Yadda mai da iskar gas suka zama makami a yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Alexey Kalmykov
- Aiko rahoto daga, BBC
- Lokacin karatu: Minti 4
Iran ta kai hari kan cibiyoyin mai da iskar gas na ƙasar Saudiyya, Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a matsayin martani kan harin da Isra'ila ta kai mata kan cibiyoyin iskar gas ɗinta wanda shi ne mafi girma a duniya.
Tun bayan fara yaƙin, Iran ta nuna aniyarta na ci gaba da kai hare-hare har sai ta haifar da tsaiko ga makamashi a fadin duniya.
An kwashe makonni uku ana gwabza yaƙi da Iran, amma kuma duka ɓangarorin babu wanda ke da niyyar lalata cibiyoyin mai da iskar gas ɗin ƙasar. Wannan ya taimaki Iran, saboda yadda take tunƙaho da dogaro da fannin wajen tsayuwa da kafafunta da cimma nasarorinta har a yaƙi da ƙasashe masu ƙarfin iko.
A yanzu dai, babu yadda Amurka za ta yi da Iran a fannin makamashi domin kulle mashigar Hormz da ta yi, ya sa ƙasashen yankin Gulf ba su iya fitar da mai da iskar gas, amma kuma ita Iran ɗin na ci gaba da siyar da man nata ga ƙasashe irinsu China, kuma Amurka ta kasa dakatar da hakan.
Farashin mai ma yana ƙara tashi, an samu ƙarancin kashi 20 na iskar gas da kuma kuma sama da kashi 10 na mai a duniya.
Iran tana amfani da jirage marasa matuƙa a 'yan tsakankanin nan domin kai hari kan cibiyoyin da ma'aikatun ƙasashen da ke goyon bayan Amurka irinsu, Qatar, Kuwait, Iraƙi, Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma manufar ita ce su ga sun haifar da fargaba da dakatar da safarar makamashi a duniya ba wai don su lalata su ba.
Cibiyoyin mai da iskar gas sun fi saukin kai hari ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, inda tun daga shekarar 2019 Iran ta nuna cewa tana ƙarfin illata waɗannan cibiyoyin.
Ita ma Amurka ta haramtawa kanta kai hari kan cibiyar man Iran na tibirin Kharg, inda kashi 90 na man da Iran take fitarwa daga yankin yake.
Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin ƙaddamar da hari kan sansanonin sojin Iran ne kawai amma banda wuraren da albarkatun mai suke, ko da yake ya ce zai iya canza shawara a kowane lokaci.
Richard Nephew, tsohon mataimakin wakilin Iran a Amurka, ya yi amannar cewa turjiyar da Iran ke yi na ƙara nuna ƙwarin gwiwar take da shi a yaƙin.
Ya ce: Ƙarfin halin da shugabannin Iran ke nunawa ya nuna cewa ta shirya wa faɗan na tsawon makonni ko watanni ko kuma shekaru. Hakan na nun cewa ba za su fusata Amurka ta hanyar lalata cibiyoyin mai da iskar gas a yankin Gulf ba."
Abin da ke faruwa

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A karon farko tun bayan fara yaƙin, Iran ta sanar da cewa an kai hari kan cibiyoyin mai da iskar gas ɗinta, wanda ɗaya ne daga cikin cibiyoyi mafi girma a duniya da ke kudancin Farisa a yankin Gulf.
Iran ce ke da iko da yankin na kudancin Farisa, yayin da Qatar ke da iko da arewacin yankin.
Qatar ce take samar da kusan kashi 20 na gas a duniya, amma tun bayan fara yaƙin, ta kulle matatar gas ɗinta da ke Ras Laffan, lamarin da ya sa farashinsa ya ƙaru a Nahiyar Turai da Asiya.
Matatar gas ta kudancin Farisa ba ta da wani muhimmanci ga Iran kamar yadda mai yake, saboda ta fi fitar da mai kuma yawanci tana amfani da gas ɗinta a cikin gida sai ɗan kaɗan da ake fitarwa zuwa Iraƙi.
Bayan harin da aka kai mata, Iran ta yi barazanar kai hari kan cibiyar gas ta Qatar da ke Ras Laffan, wanda zai iya yin mummunar ɓarna da kuma haifar da cikas a kasuwannin duniya. Iran t kuma gargaɗi Saudiyya da ta mayar da manta zuwa manyan matatun ta guda biyu, kuma ta yi irin wannan gargaɗin ga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa game da gas ɗinta.
Qatar ta yi kakkausar suka ga Isra'ila kan harin da ta kai kan cibiyoyin mai da iskar gas ɗin Iran, inda ta ce "harin na da matuƙar haɗari."
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce: "Hari kan cibiyoyin makamashi barazana ce ga duniya kuma haɗari ne ga muhalli."











