A wane hali Sheikh Sani Khalifa Zaria yake?

Asalin hoton, SOCIAL MEDIA
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana ci gaba da nuna damuwa a Najeriya game da raɗe-raɗin rasuwar malamin addinin Musulunci a ƙasar, Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zaria da ke tsare a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta (DSS).
Tun bayan ɓullar wani bidiyo a shafukan sada zumunta da wani matashi ya yi iƙirarin rasuwar malamin, hankula suka tashi a sassan ƙasar musamman daga iyalai da ɗalibansa.
Masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam da manyan ƴansiyasa a ƙasar na ci gaba da yin tambayoyin matsin lamba ga hukumomin Najeriya da su gurfanar da malamin a gaban shari'a ko su sake shi idan babu wata hujja.
BBC ta tattauna da iyalan Sheikh Khalifa Zaria da kuma waɗanda ke bibiyar lamarin tun bayan da aka kama shi a ranar 11 ga watan Disamban 2025, game da jita-jitar rasuwar.
Da me ake tuhumar malamin?
Wasu rahotanni sun ce tsare Sheikh Sani Khalifa ya samo asali ne daga zargin tura masa kuɗi zuwa asusun bankinsa da wani jami'in soja ya yi.
Iyalan malamin sun ce suna zargin an kama malamin ne bayan kyautar Naira miliyan biyu da wani ɗalibin shugaban ɗariƙar Tijjaniya ta Fityanul Islam ya ba shi, da aka yi zargin jami'in yana da hannu a yunƙurin juyin mulkin.
Hukumar leƙen asiri ta Najeriya (DIA) ce ta kama malamin a shekarar da ta gabata bisa zargin sa da hannu a yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda daga bisani ta miƙa shi ga hukumar DSS.
A ranar 18 ga watan Fabrairun 2026, babbar kotun tarayyar ƙasar a Abuja, ƙarƙashin mai shari'a Peter Lifu, ta umurci DIA ta gabatar da malamin domin duba yiwuwar bayar da belinsa amma hakan bai yiwu ba.
Ana tsare da malamin ne a wani wuri na musamman cikin sirri, kuma har yanzu ba a bai wa iyalansa da lauyoyi damar ganawa da shi ba, inda ake cewa ana ci gaba da bincike.
Abin da iyalansa suka ce
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A hirarsa da BBC, ɗaya daga cikin ƴaƴansa Ibrahim Sani Khalifa, ya ce tun da aka kama mahaifin nasu har yanzu ba su yi ido biyu da shi ba, kuma an hana shi ganawa da lauyoyinsa.
Ya ce hukumomin sun ƙi ce musu komai game da matakin da suke dauka na gurfanar da shi ko kuma abin da suka gano a bincikensu.
"Yadda kowa yake jin wannan bayani haka muke jin shi, ba abin da hukumomi suka ce mana. Rabon da mu gan shi, tun ranar da aka tafi da shi, babu wanda ya ƙara ganin shi, ko jin muryarshi, ba mu ga wanda ya gan shi ba ma har yau" in ji Ibrahim.
Ya ce lauyoyi sun yi duk mai yiwuwa a kan a bayar da belinsa amma an yi biris da su.
Ɗan malamin ya ƙara da cewa hankalinsu ya tashi da suka fara ganin jita-jitar rasuwar mahaifin nasu, amma ba za su iya tabbatar da hakan ba a yanzu, saboda sun kasa samun cikakkun bayanai daga hukumomin Najeriya.
"Wannan al'amari [na mutuwar] dai ba za mu iya cewa eh ko a'a ba. Idan aka tambaye mu ina hujja, ba mu da ita."
"A hukumace ba a ba mu bayani cewa ba yana nan ba, ko ya samu rasuwa ko wani abu ya faru."
Iyalan nasa sun buƙaci gwamnatin Najeriya su gabatar da shi a gaban shari'a idan har akwai abin da ake zargin sa da shi kuma a ba su damar ganin mahaifin na su.
Sheikh yana raye - Rahma Abdulmajid
BBC ta tuntuɓi mutanen da ke da alaƙa da binciken da ake yi inda suka shaida mana halin da Shehin malamin yake ciki.
