Me zai faru idan Gawuna ya koma wurin Kwankwaso?

Asalin hoton, Kwankwaso/Gawuna/Facebook
Al'amura na kara rincaɓewa tare da tashin ƙura a siyasar Kano gabanin kakar zaɓen shekarar 2027 da ke ƙaratowa, tun bayan da aka fara yaɗa jita-jitar cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna zai koma wurin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Nasiru Yusuf Gawuna ya yi takarar neman kujerar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar APC a 2023, inda ya fafata da gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP.
Nasiru Gawuna ya kasance ɗan takarar tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a jam'iyyar APC, inda shi kuma tsohon gwama, Rabi'u Musa Kwankwaso ya tsaya wa Abba Kabir Yusuf a jam'iyyar NNPP.
Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ɗan gidan sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya sauya sheƙa zuwa ɓangaren Abdullahi Ganduje, sai kuma jita-jita mai ƙarfi da ke nuna shi ma Nasir Gawuna wanda ke gidan Ganduje na ƙoƙarin sauya sheƙa zuwa gidan Kwankwasiyya.
Gaske ne Gawuna zai koma wurin Kwankwaso?

Asalin hoton, Gawuna Facebook
Babu wani tabbaci daga shi Nasiru Gawuna dangane da batun sauya sheƙar tasa zuwa wurin sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Sai dai kuma wani bidiyo da ya rinƙa karakaina inda a ciki Kwankwason yake jawabi ga wasu ƴan ƙungiyar da ke goyon bayan tsohon mataimakin gwamnan jihar ta Kano, Nasiru yusuf Gawuna, da suka ziyarci tsohon gwamnan domin nema wa gwaninsu wuri a tafiyar Kwankwasiyya.
"Na ji kuna cewa a rushe bulo takwas tunda dama katangar ɗaya...to a ma rushe katangar gabaɗaya mana. Allah ne ya san dalilin kawo shi wurin ni ma ya kawo ni wurin muke zama a matsayin maƙwabta.
"Kuma shi Gawuna yana cikin kwamishinonina masu daraja...duk halin da ya samu kansa ban taɓa ya yi wata magana ta ɓatanci ba. Kuma mun haɗu da shi a wurare da dama, yadda yake girmama ni muna ofis bai sauya ba...saboda haka magana ce tun da ni ma na ji ta nake murna".
Bugu da ƙari, jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa fadar shugaban Najeriya ta yi ƙoƙarin samun Nasiru Gawuna a waya domin hana shi sauya sheƙar. Sai dai har kawo yanzu babu wani martani na musanta labarin daga fadar ko kuma wani jigo a APC.
Dakta Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS ya ce alamu ne masu ƙarfi da ke nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan ka iya komawa wurin Kwankwaso bisa la'akari da abin da ya faru.
"Idan aka yi la'akari da yadda ƙungiyar ta je tana neman a duba yiwuwar samar musu gurbi a tafiyar (Kwankwasiyya) ...sannan duk da dai ba a ji daga bakin Nasiru Yusuf Gawuna ba amma ziyarar da magoya bayansa suka kai wa Kwankwaso da kuma kalaman da Kwankwason ya yi....to za a iya samun komawarsa," in ji dakta Kabiru.
Me komawar Gawuna wurin Kwankwaso ke nufi?

Asalin hoton, Kwankwaso/Facebook
Dakta Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS ya ce komawar Gawuna wurin Kwankwaso na tare da nasarori da kuma ƙalubale.
"Nasarar da za a samu ita ce ga Rabi'u Musa Kwankwaso wanda hakan na nufin zai maye gurbin abin da ya rasa na gwamna Abba Kabir Yusuf. Sannan shi ma Gawuna zai iya samun gurbin da ya rasa."
"Sai dai kuma akwai ƙalubale ga dukkanninsu. Misali ga Kwankwaso zai fuskanci ƙalubalen gurbin da zai saka Gawuna kasancewar akwai waɗanda suka daɗe suna biyayya saboda haka suna sa rai wato mece ce makomarsu. Hakan ka iya janyo a saɓawa waɗanda ya tarar a tafiyar"
"Sai kuma ƙalubale ga Ganduje da jam'iyyar APC wanda ke nuna cewar za a samu gagarumin rashi kasancewar shi ne ya yi takara kuma ya samu karɓuwa kuma hakan na nufin akwai yiwuwar tafiya da mutane da dama".
Me ya sa Gawuna ke son barin APC?
Dakta Kabiru Sufi ya ce babban dalilin da ka iya sa Gawuna ya sauya sheƙa shi ne yadda bai samu tagomashi ba bayan rashin nasararsa a takarar da ya yi a 2023.
"Duba da yadda tun bayan rashin nasarar da Gawuna ya yi a zaɓen da ya gabata, bai samu wani matsayi ba daga gwamnatin APC. Wataƙila wannan ne ke damun sa yake tunanin ya koma wani wuri inda zai iya samun wani gurbi."
A watan Yunin 2025 ne dai shugaba Tinubu ya naɗa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin lamunin gidaje na Najeriya.
Da dama dai musamman magoya bayan tsohon mataimakin gwamnan na Kano sun yi tsammanin Gawunan zai samu wani muƙami kamar na minista wanda zai ba shi damar riƙe magoya ba.










