Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane tasiri komawar manyan hafsoshi zuwa Maiduguri za ta yi ga tsaron Najeriya?
A Najeriya, ƙasar da wani rahoto kan alƙaluman ta'addanci a duniya ya ambata a cikin waɗanda suka ta fi fuskantar hare-hare, masanan harkokin tsaro na ci gaba da tsokaci kan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na umartar manyan hafsoshin tsaron ƙasar su koma Maiduguri.
A ranar 17 ga watan Maris ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar su koma Maiduguri na jihar Borno domin fuskantar yaƙin da jami'an tsaro ke yi da mayaƙan Boko Haram.
Ya yi umarnin ne bayan mayaƙan Boko Haram tsagin Iswap sun kai wasu muna-munan hare-hare a sansanonin sojin ƙasar, tare da kashe wasu kwamandojin soji, lamarin da ya ɗaga hankalin ƴan ƙasar.
Sai dai jim kaɗan da umarnin ne mayaƙan suka kai wasu hare-haren ƙunar bakin-wake a cikin birnin Maiduguri, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mutanen jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
Jerin hare-haren ƙunar bakin waken da aka kai ranar Litinin da ya yi sanadin kashe fiye da mutum 20 da jikkata sama da mutum 100.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsokaci kan wani sabon rahoto da ya nuna cewa yankin Sahel na Afirka ne yake da kusan rabi na kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci a shekarar 2025.
Rahoton mai taken alƙaluman ayyukan ta'addanci a duniya ya ce ƴan ta'adda sun yi ajalin mutum fiye da 5,500, inda a karon farko Pakistan ta zama can sama a jerin ƙasashen da aka fi samun kashe-kashen ta'addanci.
Za ta tasiri, amma... - Bulama
Domin jin ko wannan umarnin zai yi wani tasiri wajen magance matsalar ta tsaro, mun tattauna da mai bincike kan harkokin tsaro, Barista Audu Bukarti Bulama, wanda ya ce za a iya samun nasara idan an yi abin da ya dace.
"Wannan umarni na shugaban ƙasa zai iya taimakawa wajen yaƙi da Boko Haram idan an yi amfani da damar yadda ta dace," in ji Bukarti, sannan ya ƙara da cewa akwai hanyoyi da yake tunanin za su taimaka kamar haka:
- Gani da ido: "Yawancin manyan hafsoshin tsaron ba su da faimtar haƙiƙanin halin da ake ciki, musamman halin da sojojin ke ciki. Sojojin da ke yaƙin suna cikin ƙunci da rashin kayan aiki kuma suna da koke-koke da dama, su kuma shugabannin suna Abuja suna dogaro da rahoton da wakilansu ke ba su. Yanzu za su ga komai."
- Bayar da umarni: "A kan samu matsala wajen bayar da umarni, misali umarni ina za a kai sojoji, ko kuma yaushe za a kai su. Idan kuwa shugabanin suna kusa, da abu ya faru za a bayar da uamrni ko ma kafin abun ya faru a magance shi cikin gaggawa."
- Ƙara ƙarfin gwiwa: "Za su ƙara wa ƙananan sojoji ƙarfin gwiwa domin suna ganin ga manyan a kusa da su. Sun san idan suka yi ƙoƙari ana gani za a yaba musu, idan kuma suka yi ba daidai ba za a hukunta su."
- HaÉ—in kai: "Komawar za ta ba su dama su haÉ—a hancin aikin. Akwai matsala na rashin haÉ—in kai a aikin. Idan suka koma Maiduguri suna tare kuma za su yi shawara tare wajen gudanar da aikin."
Fargaba
A game da fargabar da ake yi cewa ko sun koma ɗin ba zama suke yi, sannan wasu ke fargabar wataƙaila ma ba za su shiga daji, inda ake tunanin hakan zai iya raba hankalin ƙananan sojojin, tsakanin yaƙi da kula da manyansu, sai Bulama ya ce ba haka abin yake ba.
"Ina ganin bai kamata ma su tsaya a cikin gari ba. Kamata ya yi su nausa cikin daji, sai su taimaka da gogewarsu wajen yaƙin. Sannan sujojin da suke gadinsu a Abuja ko a cikin Maiduguri ɗin sai su haɗu su shiga dajin tare."
Wani abun da yake kai-koma a zuciyar mutane shi ne ganin cewa ba wannan ne farau ba wajen umartar manyan hafsoshin tsaro su koma bakin daga.
Sai dai Bulama ya ce akwai buƙatar gwamnatin wannan lokacin ta tabbatar da a maimaita kuskuren baya ba.
"A lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari an yi irin wannan umarni, amma sau da yawa za ka su hafsoshin ba sa koma ba. Akwai lokacin da babban hafsan sojin ƙasa na lokacin ya ce ya koma Maiduguri, inda ya yi makonni kaɗan."
Bulama ya ce bayan babban hafsan ya koma Abuja ne ya kira taron manema labarai ya ce ya yi nasara kan Boko Haram.
"Amma a makon ne aka kashe sojoji ƙasar Chadi kusan 100, sannan aka kashe na Najeriya sama da 40. Ka ga ke nan kuskuren da ya kamata a gyara ke nan."
Masanin tsaron ya ce ko a gwamnatin Tinubu "akwai ministan da ya yi iƙirarin komawa jihar Sokota domin jagorantar yaƙi da ƴanbindiga, amma ba a daɗe muka gan shi a wasu wurare."
A ƙarshe Bulama ya yi kira da hukumomin Najeriya da su dage wajen tabbatar da an yi amfani da umarnin.
"Tunda sun koma, su tsaya a can har sai an raunata ƙungiyar Boko Haram ta yadda ba za ta iya dawowa cikin hayyacinta ba," in ji Bulama Bukarti.