahotanni suka ce Amurka ta gabatar.

    Nir Barkat ya bayyana ƙudurin a matsayin "mai ban sha'awa a rubuce" amma yana bukatar bayar da tabbaci in har ana son aiwatar da shi.

    Ministan ya ce gwamnatin Iran ba za ta taɓa sauya manufofinta ba, kuma manyan manufofin Isra'ila na yakin su ne barin Iran ba tare da "nukiliya, ko makami mai linzami ko kuma kungiyoyin da take goya wa baya" ba.

  9. Iran ta kai sabbin hare-hare kan Isra'ila

    Iran ta kai wasu sabbin hare hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka da ke Kuwait da Jordan da Bahrain.

    Jirage marasa matuƙa sun afkawa wani tankin mai a filin jirgin saman Kuwait, lamarin da ya haifar da tashin gobara.

    A gefe guda kuma Isra'ila ta ce ta kai hari wasu wurare biyu da ake amfani da su wajen kera makamai masu linzami masu cin dogon zango a Tehran.

    Hukumar sa ido kan ayyukan nukuliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA, ta ce Iran ta sanar da cewa wani makami mai linzami ya kai hari kan wata tashar makamashin nukiliya a birnin Bushehr da ke kudancin kasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren da Iran da Isra'ila ke kai wa a kusa da wuraren nukiliyar na da mummunan hatsari.

  10. Isra'ila ta ce ta ware sabbin wuraren da za ta kai wa hari a Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya ce shi da babban hafsan hafsoshin rundunar IDF, janar Eyal Zamir sun amince da sabbin wuraren da za a kai hare-hare a Iran da Lebanon.

    Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Isra'ila ta ce tana shirin mamaye yankunan kudancin Lebanon har zuwa kogin Litani, har zuwa lokacin da za a kawar da barazanar Ƙungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran.

    Kafofin yada labaran Labanon sun ruwaito hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a wurare daban-daban a jiya Laraba ciki har da birnin Tyre.

    Isra'ila ta ce kimanin rokoki goma Ƙungiyar Hezbullah ta harba a birnin Haifa da ke arewacin kasar.

    Ta ce an kakkabo wasu daga cikinsu, yayin da wasu kuma aka bari suka faɗa wasu filaye.

  11. Mun kai wa jirgin yaƙin Amurka Abraham Lincoln hari - Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin ruwan Iran ta bayyana a wata sanarwa cewa ta kai wa jirgin ruwan Amurka, mai ɗauke da ɗaruruwan jiragen yaƙi, USS Abraham Lincoln, hari ta amfani da makami mai linzami.

    Kafin kai harin, Shahram Irani, kwamandan rundunar sojin ruwa ta Iran, ya bayyana cewa ana sa ido kan “aiki da motsin” jirgin yaƙin Abraham Lincoln da rundunarsa, inda ya ce: “Da zarar jirgin ya shiga cikin tarkon makamanmu, rundunar sojin ruwanmu za ta kai masa hari.”

    Har zuwa yanzu, Amurka ba ta yi wani tsokaci kan wannan lamari ba..

  12. Australia ta hana Iraniyawa bizar yawon buɗe ido

    Gwamnatin Australia ta sanar a ranar Laraba cewa za ta hana wasu yan ƙasar Iran masu riƙe da bizar yawon buɗe ido shiga ƙasar na ɗan lokaci na tsawon watanni shida.

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce wannan mataki ya shafi masu zuwa yawon buɗe ido da kuma waɗanda ke da bizar kasuwanci na ɗan lokaci.

    Ministan harkokin cikin gida ya bayyana cewa rikicin yaƙi da ake fama da shi a Iran ya haifar da damuwa cewa wasu daga cikin masu bizar wucin gadi ba za su iya komawa ƙasarsu ba ko kuma ba za su iya barin Ostiraliya ba bayan bizar tasu ta ƙare.

    Sai dai an ware wasu daga cikin wannan doka, ciki har da ma'aurata ko abokin zama na ɗan ƙasar Ostiraliya ko mai zama na dindindin, da kuma iyayen yara ’yan ƙasa da shekara 18 da ke zaune a Ostiraliya.

  13. Iraƙi ta gayyaci manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iraq ta gayyaci manyan jami’an diflomasiyyar Iran da kuma Amurka bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da kuma ƙara fargabar cewa ƙasar na iya shiga rikicin yaƙin Gabas ta Tsakiya.

    Matakin na zuwa ne yayin da hare-hare kan ƙungiyoyin mayaƙa a cikin Iraƙi ke ƙaruwa, lamarin da ke tayar da hankali a tsakanin jami’an gwamnati da al’ummar ƙasar baki ɗaya.

    Rahotanni sun ce gwamnatin Iraƙi ta kuma bai wa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi damar mayar da martani kan hare-haren da aka kai musu.

    Wata ƙungiyar mayaƙa da ke da alaƙa da Iran ta zargi Amurka da kai wani hari da ya kashe wani kwamanda tare da raunata sama da mutum 12 daga cikin mambobinta.