Daya daga cikin masu taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin yaɗa labarai, Rahama Abdulmajid, wadda take bibiyar lamarin a matsayinta na ɗalibar Tijjaniya, ta ce majiyoyi masu ƙarfi sun shaida mata cewa an kusa gurfanar da malamin.
Ta kuma tabbatar da cewa malamin na cikin ƙoshin lafiya, ba kamar yadda ake yaɗawa cewa ya rasu ba.
Ko da yake ita ma ta ce ba ta samu damar yin ido biyu da shi ba amma ta samu tabbaci daga majiyoyi masu ƙarfi.
"Lallai lallai yana da rai da lafiya, kuma duka wannan magana ba ta wuce batu na soshiyal midiya ba, mutanen da suke ba da cikakken bayanai kan yanayin da ake ciki, su muka tuntuɓa, kuma Alhamdulillahi sun ce mana babu wannan zance" in ji Rahama.
"Abin da muke nema shi ne a bi doka wajen kawo shi, kowa ya ganshi, ina ga wadanda suka fi cancanta su gan shi, iyalansa ne waɗanda suna cikin damuwa fiye da mu".
Me hukumomi suka ce?
Har yanzu dai, hukumomin Najeriya ba su fito fili sun yi ƙarin bayani game da batun jita-jitar rasuwar malamin ba duk kuwa da yadda suke shan suka da matsin lamba daga ƴan Najeriya.
Hukumar DSS ce ke ci gaba da tsare Sheikh Khalifa Zaria, inda har yanzu ba ta ba kowa damar ganin sa ba.
BBC ta tuntubi mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, ta waya amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoton bai amsa kiran da muka masa ba.
Mun kuma tura masa saƙo ta manhajar WhatsApp, amma bai amsa buƙatar ba, duk da alamu sun nuna cewa ya buɗe saƙon da muka aika.
A saki Sheikh Khalifa ko a gurfanar da shi a kotu – Atiku

Asalin hoton, X/@ATIKU
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta sakin malamin ko kuma su gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da ɓata lokaci ba.
Atiku ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, inda ya nuna damuwa kan yadda ake tsare Sheikh Khalifa tun watan Disambar 2025, amma har yanzu ba a kai shi kotu ba.
Ya ce ci gaba da tsare malamin ba tare da gurfanar da shi a kotu ba, ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma haƙƙin ɗan'adam.
Haka kuma ya nuna damuwa kan yadda ake ta yaɗa jita-jita game da halin da malamin yake ciki, inda ya ce ƙin yin magana da hukumomi suka yi na ƙara haifar da rashin tabbas dangane da lamarin.
"Najeriya ba za ta iya ci gaba da kiran kanta ƙasa mai dimokuraɗiyya ba alhali ana yawan take haƙƙin 'yan ƙasa a fili," in ji Atiku.
"Ba za a iya samun dimokuraɗiyya ba tare da cikakken bin doka ba. Babu wata hukuma ta tsaro da ta fi kundin tsarin mulki, kuma babu wadda ke da ikon ɗaukar haƙƙin 'yan ƙasa a matsayin wani abu da zai juya yadda yake so".
Ya ƙara da cewa hana Sheikh Khalifa damar ganin iyalansa, lauyoyinsa da kuma samun kulawar lafiya ya nuna take haƙƙinsa na ɗanƙasa.
Su ma masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam suna ta miƙa ɓukatar sakin malamin ko gurfanar da shi.
Fitaccen lauya a Najeriya, Barista Abba Hikima, ya wallafa a shafinsa na sada zamunta cewa, idan rahotannin da ake yaɗawa suka tabbata, dole a zargi gwamnatin Bola Tinubu da alhakin duk abin da ya samu malamin.
Shi ma wani lauya Barista Abdul-Hadee Isah Ibraheem da ya yi tsokaci kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin musamman zarge-zarge da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, ya ce bai kamata gwamanati ta yi shiru kan batun ba.
Sheikh Khalifa dai ya shigar da ƙarar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annuti ta EFCC da DIA da babban lauyan gwamnatin tarayya da ministan shari'a da kuma bankin Jaiz, tare da neman a sake shi.











