Hanyoyi biyu na ramuwar azumi

Asalin hoton, Getty Images
Addinin Musulunci ya tanadi hanyoyi guda biyu na ramuwar azumin watan Ramadana ga waɗanda azumin ya kuɓucewa bisa wasu dalilai.
Hanyoyin guda biyu su ne Kaffara da Ramako.
Mece ce kaffarar azumi?
Sheikh Abu Qatada Muhammad ɗaya daga cikin limaman masallacin Juma'a na Usman bin Affa da ke Gadon Qaya a birnin Kano, ya ce Kalmar kaffara na nufin wata ibada da Allah ke wanke bayinsa daga wani zunubi da suka aikata.
''Kaffara na nufin wanke zunubi ko laifi, wato ka aikata laifi kaza, to ka yi kaza sai ka wanke kanka daga laifin da ka yi,'' in ji malamin.
Akwai abubuwan da haifar da kaffara a lokacin azumin watan Ramadan, kamar yadda malamin ya yi bayani.
- Cin abinci ko abin sha da gangan a lokacin da azumi ke bakin mutum
- Kusantar iyali da gangan kuma da rana
- Ƙaƙaro amai da gangan
- Wasa da al'aura domin biya wa kai buƙata da gangan
- Tsoho ko tsohuwar ba za su iya yin azumin watan Ramadan.
- Mai shayarwar da ta ajiye azumi.
Yaya ake kaffarar azumi?

Asalin hoton, Getty Images
Malamai sun yi bayanin cewa yadda ake yin kaffara ya dangatan ga dalilin da ya janyo wa mutum kaffarar.
- Ƴanta baiwa: Sheikh Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin Juma'a da ke garin Okene ya ce ga wanda ya sadu da iyalainsa da rana cikin watan Ramadan, kaffarsa shi ne ''ƴanta baiwa, idan hakan bai samu ba to sai ya yi azumin wata biyu, in hakan ma bai samu ba to sai ya ciyar da miski 60, kamar yadda ya zo a hadisi.
- Azumin wata biyu: A cewar Sheikh Abu Qatada Muhammad duk mutumin da ya ci ko ya sha da gangan da rana cikin wata Ramadan, ko kuma ya ƙaƙaro amai da gangan a lokacin da yake azumi. ''Zai yi azumin wata biyu ko kwana 60 a ajere ba tare da tsallake ko da kwana guda ba, domin wanke kansa daga laifin da ya aikata'', in ji limamin Juma'ar.
- Ciyarwa: Abu Qatada Muhammad ya ce wani nau'in kaffarar shi ne ciyarwa maimakon ramako. ''Wannan ya shafi tsoho ko tsohuwa ko kuma majinyacin da ya yanke ƙauna daga warkewa'', in ji shi. Ya ƙara da cewa abin da rukunin waɗannan mutane za su yi na kaffara shi ne su ciyar da mutum guda a kocewa rana da ya kasance ba su yi azumin ba. ''Za su iya ciyarwa da abinci dafaffe, ko ɗanye, kuma sau ɗaya za su ciyar da miskini guda a akocewa rana a madadin azumin wannan ranar da ba su yi ba'', a in ji shi.
- Ciyarwa da azumi: Malamin ya ce ga mace mai ciki ko mai shayarwa da ta ajiye azumi, kuma ganganci ya sa ba ta rama ba, har wani Ramadan din ya zagayo, to bayan wucewarsa idan zai rama shi, duk guda da ya yi sai ya ciyar da miskini, kamar yadda malamin ya yi ƙarin haske.
Ramuwar azumi
Ramuwa ko ramako kamar yadda limamin Juma'ar ya yi bayani shi ne rama azumi guda da wani dalili ya janyo karyewarsa.
Yadda ake yin ramuwar azumin da ya kuɓucewa mai azumi shi ne, amadadin kwanakin da ka sha azumin.
Malamin ya ce ana iya kwanakin da kaɗai ka sha azumin za ka rama, ba tare da ƙari ko ciyarwa ba.
''Kamar yadda nassin alƙur'ani ya bayyana cewa ku rama iya kwanakin da kuka sha azumin'', a cewa malamin.
Ya bayyana wasu abubuwa ko uzurorin da ke janyowa mai azumi ramako, kamar haka:
Dalilan da ke janyo ramuwar azumi

Asalin hoton, Getty Images
- Rashin lafiya: Wannan nassi ne ƙarara ya zo da shi daga al'qur'ani mai girma cewa duk mutumin da ba shi da lafiya to ya ajiye azumi daga baya ya rama shi, a cewar malamin.
- Tafiya: Kamar yadda nassi ya ambaci rashin lafiya, haka nan ya ambaci tafiya, kamar yadda malamain ya bayyana. Duk mutumin da yake da uzurin tafiya halastacciya to musulunci ysa ba shi damar ajiye azumi kuma daga baya sai ya rama adadin ranakun da ya sha azumin a lokacin tafiyar.
- Zuwan jinin al'ada: Ga mata masu al'ada su ma musulunci ya yarje musu su ajiye azumi a duk lokacin da jinin ya zo musu, da kuma tsawon kwanakin da za su ɗauka suna jinin. ''Daga baya kuma sai su rama adadin kwanakin da suka sha azumin bayan sallah'', kamar yadda ya yi bayani
- Mace mai ciki: Ita ma mace mai ciki wasu malaman suna bayar da fatawar ta ajiye azumi idan cikin yan ba ta wahala, daga baya sai ta rama, kamar yadda ya yi bayani.












