Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ƙasashen yankin Gulf ba sa rama hare-haren Iran
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Iran na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a faɗin yankin Gulf, a wani ɓangare na yaƙin Amurka da Isra'ila.
A ranar Alhamis, ta kai hari cibiyar makamashin Ras da ke Qatar, bayan Isra'ila ta kai hari kan cibiyar makamashin Iran ta South Pars - wani ɓangare na babban rumbun gas na duniya.
Kawo yanzu Qatar da sauran ƙasashen yankin Gulf ba su nuna alamun ɗaukar matakin ramuwar gayya kan Iran ɗin ba.
Amma me ya sa suka kauce wa mayar da martanin, kuma me ya sa suka ɗauki wannan matakin.
Tsoron wahala da taƙaita ɓarna
A lokacin da Amurka da Israila suka ƙaddamar da hare-haren soji kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, Tehran ta gaggauta mayar da martani ba wai ga hare-hare kan Ira'ila kaɗai ba, har kan wasu ƙasashen yankin Gulf ƙawayen Amurka.
An kai hare-hare ƙasashen Bahrain da Kuwait da Saudiyya da Qatar da Oman da kuma musamman ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Baya ga sansanonin sojin Amurka da Iran ta kai wa hari a ƙasashen, jami'ai a ƙasashen sun ce Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula, ciki har filayen jiragen sama da gine-ginen otal da gidaje, da kuma musamman cibiyoyin makamashi.
Amma duk da haka har yanzu ƙasashen ba su nuna alamun mayar da martani kan Iran ba, domin shiga yaƙin kai-tsaye.
"Daga ɓangarensu ba sa kallon yaƙin a matsayin nasu, don haka mayar da martanin zai jefa su cikin waɗanda za a iya kai wa manyan hare-hare, saboda akwai abubuwa da dama da za su yi asara fiye da wanda za su samu idan suka shiga yaƙin,'' a cewar Sina Toossi, wani babban jami'i a cibiyar tsare-tsare ta duniya da ke Amurka.
Wannan shawarar ta ja da baya a yaƙin na zuwa ne bayan la'akari "da wahalar, da lissafin dabara da ƙoƙarin iyakance ɓarnar da za a yi wa ƙasashensu", in ji Toossi.
Ƙasashen yankin Gulf na da tattalin arziƙi da ya dogara kan makamashi, da fiton kayayyaki da fannin zuba jari, a cewar Toossi, ''kuma duka Iran ta nuna alamun wargaza su''.
Kowa ya sani Iran na amfani da Tekun Fasha da mashigar hormuz - waɗanda dukansu ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya, a matsayin babbar hanyar samun damarta, in ji Toossi.
To amma Bilal Saab, babban daraktan cibiyar bincike da bayar da shawara kuma tsohon jami'an ma'aikatar tsaron Pentagon ya ce a farkon mulkin Trump ya ce idan ƙasashen Gulf suka ci gaba da ƙyale Iran, ''kamar suna nuna mata cewa za ta iya yi musu mummunar illa ba tare da fuskantar wani mataki ba''.
"Manufar mayar da martanin shi ne, tilasta wa Iran dakatar da hare-harenta, tare da sanya Iran ta guji yin hakan a nan gaba,'' in ji shi.
'Tsoron abin da ya faru a 2003 a Iraƙi'
Ga mafi yawan shugabannin ƙasashen Gulf, har yanzu suna tuna yaƙin Iraƙi da Amurka ta jagoranta, wanda ya shafi wasu sassan yankin, a cewar Pinfold, wani masanin tsare-tsare.
A 2003 ne, Amurka ya mamaye Iraƙi, tare da kawar da gwamnatin Saddam Hussein.
Amma abin da ya biyo baya shi ne giɓin mulki wanda ya haifar da rikice-rikice da ɓangaranci da samuwar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da tsawon shekarun da aka kwashe na rashin zaman lafiya a Iraƙi da ma faɗin yankin.
"Tsoron abin da ya faru na 2003 na razana su," in ji Pinfold.
"Suna fargabar buɗe ƙofar rikice-rikice da tashin hankali a ƙasashensu, kuma zai bai wa kiran damar faɗaɗa tasirinta a yankin.''
