Shin ya kamata turawa su biya diyyar bautar da ƴan ƙasashen Afrika?

A 19th Century photograph shows black enslaved people in chains at a market on the island of Zanzibar. They can be seen looking at the camera.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani ƙudiri da ya ayyana bauta a matsayin "mafi munin laifin cin zarafin bil'adama". Ƙudirin ya kuma buƙaci "a gaggauta maido da kayan tarihi da al'adu da aka sace ba tare da ɓata lokaci ba." Kayan da za a mayar zuwa ƙasashen su na asali sun haɗa da kayan zane-zane, da na tarihi da takardun ƙasa ba tare da wata tuhuma ba.

Shugaban Ghana John Mahama ne ya miƙa buƙatar kuma kungiyar Tarayyar Afirka ta goyi bayansa domin dannar ƙirji da neman biyan diyya.

Ƙasashe 123 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da kudurin, yayin da kasashe 52 suka ƙi kaurace wa jefa ƙuri'ar ciki har da Burtaniya da kasashe mambobin Tarayyar Turai, sai kuma uku da ba su amince ba.

Amurka da Argentina da Isra'ila sun kaɗa kuri'ar ƙin amincewa da ƙudurin.

"Amincewa da wannan kuɗurin ya zama kariya," in ji Mahama ga majalisar.

Ƙasashen da aka bautar da su sun shafe fiye da shekaru 100 suna neman diyya. Sai dai muhawara kan batun ta ƙara zafi ne a karni na 21, musamman bayan da wasu ƙasashe da 'yan kasuwa da a tarihi suka ci gajiyar bayi na Afirka suka amince cewa suna da hannu a safarar bil'adama.

A statue of a man and a woman in chains at Goree Island in Senegal. The place is known as 'Island of Shame' due to it being a major outpost of the transatlantic slave trade between the 15th and 19th centuries.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Kimanin 'yan Afrika miliyan 12 zuwa 15 ne aka yi safararsu domin aikin bauta

Mece ce diyyar bautar da ɗan'adam?

Daga ƙarni na 15 zuwa na 19, an kama maza da mata da yara kimanin miliyan 12 zuwa 15 a Afirka kuma aka yi fataucinsu zuwa ƙasashen Amurka don yin aiki a matsayin bayi.

An tura su zuwa kasashen Turai irinsu Sifaniya, Portugal, Faransa da Birtaniya. An yi ƙiyasin cewa mutane sama da miliyan biyu ne suka mutu a cikin manyan jiragen ruwan da ke dakon bayi.

Har yanzu ana jin raɗaɗin cin zarafin da aka yi musu na shekaru aru-aru. Ƙasashen mutanen da kuma inda aka kai su sun fuskanci matsin tattalin arziki da rarrabuwar kawuna da ƙabilanci.

Ya kamata biyan diyya ya zama kamar tausasa zuuciya - a nemi gafara da biyan diyya ga baƙaƙen fata waɗanda aka tilasta wa kakanninsu aikin bauta.

Ƙudirin da Ghana ta gabatar ya buƙaci kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su yi la'akari da neman afuwar fataucin bayi da kuma bayar da gudunmuwar asusu biyan diyyar.

Carole Coles Henry holds a black and white photo of her great great grandfather Clem Coles as she stands in the backyard of her home in Phoenix, Arizona, US on 11 November 2022 in Phoenix, Arizona. Clem Coles was enslaved on the Coles Hill Plantation in Chatham, Virginia.

Asalin hoton, The Washington Post / Getty Images

Samuel Okudzeto Ablakwa, ministan harkokin wajen Ghana, ya shaida wa BBC cewa: "Muna neman diyya - kuma mun yi bayani cewa, shugabannin Afirka ba kansu suke nema wa wannan kuɗin ba.

"Muna son adalci ga waɗanda abin ya shafa da kuma ba su tallafi da ilimi - da kuma koya musu wasu ayyuka."

Amma Esther Xosei, wata mai sharhi a Birtaniya, mai fafutuka, ta nuna shakku game da yiwuwar tasirin ƙudurin.

"Abin farin ciki ne ganin yadda ƙasashen Afirka ke taka rawa a wannan tattaunawa, amma ba za a yi nasara a MDD ba," in ji ta.

"Babban ƙalubalen shi ne har yanzu ba a yiwa mutane bayanin abin da ke cikin tarihi ba."

John Mahama addressing the United Nations, standing at a podium in front of ta marble wall

Asalin hoton, United Nations

Shin an taɓa biyan diyyar bauta a tarihi?

Tabbas, ƙasar Jamus ta taɓa biyan diyyar bautar da ɗan'adam. A shekarar 1952, ƙasashen nahiyar turai sun biya sama da dala biliyan 80 ga Yahudawan a aka bautar ciki har da na Isra'ila.

Sai dai zuwa yanzu babu wata ƙasa da ta biya diyyar bautar da ƴan Afrika da wasu baƙaƙen fata,

Ko ƙasashen da suka nemi afuwa saboda hannunsu a fataucin bayi, irinsu Netherlands a shekarar 2022, sun ƙi yarda su biya wata diyya ta kuɗi.

