Wuraren da makamai masu linzamin Iran za su iya kaiwa

    • Marubuci, Nick Ericsson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Harba makamai masu linzami da Iran ta yi zuwa sansanin sojin haɗin gwiwa na Amurka da Birtaniya da ke tsibirin Indian Ocean na nuna yadda yaƙin na Gabas ta Tsakiya yake ta'azzara.

Duk da cewa hare-haren ba su riski asalin inda aka hara ba, rundunar tsaron Isra'ila IDF ta ce wannan ne karon farko tun farkon ɓarkewar yaƙin da aka yi amfani da makamai masu cin dogon zango mafi nisa, duk da cewa har yanzu Iran ba ta tabbatar da harba makaman ba.

Masana yanzu sun fara nazarin abin da harin ke nufi ne, ciki har da fargabar ko nan gaba za a iya kai hare-hare a manyan biranen Turai irin su Berlin da Paris da London?

Wani minista a Birtaniya ya bayyana cewa ''babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ke tabbatar da iƙirarin IDF cewa Iran na da makami mai linzami mai cin dogon zango da zai iya kai wa London''

"Makaman Iran masu linzami dama can an daÉ—e ana tattaunawa a kansu," in ji Ghoncheh Habibiazad a tattaunawarsa da BBC.

"Duk da cewa Iran na nanata cewa tana ƙirƙirar makamai masu linzami ne domin kare kai, wasu na gani kai wa matakin makamai masu linzami masu cin dogon zango barazana ce ga tsaron yankin."

Kimanin wata ɗaya baya ne aka shiga tattaunawa a game da nukiliyar Iran, inda ana tsaka da tunanin sake shirya wata tattaunawar ne kuma sai yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke.

Tsibirin Chagos - wanda a ciki ne akwai sansanin sojin haÉ—in gwiwa na Diego Garcia - yana da kimanin nisan kilomita 3,800 ne daga Iran.

Mujallar Wall Street Journal da CNN sun ruwaito an harba makamai masu linzami daga wata majiyar tsaro daga Amurka, amma suka ce makaman ba su samu nasarar isa sansanin ba.

Ɗaya daga cikin makaman bai kai inda aka harba shi ba, sannan jirgin yaƙin Amurka ya kakkaɓo ɗaya, kamar yadda BBC ta kalato.

Jim kaɗan bayan aukuwar lamarin ne IDF ta ce birane da dama a turai da Asia da Afirka na fuskantar barazana, kamar yadda ta bayyana a bara cewa Tehran na shirin ƙera makamai masu linzami masu cin dogon zango.

Shugaban ma'aikatan rundunar tsaron Isra'ila, Latanal Janar Eyal Zamir ya wallafa wani bidiyo a kafofin sada zumunta bayan harba makamin zuwa tsibirin na Chagos tare da gargaÉ—in cewa, "Iran ta harba makamai masu linzami guda biyu masu cin zangon kilomita 4,000. Ba Isra'ila ta harba wa makaman ba," in ji shi.

"Makaman za su iya isa manyan biranen turai da Berlin da Paris da Rome."

Wasu masana, ciki har da masanin tsaro kuma tsohon shugaban tsaron haÉ—in gwiwa na Birtaniya, Janar Sir Richard Barrons ya bayyana wa BBC cewa wannan ya sa an fara sabon nazari kan makaman Iran masu linzami.

"A baya mun yi tsammanin makaman Iran masu linzami ba sa wuce kilomita 2,000, amma kuma Digo ya kai nisan kilomita 3,800."

Iran ta sha nanatawa a baya cewa makamanta masu linzami ba sa wuce mil 1,240, wato kilomita 2,000. Wannan ke nufin makaman Iran za su iya shiga Isra'ila, amma ba za su kai turai ba.

Marigayi Ayatollahi Ali Khamenei ya bayyana a 2021 cewa zaɓinsu ne kawai, ba wai don ba za su iya ƙirƙirar masu cin dogon zango sama da hakan ba.

Ya nuna cewa yana so ya zama barazana ne ga Isra'ila, ba ga turai ba, nahiyar ba ta tsole wa Tehran ido ba.

Amma a watan Satumban bara, wani ɗan majalisar Iran ya bayyana wa tashar talabijin na ƙasar cewa rundunar juyin-juya-halin ƙasar IRGC ta yi gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango, duk da cewa bai yi cikakken bayani ba.

Zangon makaman Iran

Bayan haka, hukumomin Amurka sun yi zargin cewa shirin Iran na sararin samaniya na alamta ƙasar na ƙera makamai masu linzami masu cin dogon zango, kamar yadda kafar Times of Israela ta nuna, kuma za ta iya amfani da shi idan buƙatar hakan ta taso.

Wasu masani sun aminta da haka. Dr Karin von Hippel, tsohon darakta-janar na cibiyar Royal United Services Institute da ke London ya bayyana wa BBC cewa, "idan makaman sun kai Diego Garcia... Iraniyawa za su iya haÉ—a makamai da za su iya cin dogon zangon kilomita 10,000, duk da cewa ba mu ga hakan a zahiri ba har zuwa yanzu."

Wannan ke nufin makaman da aka harba daga Iran za su iya kai wa nahiyar Amurka.

Sai dai wasu na cewa ko da a ce ba a kakkaɓo makaman ba, ba za su iya kai wa ga inda ake so ba.

Steeve Reed, ministan gidaje na Birtaniya ya bayyana wa BBC, "babu wani tabbacin cewa Iran na harin Birtaniya, ko kuma a ce za su iya samun nasara kai hari zuwa birnin ko da sun yi niyya."

Yanzu maganar da ake yi ita ce shin Iran na da shirye-shirye ko ƙarfin kimiyya da fasahar da ake buƙata domin ƙerawa da amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango.

Wasu kuma na cewa dama asali Iran ba ta yi niyyar hare-haren su yi nasara ba, kawai ta ƙaddamar da harin ne domin nuna ƙwanji da bayyana abin da za ta iya.

"Ba wai tana tunanin za ta kai harin ba ne a gobe zuwa London ko Paris, ina tunanin kawai ta tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro," in ji Danny Citrinowicz, tsohon sojan leƙen asiri na Isra'ila, wanda yanzu yake aiki da cibiyar nazarin tsaro ta Institute for National Security Studies da ke Tel-Aviv a zantawarsa da jaridar The Independent a London.

"Dama ita Isra'ila ai za ta bayyana cewa Iran na da burin faɗaɗa yaƙin ne da shigar da wasu ƙasashe cikin yaƙin," in ji Janar Sir Richard Shirreff, tsohon mataimakin kwamandan NATO a turai a zantawarsa da BBC.

"Dole mu kawar da kanmu. Wannan yaƙin Trump ne, kuma babu wani tsayayyen tsarin muradun da ake so a samu da zai kawo ƙarshen yaƙin. An faɗa mana cewa an tarwatsa cibiyar makamin nukiliyar ƙasar wata shida da suka wuce, yanzu ba za mu aminta da abin da Amurka ta faɗa ba."