Arsenal ta dage kan Franca, Liverpool na gaban Chelsea a zawarcin Camavinga

Wesley Franca

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Man City da Utd duk sun yi gogayya a kan Wesley Franca
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta dage a neman dan baya na bangaren dama, inda take sa ran sayen Wesley Franca na Roma, dan Brazil mai shekara 22. (Teamtalk)

Liverpool na gaban Chelsea a fafutukar sayen dan wasan tsakiya na Real Madrid Eduardo Camavinga, na tawagar Faransa, mai shekara 23, inda ta tattauna da wakilansa har sau biyu. (Caught Offside)

Kociyan Barcelona Hansi Flick, ya ce bai san abin da zai faru da Marcus Rashford ba, inda kungiyar take da damar sayen dan wasan na Ingila mai shekara 28 da ta karba aro daga Manchester United. Barca za ta iya sayensa ya zama nata dindindin a kan fam miliyan 26. (Manchester Evening News)

Arsenal na cikin matsin lamba kan ta sayar da 'yan wasanta a bazara, inda ake ganin wasu 'yan kalilan daga cikin manyan 'yan wasanta ba za su tabu ba. (Telegraph)

Dan wasan gaba na gefe na Barcelona da Brazil Raphinha, mai shekara 29, ya kawar da yuwuwar barin Nou Camp kafin karshen kakar 2026-27 duk da zawarcinsa da ake yi zuwa Saudiyya. (Sport)

Dan wasan tsakiya na Newcastle Bruno Guimaraes, mai shekara 28, ya tabbatar da ci gaba da zamansa a kungiyar, kuma dan Brazil din ba zai kafe ba lalle sai an kara masa albashi ya fi na kowa a kungiyar a matsayin wani sharadi na sabunta kwantiraginsa. (Newcastle Chronicle)

An dakatar da maganar cinikin da Fulham ke yi na sayen dan wasan PSV Eindhoven, mai kai hari Ricardo Pepim mai shekara 23, duk da cewa an kammala duba lafiyar Ba'amurken. (Fabrizio Romano)

Ba wani daga cikin 'yan wasan Chelsea da ya nemi barin kungiyar a bazara duk da rashin katabus da kungiyar ke yi. (Mail)

Watakila Barcelona da Real Madrid na sha'awar, Erling Haaland, amma kuma, Manchester City ba ta da niyyar sakin dan wasan na Norway mai shekara 25, ya bar ta a bazaran nan. (Football Insider)

Juventus na duba yuwuwar daukan Antonio Rudiger, dan Jamus mai shekara 33, wanda kwantiraginsa da Real Madrid zai kare a bazara. (Tuttosport)

Atletico Madrid ta taya dan wasan tsakiya na Atalanta Ederson mai shekara 26 a kan fam miliyan 30 da sauran tsarabe-tsarabe na fam miliyan 4, a shirin da suke yi na cinikin 'yan wasa a bazara. (Football Italia)