Amma yayin da ake cikin rashin jin daɗi a yankin Gulf kan hare-haren Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar, suna yawan dogaro kan kariyar sojin Amurka.
Baya ga sansanonin sojin Amurka da dakarun Amurka da ke ƙasashen, ƙasashen yankin Gulf da dama na musayar bayanan sirri sannan sukan dogara da Amurka ga tsaron samaniyarsu.
Waɗannan nau'rori na tsaron samniya na kakkɓo mafi yawan makaman linzami da Iran ke harba musu.
Ƙoƙarin ƙasashen yankin
Pinfold ya ce Iran ba ta kai wa dukkan ƙasashen yankin Gulf hari da "ɗaiɗai ba," in ji Pinfold, yana mai nuna bambancin dangantakar da ke tsakaninta da ƙasashen.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi kai wa hari a lokacin yaƙin.
A cikin 2020, ita da Bahrain duk sun daidaita dangantakarsu da Isra'ila.
Amma ba ta kai hari Oman ba, wadda ke da daɗaɗɗiyar rawar da take takawa a matsayin mai shiga tsakanin Iran da ƙasashen Yamma.
Pinfold ya ce "Oman ita ce ƙasa ɗaya tilo a yankin Gulf da ta taya sabon jagoran addinin Iran [Mojtaba Khamenei] murna."
Sai dai "matakin bai yi wa sauran manyan ƙasashen yankin Gulf daɗi ba."
Mohammed Baharoon, babban daraktan cibiyar bincike kan manufofin jama'a ta Dubai, ya ce "Iran na tura yankin Gulf zuwa wani ƙawancen da ke yaƙarta".
Ya ƙara da cewa, "Ta hanyar kai waƙkasashen yankin Gulf hari, Iran tana mayar da su abokan gaba da kuma shiga cikin kasadar yaƙin da ba wanda yake so."
Bayan taron da ministocin harkokin wajen ƙasashen yankin Gulf suka gudanar a ƙasar Saudiyya a ranar Laraba, ƙasashen Larabawa sun jaddada 'yancinsu na kare kai kamar yadda sashe na 51 na dokokin MDD ta tanada.
Me zai sa su mayar da martani?
Yayin da a halin yanzu ƙasashen yankin Gulf ke ja da baya daga ɗaukar fansa, " lissafin siyasa na iya canzawa cikin sauri", in ji Dokta H A Hellyer, babban jami'in ƙungiyar ta RUSI ta da ke nazarin siyasar ƙasashe a Birtaniya.
Ya ce musamman idan hare-haren da ke kawo cikas ga fitar da makamashi ke ci gaba ko ta'azzara.
Wani abu da zai iya canza tunani shi ne babban hari kan wuraren makamashi, in ji shi.
A ranar Alhamis, bayan da Iran ta kai hari a cibiyar makamashin Ras Laffan na Qatar, Iran ta sha alwashin kawo ƙarshen "ƙawancen ƙasashen Gulf" na Amurka idan aka ci gaba da kai hare-hare a kan cibiyoyinta.
Wani sauyi a ɗabi'un yankin Gulf na iya faruwa idan wakilan yankin na Iran suka kai musu hari kai tsaye.
"Idan Houthis suka kai musu hari… hakan zai buɗe wani sabon babi," in ji Pinfold.
Ya ƙara da cewa, idan aka yi hakan, ƙasashen yankin Gulf na iya ɗaukar rikicin a matsayin ba na Amurka da Isra'ila kawai ba, har da su ma kansu.
Kodayake a halin yanzu ƙasashen yankin Gulf ba su mayar da martani ba, Pinfold ya ce dabarun Iran na da matuƙar hatsari.
Ya ce Iraniyawa suna ƙona duk wata gada da suka yi da ƙasashen yankin Gulf, wanda hakan ke nuna yadda Iraniyawa ke ɗaukar wannan yaƙin.
Hellyer ya ce ƙasashen yankin Gulf ba za su amince da kai wa Iran hari ba har abada, musamman idan ana batun hare-haren cibiyoyin fararen hula.