Yadda Boko Haram ta yi wa mutane 20 yankan rago a Borno

Asalin hoton, Others
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International a Najeriya ta ce an yi wa mutane 20 yankan rago tare da sace wasu akalla 30 a yankin Mafa na jihar Borno.
Ƙungiyar ta ce waɗanda aka kashen a ranar Talata 31 ga watan Maris din 2026 ƴan gudun hijira ne maza da mata da ke zaune a cikin daji, kuma an kashe su ne a yayin da suka fita domin neman itacen girki.
Akwai kuma wasu aƙalla 30 da aka yi garkuwa da su, in ji Amnesty International.
Ta ce daga cikin mutanen da aka kashen akwai waɗanda aka yi wa yankan rago da kuma wasu da aka kashe da harbin bindiga.
Mutanen sun fuskanci barazanar Boko Haram a lokuta da dma, lamarin da ya sa suka yi gudun hijira.
Isa Sanusi shi ne shugaban kungiyar amnesty a Najeriya kuma ya ce dole ne hukumomi a Najeriya su zage dantse wajen kare fararen hula daga munanan hare-haren ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Ya shaidawa BBC cewa ''Irin waɗannan abubuwan suna yawan faruwa, b a ma jin labarin su, kuma yawancin waɗanda abin nan ya ke shafa, ba a ma maganar su domin a cikin su harda yra ƙanana,''
''Wannan yana nuna yadda wannan matsala ta Boko Haram ta ke cigaba da zama matsala ga rayuwar mutane kuma da gazawar gwamnati wajen kare rayuwar al'umma.'' In ji Isa Sanusi.
Amnesty International ta ce dole ne hukumomin Najeriya, musamman jami'an tsaro sun kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam din ta ce jami'anta masu tattara mata bayanai ne suka tabbtr da wannan lamari.
''Ka san yawanci mutanen da abin ya ritsa da su ƴan gudun hijira ne da aka mayar da su ƙauyukansu, to yawanci mutane ne da muke huɗɗa da su tsawon lokaci, suna gaya mana abubuwan da ke faruwa da su,'' in ji Isa Sanusi.
Ya yi kira ga hukumomin Najeriya su daina tursasawa mutane komawa garuruwan da suka yi hijira, idan har tsaro bai inganta a wuraren ba, saboda mafi yawa abubuwan da ke biyo baya basu da daɗi.
Ya ce ''Akwai lokacin da gwamnatin Borno ta rufe wasu sansanonin ƴan gudun hijira, ta sa mutane a mota ta mayar da su wasu garuruwa, daga ƙarshe aka kakkashe su.''
Muna samun nasara kan Boko Haram - Sojoji
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƴan kwanakin nan sojojin Najeriya sun bayyana samun nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a jihar Borno.
Ko a ranar Lahadi, sojojin sun bayyana kisan Abu Khalid, "mutum na biyu mafi girman muƙami a Boko Haram a yankin dajin Sambisa," a cewar sanarwar da sojojin suka fitar.
Sanarwar ta ce sun samu nasarar kashe Abu Khalid, da wasu mayaƙansa 10 a wani samame cikin dare da suka kai maɓoyar mayaƙan.
Kisan nasa na zuwa ne kwana daya bayan sojoji sun kawar da wani gawurtacen kwamandan Boko Haram, da ake kira Julaibib a yankin Gujba.
Ƙungiyar Boko Haram dai ta kwashe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Tun bayan fara rikicin na Boko Haram a shekarar 2009, shugabannin ƙungiyar da suka fi kaurin suna su ne Muhammad Yusuf da ya assa ta, sai kuma Abubakar Shekau wanda ya karbi jagoranci jagorancin ƙungiyar, kafin ɓallewar tsagin ISWAP ƙarƙashin jagorancin Abu Mus'ab Al-Barnawi.












