Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsare-tsaren da muka gabatar wa jam'iyyun siyasa - INEC
Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) ta gabatarwa jam'iyyun siyasar ƙasar sabbin tanade-tanaden da ta yi domin shirya babban zaɓen 2027 da ke tafe.
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin bai wa jam'iyyun siyasar damar bayar da gudunmuwa ta fannin shawarwari da jan hankali kan yadda za a gudanar da zaɓe mai inganci a 2027.
Shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan, wanda ya jagoranci wani taron tattaunawa da shugabannin jam'iyyun Najeriya a Abuja babban birnin ƙasar ya ce sabbin tanade-tanaden sun tafi daidai da dokar zaɓe ta 2026, kuma za su taimaka wajen aiwatar da gyara a kura-kuran baya da aka gano.
A wata hira da BBC, Zainab Aminu, jami'a a hukumar ta Inec ta ce shugaban hukumar ya miƙawa jam'iyyun kundin tanade-tanaden domin su yi nazari a kai kuma su tabbatar da sun tafi daidai ta dokar zaɓe da aka sanyawa hannu ta 2026.
- Gudanar da zaɓukansu na cikin gida (na jam'iyyu)
- Yin rijista da kuma soke rijistar jam'iyyun siyasa.
- Haɗakar jam'iyyu domin zama jam'iyya ɗaya gabanin zaɓe.
Dangane da martanin jam'iyyun siyasar bayan Inec ta gabatar masu da tanade-tanaden, sai Zainab Aminu ta ce "Sun yi na'am da tanade-tanaden da aka gabatar masu domin kuwa dukka abubuwa ne da suka samo asali daga dokokin zaɓe da dokokin ƙasa da kuma ita hukuma yadda ta zauna ta tsara yadda za ta riƙa gudanar da ayyukan ta
"inda kuma suka ga suna da ƙorafi, baya rasa nasaba ga ita kanta dokar zaɓen ta 2026, kuma dama akwai wurin da za su je domin kai wannan ƙorafi domini ta hukumar zaɓe bai ta ce take yin dokokin ba kamar yadda muka sani, majalisar ce ta wakilai da dattawa ke da alhakin yin gyare-gyare a dokoki na zaɓe," in ji Zainab Aminu.
Ta yi bayanin cewa dokar zabe da kuma tanade-tanaden da hukumar zaɓen ta tsara da kuma gabatarwa jam'iyyu abubuwa ne masu muhimmanci sosai, musamman a fannin aikin da ke gaban jam'iyyun a yanzu kafin shiga zaɓe, watau zaɓukan fitar da gwamni.
Inec ta kuma yi wa jam'iyyun bayanin irin tanadin da ta yi domin shirin zaɓen 2027, ciki harda na aikin sabinta rijistar masu zaɓe a faɗin Najeriya.
Aikin rijistar dai ya yi nisa, kuma dama can hukumar ta tsara cewa za a fara shi ne daga ranar 18 ga watan Ogustan 2025 ga masu rijista ta intanet, sai kuma aka fara zango na biyu, na kammala rijitar ido da ido wanda aka fara daga ranar 25 ga watan Ogustan 2025 domin bai wa dukkan ƴan Najeriya da suka kai shekara 18 damar yin rijistar da shiryawa zaɓe mai zuwa.
Haka nan kuma Inec ta ce za ta sanar da lokacin baje kolin rijistar masu zaɓen domin jama'ar ƙasa su yi nazari da zaƙulo wajen da kura-kure suke don aiwatar da gyara kafin lokacin zaɓen.
Yanzu haka dai harkokin siyasa sun fara kankama a Najeriya, inda ake ganin yadda ƴaƴan jam'iyyar APC mai mulki ke cigaba da fitowa suna bayana goyon bayan su ga tazarcen shugaba Bola Tinubu, yayin da a ɓangaren ƴan adawa ake shaida faɗi-tashi tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da kuma tsohon gwamnan Anambra Peter Obi waɗanda ke fatan yin takara a jam'iyyarsu ta ADC, domin fafatawa da shugaba Tinubu.