Dalilin da ya sa nake goyon bayan ɓangaren Wike a PDP - Sule Lamido

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilansa na nuna goyon baya ga ɓangaren Ministan Abuja Nyesom Wike a jam'iyyar PDP.

Babbar jam'iyyar hamayyar ta Najeriya PDP na ci gaba da nutsewa cikin rikici bayan da kotu ta tabbatar da jagorancin ɓangaren tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja Nyesom Wike.

A hirarsa da BBC, Alhaji Sule Lamido ya ce muddin ana son a samu sulhun da zai fitar da jam'iyyar daga rikici, dole masu ruwa da tsaki a jam'iyyar su rungumi kwamitin rikon jam'iyyar karkashin jagorancin Alhaji Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan Abuja.

Ya ce hakan ya zama dole kasancewar ɓangaren ya samu amincewar hukumar zabe ta INEC, "don haka shi ya kamata a bi a matsayin wani mataki na warware rikicin PDP da ya dabaibaiye jam'iyyar," in ji shi.

Wannan mataki na Sule Lamido ya zo da mamaki kasancewar yana cikin jiga-jigan PDP da suka yi adawa da Nyesom Wike wanda suke zargi shi ya jefa jam'iyyar cikin ruɗanin da take ciki inda har ta rasa gwamnoni da dama.

Kodayake Alhaji Sule Lamido ya yi adawa da babban taron PDP da ɓangaren Tanimu Turaki ya gudanar a birnin Ibadan inda ya nemi a rushe shugabannin riƙo da aka zaɓa bayan hana shi takara.

A watan Oktoba ne aka hana shi damar sayen fom ɗin tsayawa takarar shugabancin PDP, lamarin da ya sa ya garzaya kotu, kuma matakin da ya kai ga rusa sakamakon babban taron Ibadan.

Wasu za su yi mamakin yadda yanzu tsohon gwamnan na Jigawa ya dawo yana kiran a dawo a bi jagorancin ɓangaren Wike.

'Ba mu da zaɓi illa mu bi kwamitin Wike'

Alhaji Sule Lamido ya ce duk wani mai kishin PDP yanzu ba ya da wani zaɓi illa ya bi kwamitin riƙo da ke samun goyon bayan Wike.

"Shi ne kwamitin da doka ta amince kuma wanda hukumar Inec ta aminta da shi."

"Ko kana son Wike ko ba ka son shi, a yanzu kwamitin riƙonsa ne a hukumar zaɓe a Najeriya," in ji Sule Lamido.

Ya ce idan dai har mafita ake nema wa PDP don a yi takara a zaɓen da ke tafe dole duka ɓangarorin jam'iyyar a zo a zauna a yafi juna, sannan a kira Wike a zauna sulhu da shi.

"Yanzu Wike da APC da Tinubu ne suka fi cin ribar rikicin PDP idan har ba mu cire son zuciya ba," a cewar Sule Lamido.

Ya kuma ce idan an shigar da kowane ɓangare a kwamitin riƙo na Wike, za a iya sake fasalta shi a gabatar wa hukumar zaɓe.

"PDP na sheɗa ne saboda Wike"

Ya ce Wike bai fito ya ce ya bar PDP ba, don haka dole a ɗauke shi har yanzu ɗan jam'iyyar ne.

Sule Lamido ya ce yadda gwamnoni suka fice daga PDP, hakan ya nuna yanzu babu inda PDP take da rai idan ba ɓangaren Wike ba.

"Tun da yanzu haka ne, sai mu zo a zauna mu tunkari Wike mu ce masa jam'iyyar nan ba taka ba ce, muna son a yi wa kwamitinka kwaskarima ya ƙunshi kowa."

"Babbar manufar ita ce a samu ƴantakara a jam'iyyar PDP a kowane sashe na Najeriya," in ji Sule Lamido.

Tsohon gwamnan na Jigawa ya yi watsi da zargin da wasu ke yi cewa ya sauya ra'ayi ne saboda tunanin an yi masa wani alƙawali a gwamnatin APC ko kuma saboda shari'ar da ake yi masa da ƴaƴansa.

"Ni wannan ra'ayi nawa shi ne tun da har doka ta amince da ɓangaren Wike to a dawo a tunkare shi,"

"Mu faɗa masa cewa mun san kana yi wa Tinubu aiki, amma ka ɗora ɗantakararka na Rivers na PDP, idan aka yi haka, dole a samar da ƴantakara a jihohin Jigawa da Kano da Sokoto da Kebbi da sauran jihohi," a cewar Sule Lamido.

Masharhanta da dama dai na zargin daga waje ake kunno wutar rikicin cikin gida na PDP domin tabbatar da cewa ba ta taka rawar gani ba a babban zaɓen ƙasar mai zuwa.

Wasu na ganin idan har rikicin PDP ya ci gaba, za ta iya rasa damar shiga zaɓen 2027.