Ko rufe mashigar Hormuz ne ya sa farashin mai ya tashi a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
A daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran, hankali ya koma ne kan yadda lamarin ya shafi tattalin arzikin duniya bayan farashin makamashi ya tashi a sanadiyar yaƙin.
A wata tattaunawa da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya yi gargaɗin cewa idan yaƙin na Gabas ta Tsakiya ya ci gaba da ta'azzara, Najeriya za ta iya komawa yanayin kullen annobar Covid-19.
Dangote ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, inda ya yi kira ga ƴan ƙasar su yi addu'a, sannan ya buƙaci ƙasashen duniya su sa baki domin kawo ƙarshen yaƙin.
A cewarsa, "yanzu haka wasu ƙasashen sun fara umartar ma'aikatansu su fara aiki daga gida," in ji shi.
"Ina tunanin yanzu haka Indonesia aikin kwana huɗu kawai suke yi a mako. Sannan suna duba yiwuwar idan abubuwa suka ci gaba da rincaɓewa, za su buƙaci ma'aikata su fara aiki daga gida. Za mu koma tamkar lokacin Covid-19, inda mutane suke aiki gida gida," in ji Dangote.
Sai dai ya ce babbar matsalar ita ce wasu mutane za su yi ƙoƙarin cin moriyar lamarin.
"Za su ga ai lokaci ne na samun kuɗi. Don haka idan ba a samu zaman lafiya ba, farashin zai ci gaba da tashi ne, sannan kuma gefe guda gwamnati ba za ta yi ta ƙara albashi ba."
A yanzu haka farashin man fetur ya zarta dala 100 kan kowace ganga a kasuwannin duniya.
Me ya sa farahin ya tashi a Najeriya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Najeriya, ƙasar da ke yammacin Afirka na samun fiye da kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta ne daga man fetur da iskar gas da take sayarwa a kasuwannin duniya.
Galibi kuɗaɗen da Najeriya ke amfani da su a kasafin kuɗinta tana samu ne daga arzikin man fetur da take sayarwa
Don haka ne ma a duk lokacin da shugabannin ƙasar ke gabatar da kasafin kudin ƙasar, sukan yi ƙiyasin kuɗin da ƙasar za ta samu daga man da take sayarwa.
A watan Disambar bara, lokacin da shugaban ƙasar, ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2026, ya ƙiyasta shi kan dala 64.85 kowacce gangar mai da ƙasar za ta sayar.
To sai dai a yanzu da farashin kowace gangan ya haura dala 100, masana tattalin arziki na ganin hakan riba ce ga Najeriyar, wadda a yanzu farashin ya zarta ƙiyasinta.
Hakan ya sa ake tunanin ƙasar riba za ta ci samu daga yaƙin na Iran, saboda aƙalla za ta riƙa fitar da manta tana sayarwa.
Farfesa Adamu ya ce a yanzu kowace ganga da ƙasar za ta sayar za ta samu ribar kusan dala 36.
Kasafin kuɗin ƙasar ya kuma ƙiyasta haƙo ganga miliyan 1.8 a kowace rana.
''Ke nan a kowace rana Najeriya a yanzu na samun ribar dala miliyan 64, ƙari a kan abin da ta yi hasashen samu a kowace rana, sanadin sayar da mai'', in ji malamin jami'ar.
Sai dai ba nan gizon ke saƙa ba, domin a daidai lokacin da ake murnar Najeriya za ta riƙa samun kuɗaɗen shiga, farashin man ne ya yi tashi gwauron zabi a ƙasar, lamarin da ya ƴan ƙasar suke tambayar ina matsalar take?
A game da wanan, Farfesa Ahmed Adamu ya ce ɗanyen mai kasuwarsa ta duniya ce, "ko a ina aka samo shi, dole a saita farashin da na duniya. Misali Iran tana kashe tsakanin dala 10 zuwa 15 a kowace ganga wajen samarwa, sannan ta sayar a sama da dala 100."
Masanin harkokin makamashin ya ce ko da tsada ko da arha aka samar da shi, dole da farashin duniya za a sayar.
"Ba kamar kayan masarufi ba ne, da za ka lissafa abin da ka kashe, sai ka ɗaura riba ka sayar. Akwai ƙasashe ma waɗanda saboda suna samar da man da tsada ne, idan misali ɗanyen mai ya sauka ƙasa da dala 50 sai ya zama asara suke yi saboda suna kashe sama da haka wajen samarwa," in ji Farfesan.
Ya ce a Najeriya ma haka abin yake, "idan aka samar da man, yanzu ana sayarwa ne a farashin sama da dala 100. Don haka dole idan za a sayar wa Dangote a sayar masa a wannan farashin."
Masanin ya ce a baya ƴan Najeriya ba su cika jin raɗaɗin hawa da saukan farashin man fetur ba ne saboda tallafin man fetur, "amma da aka cire tallafin, shi ne ƴan ƙasar suke ƙara fahimtar yadda kasuwancin mai yake."
Alaƙar farashin da rufe mashigar hormuz
Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne.
Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a kullum ta tekun.
Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.
Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.
Farfesa Ahmad Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur da iskar gas da ke jami'ar Philomath da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ya ce hanyar ruwa ce da ba ta girma sosai, amma take da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
"Ita wannan mashiga hanyar ruwa ce wadda tsayinta bai wuce kilomita 33 ba, wadda ta a daidai ƙasar Iran. Kuma hanya ce da jiragen dakon ɗanyen man fetur ke wucewa a kullum."
"Kullum ana wucewa da gangar ɗanyen mai kusan miliyan 20. Kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai da ake buƙata a duniya," in ji shi.
A matsayin martanin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata, Iran ta rufe mashigar ta Hormuz.
Ya ce rufe mashigar na nufin ana rasa aƙalla ganga miliyan 20 na mai a kullum, "sannan duk abin da ya yi ƙaranci yana ƙara tsada. Kuma mashigar ta rufe mai da ke da arha daga Gabas ta Tsakiya. Yanzu haka an fara taƙaita amfani da motoci a wasu ƙasashe yankin Asia," in ji Farfesa Ahmed.











