Idi ko Juma'a? Fatawar malamai kan haduwar Idi da Juma'a
Kamar a wasu shekarun baya, a bana ma sallar Idi ta fado ranar Juma'a sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a ranar Larabawa wato 29 ga watan Ramadana.
A duk lokacin da aka samu irin wannan haduwar ko kuma karo tsakanin sallolin Idi guda biyu wato na sallah da Juma'a, al'ummar Musulmi kan shiga halin ruani dangane da yadda za a gudanar da Idi a irin wannan yanayi.
BBC Hausa ta tattauna da fitattun malaman addinin Musulunci guda biyu a Najeriya domin samun mabanbantan ra'ayoyi kan yanayi.
Mun tattauna da Sheikh Ahmad Mamhud Gumi da Sheikh Halliru Maraya a 2023, inda malaman biyu suka kawo fatawowyi da fahimta daban-daban dangane da wannan rana.
Fatawar Sheikh Gumi

Asalin hoton, BBC/Grab
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, malamin addinin Musulunci ya ce idan Idi ya dace da ranar Juma'a to Musulmi na da Idi guda biyu.
"Idan an samu Idi ya zo ya dace da ranar Juma'a to Musulmi na da taro guda biyu. Taron idi da ake yi duk shekara-shekara sannan kuma akwai haɗuwa ta ranar Juma'a.
Kowacce ibada ce daban ba tare da an haɗa ta da wata ba. Sai dai waɗanda Juma'a ba ta wajaba a kansu ba waɗanda suke mutanen ƙauye, mutanen nesa kamar mutanen al'awaali ko kuwa al'aliyaa waɗanda ke barin ƙauyukansu su zo Madina sallar Idi to waɗannan an ba su rangwame cewar ba sai sun koma Madina sallar Juma'a ba.
Ba a ɗuke musu sallar Azahar ba kamar yadda muka ji wasu na faɗa cewa wanda ya zo sallar Idi ka da ya je sallar Juma'a. Wannan fahimtar kuskure ne. Sai dai kuma idan akwai larura kamar tafiya ko rashin lafiya." In ji Sheikh Ahmad Gumi.
Ra'ayin Sheikh Halliru Maraya

Asalin hoton, Facebook/ Halliru Maraya
Sheikh Halliru maraya wanda malamin addinin Musulunci ne a Kaduna ya ce al'amarin ba na rikicewa ba ne.
"Irin wannan abu ya taɓa faruwa lokacin manzon Allah kuma abin da annabi ya yi shi ne ya je Idin kuma ya je masallaci ya gabatar da sallar Juma'a. A lokaicn da aka yi salalr Idi sai ya ce yau ne sallar Idi kuma mun yi Idi kuma game da sallar Juma'a duk wanda yake so zai iya sallar Juma'a amma mu dai za mu yi sallar Juma'a ɗin"
"Saboda haka babban abin da ya dace shi ne mutane su dage su yi sallar Idin sannan kuma su yi sallar Juma'a. Wannan shi ne abin da ya kamata."
"Akwai magana kuma mai raunin gaske da ke cewa idan mutum ya yi sallar Idi to wai da Juma'a da Azahar ɗin duk sun faɗi. Amma wannan malamai kaɗn ne suka yadda da ita saboda tana da matuƙar rauni."











