Real Madrid da Barca na zawarcin Kees Smit, Arsenal na fuskantar hamayya kan Goretzka

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta fuskanci gasa daga Juventus wajen sayen Leon Goretzka, ɗan wasan tsakiya na Jamus mai shekara 31, wanda ake sa ran zai bar Bayern Munich idan kwantiraginsa ya ƙare a lokacin rani. (Gazzetta dello Sport)
AC Milan na sa ido kan ɗan wasan gaba na Jamhuriyar Ireland Troy Parrott, mai shekara 24, wanda farashinsa zai kai kusan fam miliyan 25 daga AZ Alkmaar a lokacin bazara. (Independent)
Brighton na ƙoƙarin kammala yarjejeniya da Cologne domin ɗaukar ɗan wasan gefe na Jamus mai shekara 19 Said el Mala bayan ya sauya wakilansa. (Bild)
Manchester City na iya barin ɗan wasan gefe na Brazil Savinho, mai shekara 21, ya tafi a lokacin bazara, inda Tottenham za ta iya neman sa idan ta ci gaba da zama a gasar Premier League. (Football Insider)
Juventus za ta mayar da hankali kan ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva na Manchester City, mai shekara 31, bayan ta rage sha'awarta ga Sandro Tonali na Newcastle mai shekara 25, saboda Manchester United da Arsenal duk suna son ɗan wasan na Italiya. (Gazzetta dello Sport)
Fulham ta cimma yarjejeniyar baka, don ɗaukar ɗan wasan gaba na Amurka Ricardo Pepi mai shekara 23 daga PSV Eindhoven, har ma an riga an amince da sharuddan daukarsa. (Fabrizio Romano)
Xabi Alonso zai nemi sayen Alessandro Bastoni na Inter Milan (mai shekara 26), da Adam Wharton na Crystal Palace (mai shekara 22), da Bradley Barcola na Paris Saint-Germain (mai shekara 23) idan ya maye gurbin Arne Slot a Anfield a lokacin rani. (Teamtalk)
Manchester United ta tuntubi Ajax domin bincika yiwuwar yarjejeniya kan ɗan wasan gaba na Belgium mai shekara 20 Mika Godts. (Sacha Tavolieri)
Real Madrid da Barcelona suna gaba da ƙungiyoyin Premier League wajen neman ɗan wasan tsakiya na Netherlands mai shekara 20 Kees Smit daga AZ Alkmaar, saboda yana son komawa Spain domin rayuwa a wuri mai rana. (AS Spanish)
Manchester United da Liverpool suna ƙara nuna sha'awarsu ga ɗan wasan tsakiya na Wolves da Portugal Joao Gomes mai shekara 25. (Teamtalk)
Kocin Barcelona Hansi Flick zai tsawaita kwantiraginsa zuwa 2028 bayan Joan Laporta ya sake zama shugaban ƙungiyar. (Florian Plettenberg)










