Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amfanin shan ruwan zafi da safe ga lafiyar jikin ɗan'adam
- Marubuci, Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
"Kawai sai na fara ganin hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta na mutanen da ke shan ruwan ɗumi... kawai sai na fara tunanin cewa me ya sa ba zan gwada ba," in ji Maryam Khan ƴar shekara 21.
Ba abu ne mai wahalar kwaikwayo ba kuma ba mai tsada ba - abin da Maryam Khan da wasu mutane da dama ke son yi ba shi da wahala - shan ruwan zafi da safe.
An bayyana alfanun shan ruwan zafi ko na ɗumi a tsawon dubban shekaru kamar a tsarin maganin gargajiya na China wato Ayurveda, wanda ya samo asali daga Indiya.
Sa dai al'adar shan ruwan zafi da ta daɗe ta sake farfaɗowa a yanzu kuma ta na yawo a shafukan sada zumunta tun farkon shekarar nan.
An yi ta yaɗa bidiyoyi a dandalin TikTok da Instagram waɗanda miliyoyin mutane suka kalla, an kuma saka musu rubuce-rubuce kamar "newly Chinese" da kuma "China maxxing".
Wannan yawanci ya ƙunshi matasa da ke shan ruwan ɗumi, cin karyawa mai ɗumi da kuma motsa jiki bayan tashi daga barci.
Sai dai, shin wannan salo na rayuwa zai inganta lafiyar mutum?
Maganin inganta jiki
Wani abu da miliyoyin masu amfani da maganin gargajiya a China suka yi imani da shi, shi ne kuzari, da kuma zagayawar abubuwa a jiki da kamuwa da rashin lafiya idan abubuwan suka daina zagayawa.
Masu amfani da maganin sun yi imanin cewa shan ruwan ɗumi - wanda zafinsa ya ɗan ragu zuwa maki 40-60 don kauce wa ƙona baki ko maƙogoro - na ƙara inganta jiki da kuma rayuwa mai tsawo.
"Ka yi tunaninsa kamar gida," a cewar wani mai bincike kan maganin gargajiyar China, farfesa Shun Au.
Ya bayyana cewa a tsarin lafiya, cin abinci mai sanyi tamkar fari ne ya tunkari gidanka.
Masu maganin gargajiyar a China sun kuma bayar da shawarar cewa a riƙa saka takalmin silifa a gida da kuma karyawa da abu mai zafi.
Waɗannan ɗabi'u ne da suka kai Maryam Khan wajen amfani da magungunan gargajiya na China, wadda ke zaune a Landan, bayan da ta fara ganin bidiyon a TikTok.
Ta ce ta ji alfanun maganin sosai - wanda ya haɗa da jin lafiyar jiki, numfashi mai kyau, da sauransu - da sauya gahawar da take sha zuwa ruwan ɗumi.
"Na fara shan ruwan zafi da lemu, wani lokaci kuma da minti... kuma na ji daɗin jikina," in ji ta.
Me ya sa mutane suka koma amfani da maganin gargajiya?
Komawa amfani da maganin gargajiyar China da matasan ke yi ya nuna sauyi a ɗabi'un rayuwa, a cewar Dakta Shyama Kuruvilla, darektar cibiyar maganin gargajiya na duniya.
"Ko a Turai, akwai bincike da dama a yi... ɗaya a Jamus ya nuna cewa kashi 70 na al'umma na amfani da wani na'ui na maganin gargajiya. A wasu ƙasashe kuma - China da Indiya - alkaluman za su kai kashi 90," in ji ta.
Wasu mutane ba sa samun damar amfani da magungunan zamani, inda suke komawa amfani da maganin gargajiya a matsayin wani zaɓi na daban.
Wasu kuma na amfani da maganin gargajiya ne saboda sauƙinsa. Ɗabi'u kamar shan ruwa mai ɗumi za su kasance wata hanya ta inganta lafiya, zuciya da kuma muhalli.
Ɗabi'ar ta na da alaka da daɗaɗɗen tarihi na al'ada wanda ke da muhimmanci ga mutane.
"Masu sayar da magunguna gargajiyar da dama waɗanda suka fito daga al'ummomi, na cewa, 'mun yi amfani da wannan magani na tsawon dubban shekaru... kuma mun ga ya taimaki mutane da dama," in ji Kuruvilla.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce akwai buƙatar mutane su nemi shawarar likitoci kafin amfani da maganin gargajiya domin tabbatar da cewa magungunan ba su da haɗari.
Amma yaya ga batun shan ruwa mai zafi? Duk da cewa WHO ba ta bayar da wasu sharuɗa ba, Dakta Kuruvilla ta ce ya danganta da yadda zafin ruwan yake, wane adadi mutum ya sha, sannan yaya yanayin lafiyarsa.
Me kimiyya ya ce?
Shan ruwa mai ɗumi na da wasu alfanu, a cewar Dakta Rosy Brooks, wani kwararre kan magunguna.
"Akwai alfanun narƙar da abinci da kuma bahaya cikin sauki," in ji ta.
Kuma akwai hujjoji kaɗan da suka nuna cewa ruwa mai ɗumi na taimakawa wajen juyawar jijiyoyi da kuma sarrafa maƙogoro har zuwa cikin mutum," a cewar ƙwararriyar.
"Amma ba ya ga haka, alfanun shan ruwan sanyi ko zafi shi ne kashe ƙishirwa," kamar yadda ta bayyana.
"Babu hujjar da ta nuna cewa ruwan sanyi na yi wa jiki illa," in ji Dakta Selina Gray da ke Birtaniya.
Ta ƙara da cewa duk da wasu magunguna mara gaskiya da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta, babu hujjar da ta nuna cewa shan ruwan zafi na ƙona kitse ko narƙar da abinci.
"Idan mutum ya fi son shan ruwan ɗumi, hakan abu mai kyau ne, sai dai a hanya ce ta narƙar da abinci cikin sauri ba," in ji ta.
Grey, wadda ta girma a Singapore kan tsarin maganin gargajiyar China, ta ce "har yanzu mahaifiyata na faɗamin cewa in sha ruwan zafi domin ɗuma cikina".