Abin da ya sa ƙwayoyin halitta na haihuwa ke da sarkakiya

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙwayar halittar haihuwa, wata aba ce da maza ke so saboda tana ɗauke da ƙwayoyin hallitar gado waɗanda ke gano mazantaka da kuma samar da maniyyi.

Yana ɗauke da ƙwayoyin halitta kalilan.

Sakamakon bincike kan wannan batu ya samar da madogara mai ƙarfi don yin bincike kan yadda ƙwayoyin halitta da kuma maniyyi ke aiki, yadda ƙwayar halittar ta samo asali da kuma ko cewa za ta ɓace cikin shekaru miliyan kaɗan, kamar yadda aka yi hasashe.

Samun jarirai maza

Mun sani sama da shekara 60 cewa wasu ƙwayoyin halitta sun ƙware wajen gano abin da za a haifa a tsakanin ƴan adam da kuma sauran dangin dabbobi masu shayarwa.

Mata na da ƙwayoyin halitta na X da ke aiki tare wuri ɗaya, yayin da maza ke da guda ta X da kuma karamar ƙwayar halitta ta Y.

Mai na'uin Y shi yake alamta jariri namiji da za a samu saboda shi yake ɗauke da ƙwayar halitta da ake kira SRY, wadda ke jagorantar wasu ƙwayoyin halitta su zama ɗan tayi.

Ɗan tayin shi yake samar da sinadaran namiji, kuma waɗannan sinadarai suke jagorantar har halitta ta zama namiji.

Ba tare da ƙwayar halittar Y da kuma ƙwayar halitta SRY ba, waɗannan ƙwayoyin halitta suna ci gaba a mazaunin kwai zuwa ɗantayi na XX. Sannan sinadaran mata daga baya su samar da jaririya ta mace.

Ƙwayoyin halitta na DNA

Ƙwayar halittar haihuwa ta Y tana da bambanci da ta X da kuma wasu ƙwayoyin halittar haihuwa 22 da ke cikin ƙwayar halittar ɗan'adam. Karami ne kuma yana ɗauke da ƙwayoyin halitta kalilan (guda 27 idan aka kwatanta 1,000 wanda kwayar halittar X ke da shi).

Ƙwayar halitta ta Y tana da ƙwayoyin halitta na DNA da dama waɗanda ba a cika gani ba.

Ƙwayar halitttar na cike da ƙwayoyin halitta na DNA waɗanda yawanci suke baƙaƙe; ba a iya ganin su sai da na'urar hangen nesa na microscope.

Me ya sa ƙwayar halittar Y ke da tsarkakiya?

Me ya sa Y yake haka? A ɗora laifin haka kan sauye-sauye.

Muna da hujjoji da ke nuna cewa shekaru miliyan 150 da suka wuce, ƙwayoyin halitta na X da Y na haɗe tare.

Sannan, aka samar da ƙwayar halitta ta SRY daga waɗannan ƙwayoyin halitta biyu.

Akwai muhawara sosai kan cewa ko ƙwayoyin za su daidaita saboda ganin cewa a wannan yanayi dukkan ƙwayoyin halitta na Y za su ɓace a cikin shekaru miliyan kalilan da ke tafe (kamar yadda ya riga ya faru a wajen ɓeraye).

'Aikin jera ƙwayoyin halittar ba karamin aiki bane'

An kammala aikin tsara ƙwayoyin halitta a shekara ta 1999. Tun wancan lokaci, masana kimiyya sun yi ƙoƙarin jera ɗaukacin ƙwayoyin halitta, ciki har da X.

Sun yi aikin ne ta hanyar yanka ƙwayar halitta ta DNA zuwa ƙanana-ƙananan tushe guda 100 da kuma sake harhaɗa su.

Sai dai, a baya-bayan nan an samu wata fasaha da ke ba da damar jera ƙwayoyin halittar na DNA, abin da ke janyo samun dubban tushe-tushe.

Duk da fasaha da aka samu, jera ƙwayoyin halitta na DNA ya zama babban aiki, kuma masu bincike sun yi ta ƙoƙarin gwada sa'ar su a yanayi mai wahala.