Hanyoyin daidaita lokacin motsa jiki domin samun sakamako mafi kyau

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital health editor
- Lokacin karatu: Minti 3
Masu bincike a fannin lafiya na cewa jikin mutum na da wani "agogo" na ciki wanda ke tsara lokacin bacci da tashin jiki da kuzari. Saboda haka, idan mutum ya daidaita lokacin motsa jiki da lokacin wannan agogo na jiki, zai fi samun sakamako mai kyau.
Misali, idan mutum yana cikin masu tashi da wuri, yana da kyau ya motsa jiki da safe, domin a wannan lokacin jikinsa yana da kuzari. Amma idan mutum ya fi jin ƙarfi da kuzari da yamma ko dare, to motsa jiki a lokacin zai fi masa amfani.
Binciken ya nuna cewa idan aka daidaita motsa jiki da wannan tsarin agog na jiki, zai iya ƙara inganta lafiyar zuciya, musamman ga mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya.
Haka kuma, mutanen da suka bi wannan tsarin sun samu bacci mai kyau, hawan jini ya ragu, sannan sikarin jikinsu ya fi daidaituwa. Wannan yana nuna cewa lokacin da mutum ke motsa jiki yana da muhimmanci kamar yadda motsa jikin kansa yake.
Daidaita lokacin motsa jiki da lokacin da mutum ya fi jin kuzari
Mutum 134 masu shekaru tsakanin 40 zuwa 50 a ƙasar Pakistan ne suka shiga wannan bincike.
Sun kasance mutanen da ba su da ƙwarin jiki sosai kuma kowannensu na da aƙalla da wata alamar haɗarin cututtukan zuciya, kamar hawan jini ko kiba.
An umarce su su riƙa motsa jiki na tafiya da sauri a kan na'urar tafiya ta mosta jiki wato treadmill na tsawon minti 40 a rana, sau biyar a mako, na tsawon watanni uku, tare da kulawar masana.
Bisa tambayoyin da aka yi musu, an raba su gida biyu: mutane 70 masu tashi da wuri wato su yan safe ne da kuma 64 wadanda su yan dare ne
Wasu daga cikinsu sun motsa jiki a lokacin da ya dace da lokacin jikinsu, wato lokacin da jikinsu ke da kuzari, yayin da wasu kuma suka yi a lokacin da bai dace da lokacin jikinsu ba.
Duk da cewa dukkan rukunin sun samu ci gaba a lafiyarsu, amma waɗanda suka daidaita lokacin motsa jiki da lokacin jikinsu sun fi samun fa'ida sosai.
An samu raguwar hawan jini da ƙaruwa a ƙarfin numfashi da juriya da ingantuwar sinadaran jiki, da kuma samun bacci mai kyau.
Masu binciken sun ce lokacin jiki na mutum yana shafar yadda yake bacci da farkawa, da kuma yadda hormones da kuzari ke sauyawa a rana. Wannan na iya shafar yadda mutum ke motsa jiki da kuma yadda yake iya ci gaba da shi har jiki ya saba.
Motsa jiki na bai daya - mutum ya saurari jikinsa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu binciken sun ce sakamakon ya nuna cewa tsarin "mota jiki na kowa da kowa ba shi da tasiri sosai. Wato, ba kowa ne zai amfana da motsa jiki a lokaci guda ba, domin mutane na da bambancin lokacin jikinsu.
Sun kuma bayyana cewa rashin daidaito tsakanin jadawalin rayuwar mutum da lokacin jikinsa, wanda ake kira "social jetlag", na da alaƙa da ƙarin haɗarin cututtukan zuciya. A cewarsu, masu yan dare sun fi fuskantar wannan matsala, don haka bai kamata su tilasta kansu motsa jiki da safe ba idan bai dace da su ba.
Dr Rajiv Sankaranarayanan na "Ƙungiyar Kwararrun Zuciya ta Burtaniya (British Cardiovascular Society) ya ce wannan bincike na goyon bayan a riƙa tsara motsa jiki bisa lokacin jiki saboda jiki ya saba amma ya ƙara da cewa ana buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da hakan.
A gefe guda kuma, Dr Nina Rzechorzek daga jami'ar Cambridge ta ce duk da cewa lura da lokacin motsa jiki yana da muhimmanci, abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya riƙa motsa jiki akai-akai.
Hukumar lafiya ta Burtaniya ta ba da shawarar cewa manya su:
- Riƙa yin motsa jiki na ƙarfafa tsokako ɗaga abu mai nauyi aƙalla sau biyu a mako
- Su yi aƙalla minti 150 suna motsa jiki mai sauƙi kamar tafiya da sauri, ko minti 75 na motsa jiki mai ƙarfi kamar gudu a kowane mako
- Su rarraba ranakun motsa jiki a cikin kwanakin mako ko su riƙa yin shi kullum
- Su rage zama na dogon lokaci ba tare da motsowa ba
Bincike ya nuna cewa haɗa nau'ukan motsa jiki daban-daban na taimakawa wajen samun ingantacciyar lafiya.










