Kwanton-ɓauna 10 da ƴanbindiga suka yi wa jami'an tsaron Najeriya a shekara biyu

Ƴanbindiga

Asalin hoton, NPF

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Talata da gabata ne ƴanbindiga da aka kyautata zaton ƴan Lakurawa ne suka yi wa sojojin Najeriya kwanton-ɓauna, inda suka kashe sojoji 13 tare da jikkata da dama a jihar Kebbi.

Harin ya faru a garin Giro-Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga, lamarin da ya faru a daidai lokacin da dakarun sojin Najeriya ke ƙoƙarin kai ɗauki bayan samun kira da suka yi daga al'ummar garin.

Hukumomi na cewa sojojin da aka kashe su11 ne sai kuma jami'in ɗansanda guda ɗaya sai kuma sauran waɗanda suka rasu da samun raunuka da suka haɗa da fararen hular da suka kasance tsakanin sojoji da Lakurawa yayin musayar wuta.

Kakakin ƴansandan jihar ta Kebbi ya shaida wa BBC cewa ba zai iya cewa uffan ba kan farmakin kasancewar abin da ya faru aiki ne na sojoji.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya kai ziyarar gani da ido zuwa wurin da al'amarin ya faru tare da zuwa asibiti domin duba wadanda suka samu raunuka.

Ko a watannin baya dai Lakurawa sun kai harin kwanton-ɓauna kan ayarin sojojin jagoran sojin runduna ta 8, duk da cewa sojojin ne suka samu nasarar fatattakar ƴanbindiga.

Amma me ya sa ƴanbindiga da Lakurawa suke iya kai hari kan sojoji da jami'an tsaro, kuma shin yaushe suka fara wannan.

BBC ta tuntuɓi Beacon Security and Intelligence Limited, inda shugaban kamfanin, Dr Kabiru Adamu ya rairayo wasu lokuta 10 da aka kai mumanan hare-hare a cikin shekara biyu.

Jihar Filato

A ranar 7 ga watan Yulin 2025 ne ƴanbindiga suka kai harin kwanton-ɓauna kan ƴan sa-kai a lokacin da suke ƙoƙarin farautar ƴanbindigar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar.

Maharan sun buɗe wuta ne, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, inda suka kashe ƴan sa-kai aƙalla 70, sannan kuma an ƙone gidaje da dama a lokacin.

Jihar Zamfara

A jihar Zamfara, a ranar 23 ga watan Yunin 2025, rahotanni sun bayyana cewa mahara da ake zargi ƴanbindiga daga dabar ƙasurgumin ɗanbindiga, Bello Turji sun yi wa jami'an tsaro kwanton-ɓauna a yankin.

Majiyoyin kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited wato BSIL sun tabbatar da harin, inda suka ce an kashe ƴan sa-kai 40 da sojoji 4, sannan maharan suke ƙone motocin soji.

Bayan wannan ne kuma Bello Turji ya fitar da bidiyon kashe tsohon ɗanbindga Mashari Maniya, wanda ya zarga da haɗa baki da jami'an tsaro.

Jihar Neja

A ranar 8 ga watan Afrilu ne mahara da ake kyautata zaton ƴanbindiga ne suka kashe ƴan sa-kai guda 30.

Maharan sun kashe ƴan sa-kan ne a garin Dogon Dawa da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kamfanin Beacon ya ce maharan sun ƙaddamar da harin ne kan ƴan sa-kan saboda ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da ƴanbindiga.

Jihar Zamfara

A wani harin daban a ranar 18 ga watan Fabrairun 2024, ƴanbindiga sun kai hari kan jami'an ƴansanda a ƙaramar hukumar Zurmi, inda suka kashe mataimakin babban hafsan ofishin sannan suka yi garkuwa da wasu mutane.

Maharan sun yi harin ne a matsayin ramuwar gayya bayan jami'an tsaro sun kashe wani ɗanbindiga.

Jihar Neja

Haka kuma a ranar 24 ga watan Yunin 2025, an kashe aƙalla sojoji 20 a wani hari da ƴanbindiga suka kai a kusa da garin Bangi da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Kamfanin Beacon ya ruwaito cewa maharan sun kai harin ne kan sojojin domin sansaninsu na matsu musu lamba.

Jihar Kaduna

A ranar 1 ga watan Janairun 2024, ƴanbindiga sun kai harin kwanton-ɓauna kan ƴan sa-kai, inda suka kashe guda 19 daga cikinsu.

Maharan sun kai harin ne bayan ƴan sa-kan sun kai ɗauki a lokacin da ƴanbindiga suka kai a gonaki da manoma, lamarin da ya haifar da rigima da faɗi mai zafi a tsakanin ɓangarorin biyu.

Jihar Bauchi

A jihar Bauchi, a ranar 4 ga watan Mayun 2025, wasu mahara da ake kyautata zaton ƴanbindiga ne suna kai harin kwanton-ɓauna kan mafarauta ƴan sa-kai a garuruwan Duguri da Gwana da ke ƙaramar hukumar Alƙaleri na jihar Bauchi.

A harin, an kashe ƴan sa-kai 19, ciki har da wasu ƴan ƙauyen Sabuwar Sara duk a jihar ta Bauchi.

Maharan sun ƙaddamar da harin ne biyo bayan ƙara ƙaimi da mafarautar suka yi wajen ƙoƙarin daƙile ayyukan ƴanbindigar.

Jihar Neja

Haka kuma a ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2025, mahara sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna, inda suka kashe aƙalla guda 17 daga cikinsu, duk da cewa an yi musayar wuta a harin.

Maharan sun kai harin a garin Kwanan-Dutse da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Maharan sun ɗauki matakin kai hari kan sojojin ne saboda sansaninsu na hana ayukan ɓanbindiga sakat.

Jihar Neja

A ƙaramar hukumar Wushishi ta jihar Neja, a ranar 13 ga watan Agustan 2023, ƴanbindiga sun kai hari, inda suka kashe sojoji aƙalla guda 21.

A ranar ma dai an yi gumurzu, inda aka yi ɗauki ba daɗi tsakanin sojojin da ƴanbindigar.

Jihar Neja

A jihar Nejar ɗai, mahara sun kai hari a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2023 a ƙaramar hukumar Rafi.

A harin ne ƴanbindiga suka samu nasarar kashe aƙalla ƴan sa-kai guda 13, sannan suka yi garkuwa da wasu ƴan sa-kan aƙalla guda 30.

Yawaitar hare-hare

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alƙaluman wata ƙungiyar ACLED mai sanya ido kan tsaro da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a wannan shekarar ta 2025.

To sai dai kuma kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce bisa alƙaluman da ya tattara, ƙungiyar Boko Haram ta kai hare-hare har sau 199 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Satumbar 2025.

Shugaban kamfanin Dokta Kabiru Adamu ya ce da dama masu nazarin ayyukan Boko Haram ba sa banbance tsakanin ƙungiyar da sauran ƙungiyoyi masu riƙe da makamai.

"Wani abu mai muhimmanci da masu bincike ba sa banbantawa shi ne akwai ƙungiyoyin da ba na Boko Haram ba da ke kai hari sai a kira su da Boko Haram. Misali akwai ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai amma ba sa iƙrarin jihadi, idan suka kai hari sai a yi kuɗin goro a ce Boko Haram," in ji Kabiru Adamu, Beacon Security and Intelligence Limited.