    A yankin Kurdistan kuma, wani hari da ake dangantawa da Iran ya yi sanadin mutuwar mambobi shida na wata ƙungiyar mayaƙan Kurdawa.

    Haka zalika, ƙungiyoyin da ke da kusanci da Iran a cikin Iraƙi sun ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka tun bayan fara wannan rikici.

    Masu sa ido kan harkokin tsaro na ganin cewa irin wannan yanayi na iya ƙara jefa Iraƙi cikin wani sabon rikici, musamman idan ba a samu sassaucin rikicin da ke faruwa a yankin ba.

  14. Abubuwan da daftarin Trump kan tattaunawa da Iran ya ƙunsa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images/collage

    BBC ba ta ga daftarin ba da aka ce shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya aikewa Iran.

    Bugu da ƙari, babu tabbacin batun a hukumance dangane da abin da daftarin ya kunsa. To sai dai kuma cikakkun bayanai daga kafafen watsa labaran Amurka da Isra'ila na rawaito daftarin.

    Kafar watsa labarai ta Channels 12 ta Isra'ila ta rawaito cewa daftarin ya ƙunshi abubuwa kamar haka:

    • Za a lalata cibiyoyin nukiliya na Natanz da Isfahan da Fordow
    • Za a bai wa hukumar IAEA cikakkiyar damar saka ido kan ayyukan Iran
    • Iran za ta daina amfani da mayakan sa-kai a yankin sannan ta daina tallafa musu da ba su makamai.
    • Lalata duk abin da ya jiɓanci nukiliyar da Iran ta alkilta ya zuwa yanzu
    • Bayar da tabbacin cewa Iran ba za ta sake yunƙurin cimma makaman nukiliya ba.
    • Ba za a sake alkilta makamashin nukiliya a Iran ba sannan dukkan abin da aka alkilta za a miƙa wa hukumar IAEA.
    • Dole ne mashigar Hormuz ta kasance a buɗe sannan a samu Ć´ancin zirga-zirgar jiragen dakon mai.
    • Za a sanar da matsaya a nan gaba dangane da shirin Iran na ƙera makamai masu linzami amma za a rage yawansu da nisan da za su iya kaiwa sai dai wanda za ta yi na kare kai.
    • Amurka za ta tallafa wajen gina shirin nukiliya domin samar da wutar lantarki a Bushehr.
    • Amurka za ta cire dukkan takunkuman da ta ɗora wa Iran shekara da shekaru
    • Kawar dukkannin barazanar sake ƙaƙaba takunkumi.

    Akwai kuma rahotanni da ke cewa akwai yiwuwar za a cimma tsagaita na wata domin ci gaba da tattaunawa - sai dai kuma ba bu tabbacin hakan kasancewar babu cikakkun bayanai da Fadar White House ta bayar.

    Sai dai a wata sanarwa da cibiyar haɗin kan dakarun ƙasar Iran ta fitar ta musanta batun tattaunawa da Amurka.

    Cibiyar ta ce ba da su Trump yake tattaunawa ba sai dai idan da kansa yake tattaunawa.

    Mai magana da yawun rundunar da Khatam al-anbiya mai shiga tsakanin dakarun Iran, Ebrahim Zolfaghari a cikin sanarwar ta faifan bidiyo ya ce " har rikicin da ke tsakaninku ya kai kun fara tattaunawa da juna?"

  15. Ukraine ta kai harin jirgi maras matuƙa Tekun Baltic

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani hari da Ukraine ta kai ta amfani da jirgin mara matuƙi ya haddasa gobara a wata babbar tashar jiragen ruwa da ke Tekun Baltic a arewa maso yammacin Russia.

    Gwamnan yankin Leningrad ya ce ana ƙoƙarin shawo kan gobarar da ta tashi a tashar Ust-Luga,, yana mai ƙara da cewa ba a samu rahoton asarar rai ba.

    Tashar na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin fitar da kayayyakin Rasha zuwa ƙasashen waje, ciki har da taki, da man fetur da kwal.

    A ranar Litinin, Ukraine ta kai wani hari makamancin wannan wanda ya haddasa gobara a tashar Primorsk Port, wadda ita ma ke kusa da iyakar Finland a arewa maso yammacin Rasha.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya zargi Rasha da nuna “mugunta matuƙa” bayan da ta kai daya daga cikin munanen hare harenta a ranar Litinin. Rahotanni sun ce Rasha ta harba kusan jiragen yaƙi marasa matuƙi dubu guda cikin sa’o’i 24.

  16. Ƙawancen jam'iyyu masu sassauci ke kan gaba a zaɓen Denmark

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakamakon zaɓen ƙasar Denmark ya nuna cewa ƙawancen jam’iyyun masu sassaucin ra'ayi da firaminista Mette Frederiksen ke jagoranta ne ya samu mafi yawan kuri’u.

    Kawancen ya lashe kujeru 84 a majalisar dokoki, amma bai kai kujeru 90 da ake buƙata domin samun cikakken rinjaye ba.

    Jam’iyyar firaministar, wato Social Democrats, ta samu sakamako mafi muni tun daga shekara ta 1901, amma duk da haka ita za ta jagoranci kafa gwamnatin gamin gambiza.

