Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda hare-haren Iran suka faɗa kusa da cibiyar nukiliyar Isra'ila
Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami a garuruwan Arad da Dimona da ke kudancin Isra'ila, inda suka jikkata akalla mutum dari.
Dimona na kusa da wata mahimmiyar cibiyar makaman nukiliya ta Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun ce suna gudanar da binciken dalilin da ya sa ba a kakkabo makaman na Iran ba.
Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta nemi a kai zuciya nesa bayan harin Iran kan cibiyar nukiliyar Isra'ila a Dimona.
Jami'an agajin gaggawa sun ce harin ya shafi ginin cibiyar nukiliyar kuma barnar da aka yi na da girma.
An yi imanin cewa wurin da Isra'ila ke kira cbiyar binciken nukiliya, da Iran ta kai wa hari, yana dauke da makamin nukiliyar Isra'ila. Iran ta ce harin martani ne ga harin da Isra'ila ta kai a daya daga cikin cibiyoyin nukiliyarta a Natanz.
Iran kuma ta sake kai hari a garin Arad, kuma jami'an lafiya na Isra'ila sun ce sama da mutum 70 suka jikkata a harin tare da lalata gidaje da dama. A Dimona kuma sama da mutum 30 ne suka jikkata.
Isra'ila ta ce za ta yi binciken dalilin da ya sa har aka kasa harbo makamin da Iran ta yi amfani da shi wajen kai harin tare da gargadin cewa za ta ci gaba da kai wa Iran hari.
A wani sabon gargaɗi, shugaba Trump ya ba shugabannin Iran wa'adin sa'a 48 su buɗe mashigar Hormuz, inda ya yi barazanar tarwatsa gaba dayan tashoshin samar da lantarki na Iran.
Wannan ba shi ne karon farko da Trump ke barazanar kai hari kan tashoshin samar da makamashi na Iran ba.
A ranar Alhamis ya ce Amurka za ta tarwatsa tashar samar da iskar gas ta South Pars.
Iran ta mayar da martani da cewa muddin aka kai wa kayayyakinta na mai da makamashi hari, ba makawa za ta mayar da martani ta hanyar kai hari a kan dukkanin wasu kayayayyakin samar da makamashi na Amurka da ke yankin.