Sai dai ita gwamnatin Jamus ta samar da wani asusun dala miliyan 230 domin samar da ayyukan jin daɗin jama'a domin tausasa zuciyar waɗanda aka bautar.

"Abu mafi muhimmanci shi ne, a gane cewa babu wanda yake ƙoƙarin canza tarihi, amma sai dai ana ƙoƙarin magance illar hakan a yanzu," in ji Dr Celeste Martinez, wani mai bincike kan ayyukan bauta a Afrika.

A black and white sketch of three slaves being restrained

Asalin hoton, Universal Images Group via Getty Images

Me Majalisar Dinkin Duniya za ta iya yi?

Ita kanta Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan a biya diyya ga waɗanda lamarin ya shafa. A watan Satumban 2025, babban kwamishin kare haƙƙin ɗan'adam, Volker Türk, ya ce ya zama "wajibi a biya diyya a kan irin wannan aiki".

Sai dai, ba a taɓa ƙada ƙuri'a kan wannan ƙudurin a babban taron majalisar ba, inda dukkanin ƙasashe 193 ke da ƙuri'a ɗaya.

Majalisar ba za a ta iya tilasta a biyya ba, amma za ta iya halasta hakan.

"Wannan babban mataki ne a siyasance, kuma ya kamata a tattauna shi a MDD," in ji Almaz Teffera, babban mai bincike kan wariyar launin fata a ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch.

"Hakan zai ba da damar tattaunawa tsakanin ƙasa da ƙasa, a kan batun biyan diyya da wasu damarmaki na ci gaba."

People calling for slavery reparations, protest outside the entrance of the British High Commission during the visit of the Duke and Duchess of Cambridge in Kingston, Jamaica on 22 March 2022

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Nawa ya kamata a biya?

Abin da aka fi tattaunawa a wannan batun shi ne, wa ya kamata ya biya diyyar kuma nawa?

Ana ta kiraye-kiraye ga kamfanoni da hukumomi da iyalai da suka yi amfani da bayi da su biya diyyar. Sai dai yawancin buƙatun, ana ɗora alhakin ne a kan gwamnati. A shekarar 2013, Caricom, wato haɗakar ƙasashen Caribbean, sun gabatar da wani daftari mai manufofi goma domin biyan diyya da adalci.

Buƙatun sun haɗa da yafe basussukan ƙasashen waje, da gina cibiyoyin kiwon lafiya da yaƙi da jahilci. A shekarar 2023, haɗakar ta gabatar da wani bayani da ke iƙirarin cewa ƙasashe 15 na bin bashin aƙalla dala tiriliyan 33 daga turawan mulkin mallaka.

"Gwmanati tana da laifi, saboda ta ba da dama an yi amfani da ita wajen yin fataucin bayi da mulkin mallaka," in ji Verena Shepherd, wani Farfesa a jami'ar West Indies.

Colourful boats float in front of the Elmina slave fort

Asalin hoton, Ullstein Bild via Getty Images

Patrick Robinson, babban mai shari'a a kotun ƙasa da ƙasa, ya gabatar da cewa ƙasashe 31 na bin bashin dala tiriliyan 107 daga ƙasashe irinsu Brazil da Amurka, waɗanda suka ji gajiyar bayin bayan sun samu 'yanci daga Birtaniya da Portugal.

Babban abin damuwa game da biya diyyar bautar shi ne yadda ake ɗaukar dogon lokaci. Saɓanin baya da ake biyan waɗanda abin ya shafa, tun a lokacin da suke raye.

John Dramani Mahama, President of the Republic of Ghana, walks toward a bilateral meeting during the 39th Ordinary Session of the Assembly of the African Union at the AU Headquarters in Addis Ababa on 15 February 2026.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Su wa suka nemi afuwar?

Masu hanƙoron ganin an biya diyyar irinsu Caricom, ba batun kuɗi kawai suka maida hankali a kai ba, har da buƙatar neman yafiya a hukumance daga ƙasashen da suka amfani da fataucin bayi.

Idan har ana son a tausasa zuciyar waɗanda aka bautar da su, ya zama wajibi ƙasashen turai su ba da haƙuri, in ji Verene Shepherd.

"Amma wasu sun fitar bayanan da na sani ne kawai. Irin waɗannan bayanan suna nuna cewa iyalai da waɗanda abin ya shafa ba su cancanci a ba su haƙuri ba"

Sara Hamood, mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam a Majalisar Dinkin Duniya, ta ce neman afuwar na da matuƙar muhimmanci idan har ana so a yi adalci.

"Maganar kuɗi wani sashe ne kawai na batun. Mun riga mun faɗa cewa babu wata da ta nuna nadama game da bautar da 'yan Afrika da kuma illar da hakan ya haifar." in ji ta.

"Neman yafiya a hukumance, da kaɓar gaskiya da bayyana abin da ya faru na daga cikin matakan da ake son a ɗauka."