Illar yin aure bayan shekara 35 ga maza

Lokacin karatu: Minti 3

Mazan da suka bari sai bayan sun wuce shekara 35 sannan suka yi aure na cikin haɗarin samun yara bakwaini ko kuma masu ɗauke da lalurar da kan shafi ƙwaƙwalwa ta galhanga.

Baya ga haka kuma, a kowace shekara inganci da yawan maniyyinsu na raguwa, har sai sun yi aure.

An gano hakan ne a bincike-bincike da dama da aka yi a tsawon shekaru.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan bincike da aka yi sashen koyar da likitanci na jami'ar Stanford da ke ƙasar Amurka, ya yi nazari kan jarirai kimanin miliyan 40.

Duk da cewa mutane da dama ba su da masaniya kan irin waɗannan bayanai, amma abin farin cikin shi ne masana sun bayar da shawarar cewa mutanen da suka kai wannan mataki ya kamata su riƙa zuwa ana duba su domin guje wa haihuwar yara masu matsala.

Dakta Karla Giusti Zacharias, wadda ƙwararriyar likita ce a ɓangaren samun haihuwa a asibitin Sao Luiz Itaim da ke birnin Sao Paulo a ƙasar Brazil, ta ce tana ganawa a kai- akai da maza masu neman haihuwa.

"Nakan samu maza waɗanda suka zarce shekara 40 zuwa 60 kuma sun auri mata masu ƙananan shekaru, kuma suna neman haihuwa," in ji ta.

"Sukan tambaye ni: 'mece ce illar haihuwar yara ga namijin da shekarunsa suka ja?'''

"Ƙwayoyin samun haihuwa na mace sun sha bamban da na namiji kuma suna aiki ta hanya daban-daban," in ji ta.

"Yayin da mata suke da taƙaitattun ƙwayoyin haihuwa, maza kuwa na iya haihuwa har ƙarshen rayuwarsu."

Saboda haka ƙwayoyin da ke samar da maniyyin namiji ba su ƙarewa, sai dai ingancinsu na raguwa kuma hakan na faruwa ne yayin da mazan suka kai wasu shekaru, in ji Dr Zacharias.

Yayin da namiji ke ƙara tsufa, ƙwayoyin halittarsa kan rage girma kuma ƙarfin aikinsu na raguwa, hakan na iya zama haɗari ga jariran da za a haifa.

Bincike da dama sun nuna cewa ko da yaron da aka haifa ya kauce wa kamuwa da wasu cututtukan, akwai yiwuwar ya yi fama da cutukan da suka shafi hanyoyin lumfashi da kuma lalurar ƙwaƙwalwa.

Mazan da suka zarce shekara 35 a duniya sun fi shiga hatsarin haihuwar yara marasa nauyi, ko kuma waɗanda ke buƙatar a saka su a kwalba.

Mece ce galahanga?

Galahanga dai shi ne haifar yaro da wasu ƙarin ƙwayoyin halitta.

Yanayin ƙwayoyin halittar yawanci na shafar koyon wani abu da zai yi da kuma yanayin jikinsa.

Lalurar ba cuta ba ce, illa rashin lafiya ko yanayin da wani zai iya kamuwa da shi.

Ba a dai san me ke haddasa lalurar ba - saboda kawai haifar mutum ake yi da ita.

Yawanci mutanen da aka haifa da lalurar suna samun ƙarin ƙwayoyin halitta, saboda canjin maniyyi ko kwai kafin a haife su.

Ana samun waɗanda ake haifa da lalurar ko'ina a yankuna da ke faɗin duniya kuma galibi tana yin tasiri a kan salon koyo, halayen jiki da kuma lafiya, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ana haifar jariri ɗaya cikin 800 da galahanga, a cewar masu shirya bikin Ranar Galahanga ta Duniya .

Lalurar tana da nau'o'i guda uku amma (trisomy 21) wanda shi ne nau'i na yau da kullum - inda ake samun waɗanda ake haifa da wasu kwayoyin halitta.

An saka wa lalurar sunan wani likita ne Dr John Langdon Down wanda shi ne mutum na farko da ya fara rarraba nau'o'inta.

Alamomin lalurar sun kunshi:

  • Lallausar fuska, musamman kan hanci
  • Idanu waɗanda suka karkata sama
  • Gajeren wuya
  • Layi ɗaya a kan tafin hannu
  • Rashin tsayi kamar yara da manya