    Ta ce a shirye nake na ci gaba da rike ragamar jagorancin Denmark har nan da shekaru hudu, sai dai akwai jan aiki, wajen kafa gwamnati a gabanmu.

    A ɗaya ɓangaren kuma, jam’iyyun masu ra'ayin mazan jiya sun samu kujeru 77 a majalisar.

  17. Farashin ɗanyen mai ya faɗi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya faɗi, daga bude kasuwarsa a Larabar nan, yayin da kasuwannin hannayen jari na nahiyar Asiya suka dan farfado, bayan da Iran ta sanar da MDD cewa za ta ba wa jiragen ruwa na kasuwanci damar wucewa ta mashigin Hormuz.

    Tehran ta ce za a bar jiragen ruwa ciki har da na dakon mai su wuce ta mashigin, muddin suka nemi sahalewar hukumomin Iran.

    Tun da farko an ji shugaba Trump na cewa ya samu wata muhimmiyar kyauta ta miliyoyin kudi daga wasu da ya ce yana magana da su a Iran kan cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin.

    Wakiliyar BC ta ce shugaba Trump ya ce Iran din ta amince cewa ba za ta samar da makamin Nukiliya ba, to amma dama can ta jima tana fadin shirin Nukilyata na farar hula ne ba wai makami ba.

    Sai dai mahukunta a Tehran sun musanta kalaman shugaban kasar da kakkausar murya, suna cewa yana fadin hakan ne kawai don was da hankalin masu zuba jari da kuma farfado da farashin mai a duniya.

  18. Abin da Iran ta shaida wa IAEA

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar sa ido kan ayyukan Nukuliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Iran ta sanar da ita cewa wani makami mai linzami ya bugi wata tashar wutar nukiliya a birnin Bushehr da ke kudancin kasar.

    Shugaban hukumar, Rafael Grossi, ya sake jaddada kira da a yi matuƙar taka-tsantsan domin kauce wa haɗarin da ya shafi makamashin nukiliya.

    An ji ƙarar fashe-fashe a gabashi da arewaci da kuma tsakiyar Tehran a daren Talata, yayin da Israel ta tabbatar da cewa ta kaddamar da sabbin hare-hare.

    Iran ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa Israel da Kuwait da Jordan da kuma Bahrain.

    Ɗaya daga cikin makaman ya bugi wani tankin mai a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Kuwait, lamarin da ya haddasa gobara. Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta ce an shawo kan gobarar, kuma ba a samu asarar rai ba.

  19. Faransa da Canada sun soki mamaye kudancin Lebanon da Isra'ila ta yi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Faransa da Canada, sun yi Allah-wadai da shirin Isra'ila na mamaye kudancin Lebanon har zuwa kogin Litani, suna cewa dole ne a mutunta ikon ƙasar da iyakokinta.

    Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya ce irin wannan mataki zai haifar da “manyan matsalolin jin ƙai ga al’umma”.

    Isra’ila ta ce sojojinta za su karɓi iko da yankin ne har sai an kawar da barazanar ƙungiyar Hezbollah.

    Tuni sama da mutum miliyan guda suka tsere daga muhallansu sakamakon rikicin. Kamfanin dillacin labaran kasar ta Lebanon, ya ruwaito cewa hare-haren Isra’ila da aka kai da sanyin safiyar Laraba sun kashe aƙalla mutum shida a birnin Sidon.

    A gefe guda kuma, wata mata ‘yar Isra’ila ta mutu a arewacin ƙasar a jiya Talata sakamakon harin makamin roka da ƙungiyar Hezbollah ta kai.

  20. Kai kaɗai kake kiɗanka kai rawarka - Dakarun Iran ga Trump

    ..

    Asalin hoton, Press TV

    Cibiyar haɗin kan dakarun ƙasar Iran ta ce ba da su Trump yake tattaunawa ba sai dai idan da kansa yake tattaunawa.

    Mai magana da yawun rundunar da Khatam al-anbiya mai shiga tsakanin dakarun Iran, a wata sanarwa da ba a ambaci sunan Trump ko Amurka ba, ya ce "mai ikrarin ita ce ƙasa mafi ƙarfi a duniya", inda ya ƙara da cewa "ka da ku ayyana galabar da aka samu a kanku da tattaunawa."

    Ebrahim Zolfaghari a cikin sanarwar ta faifan bidiyo ya ce " har rikicin da ke tsakaninku ya kai kun fara tattaunawa da juna?"

    "Ba za ku sake ganin tasirin muradanku a yankin ba haka ma farashin makamashi da mai har sai lokacin da kuka fahimci amfanin zaman lafiya a yankin tukunna da dakarunmu masu ƙarfi za su samar. Daidaito na samuwa ne ta hanyar ƙarfi," in ji Zolfaghari.

    Ya kuma ƙara da cewa "irinmu ba za su taɓa biyan buƙatun irinku ba. Ba yanzu ba. Ba kuma za ta taɓa saɓuwa ba".

Trending Now