Yadda zargin sakaci ke janyo salwantar rayuka a asibitin Jami'ar Maiduguri

Asalin hoton, ABDURRAHMAN AHMED BUNDI
Zargin sakaci da aiki, da rashin kyakkyawar kulawar da ta dace ga majinyata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno, ya tayar da kura a Najeriya, sakamakon yadda ake samun rahotannin asarar rayukan majinyata.
Yanzu haka dai wasu daga cikin wadanda irin wannan ta rutsa da 'yan uwansu sun tada kayar baya a shafukan sada zumunta na Internet, inda suke ta bayar da labarin abun da ya faru da su.
BBC ta samu zantawa da wasu daga cikin masu irin wannan korafi don jin ainihin abun da ke faruwa, kuma yawancinsu sun ce an jima ana fama da wannan matsala a asibitin, kuma mutane da dama sun sha wahala sosai, wasu ma sun rasa rayukansu.
Maina Isa Umar, wani mutumin birnin na Maidiguri, da ya rasa mahaifiyarsa a asibitin, ya ce shi ganau ne ba jiyau ba.
Ya shaida wa BBC Hausa cewa 'Idan ka shiga wajen lamarin har ya wuce dukkan yadda ake fada, da muka zo yin gwajin MRI kafin a ba mu lokaci zuwa, da kuma fitowar sakamako an zarce sati guda, muna ta shan wahala, ga shi mahaifiyata tana cikin wannan yanayi na rashin lafiya da kuma ukuba, haka karfinta ya kare karkaf bamu samu mun san menene ya ke damunta ba''

Asalin hoton, UNIMAID
Ya kara da cewa ''Akwai lokacin da tana kwance tana barci da safe, karfe shida lokacin da ake zuwa a auna yanayin jikin mutum, wata jami'a ta zo, ba ta tayar da ita, ko yi mata magana ba, haka nan kawai ta sanya mata abun da ake sanya wa a hannu, nan da nan ta fara fizge-fizge, zuciyarta ta tsinke, numfashinta ya dauke, an kai awanni biyu ko uku kafin a iya daidaita numfashinta, tun daga suman da ta yi a wannan rana da aka shigar da ita na'urar ba da agajin gaggawa ba ta sake dawowa hayyacinta ba har lokacin da Allah ya mata rasuwa''.
BBC Hausa ta tambaye shi, ko ba ya ganin watakila wasu za su ce wannan zargi ne yake yi? sai Maina ya ce ''Zargin me? ni fa uwata ce ta yi rashin lafiya, kuma a gabana komi ya faru, kuma bayan ni akwai mutane da yawa da mun san juna da irin wannan suma ta faru da su, mutane da yawa suna da irin wannan korafi wallahi tallahi, kuma sun rasa 'yan uwansu.''
''Ga ka da marar lafiya za a ce za a zo a masa allura ko a sa masa ruwa, sai ka ke ka yi musu magana sau goma lokaci ya yi, amma su ki sauraronka'' inji Maina.
Ni ma na rasa mahaifina - Barista Dantani

Asalin hoton, HAMZA NUHU DANTANI
Barista Hamza Nuhu Dantani, wani lauya mai zaman kansa, kuma dan asalim Maiduguri, ya ce shi ma irin wannan matsala ta faru da shi.
Lauyan wanda ya yi shuhura a Internet, ya ce shi ma ya rasa mahaifinsa a wannan asbiti na koyarwa na jami'ar Maiduguri, har ta kai ga rasuwar mahaifinsa.
Ya kara da cewa ''A gabana ma wadannan abubuwa sun faru, kuma idan ka duba wasikar da na aika wa asibitin da na wallafa a shafina na sada zumunta yawanci wadanda suka yi martani sun ce sun fuskanci irin wannan matsala a wannan asibiti.
Ya ci gaba da cewa har yanzu bai samu wani martani daga mahukuntan asibitin dangane da wasikar da ya aika masu ba.
Yayin da muka tuntubi jami'ar watsa labarai ta asibitin koyarwar na jami'ar ta Maidugurin kan wadannan batutuwa, ta ce an rubuta wa hukumar asibitin wasikar koke game da hakan, saboda haka ba za ta iya yin magana a hukumance ba, har sai an kammala bin kadin lamarin.










