Me ya sa sarakunan Masar suka yi amfani da gadaje masu ƙarfi?

Lokacin karatu: Minti 5

A can yammacin tsibirin Orkney da ke Scotland, wani daɗaɗɗen ƙauye mai suna Skara Brae wanda aka manta tsawon shekara 4,500 da suka wuce. Gidajen ƙauyen masu ɗaki ɗaya-ɗaya na ƙewaye da katangu masu ƙarfi haɗe da ciyayi da kuma hanyoyi da aka yi da duwatsu.

Sai dai a nan, abubuwa biyu da ke cikin gidajen abu ne da aka san a zamanin yau - wato gadaje.

Gidajen a ƙauyen Skara Brae da ke arewacin Scotland suna kama da juna, inda ɗaki guda ke da tsawon mita 40, wurin hura wuta na girki ko wani abu da kuma kayayyakin tarihi.

Akwai kujeru guda biyu wanda suka kai tsayin mutum, haɗe da tebura da kuma wuraren ajiya.

Kamar sauran kayayyaki da ke wannan tsibiri, waɗannan gadaje na tarihi an ƙera su ne da dutwasu masu ƙarfi.

Za ka iya gane su da wuri cewa gadaje ne waɗanda za ka iya jingina kanka a kai.

Idan aka yi la'akari da tsoffin rubuce-rubucen da aka samu akan wasu daga cikin gadajen da kwarangwal ɗin da aka sanya a ƙarƙashinsu, muna iya tunanin cewa an yi ƙera su ne tun kusan ƙarni na 21.

Ɗan'adam ya shafe dubban shekaru yana ƙera gadaje. Masanin ilimin halin dan adam, Brian Fagan da masaniya kan nazarin tarihin ɗan,'adam, Nadia Durani na Jami'ar California, Berkeley, sun bayyana yadda aka samu hakan tun da farko a cikin littafinsu 'What we did in bed: a horizontal history'.

Kusan dukkan abin da ke rayuwa sun yi amfani da ganye mai laushi, wanda ƙwari ba sa ratsa shi wajen shimfiɗawa ƙasan gadajensu, inda ta haka ne aka fara samun shimfiɗa ta gadaje.

Gadajen ƙasa a ƙauyen Skara Brae da kuma Durrington kusa da Stonehenge na cikin abubuwa masu daɗaɗɗen tarihi a duniya.

An fara ganin gadaje a sassan duniya shekaru 5,000 da suka wuce, bayan zuwan ƙere-ƙere da kuma rubuce-rubuce.

Ganin gadaje a kusa da wurraren bizin a tsibirin Orkney a Malta, mai nisan kilomita 1,700, ciki har da mutum-mutumin wata mata kwance hannunta a kanta, alamu ne na gadaje a zamanin da ya wuce.

Fagan da Durrani sun bayyana cewa a can baya, waɗannan gadaje ba wuraren hutu ne kaɗai ba. Suna ɗauke da alamomi na abubuwa kamar bayan rayuwa.

A tsawon dubban shekaru da suka wuce, an yi ta samun ire-iren gadaje daban-daban, la'akari da al'adu da kuma rayuwar mutane.

Wannan maƙala ta duba tarihin gadaje a ƙasashen yamma.

Tsarin kwanciya a tsohuwar Masar

Lokacin da Howard Carter ya shiga kabarin Sarki Tutankhamun a shekara ta 1922, ya samu abubuwa da yawa da aka yi da zinare masu sheƙi, ciki har da gadaje shida.

Akwai abubuwa da suka haɗa da gadon jana'izar da aka yi wa ado kamar Mehet-Veret, gunkin shanu, gadon katako da aka karkata, da gadaje da ake nannaɗewa waɗanda ake amfani da su yayin tafiya.

Yawancin gadaje na zamanin Masar a da, an yi su ne don masu hannu da shuni. Yawancin gadajen sarki Tutankhamun suna da katako da katako da aka saka da igiya ko siliki.

Kamar yadda al'adar zamanin, sarakuna su kan yi barci da daddare inda suke saka kawunansu a kan wani abu mai tsayi, maimakon matasan kai masu laushi.

Ana amfani da wannan hanya sau da yawa a lokacin zafi yayin da yake inganta yanayin iska.

Ƴan tsohuwar Masar, ciki har da kakar Sarki Tutankhamun, sun yi amfani da irin wannan gadon don kare kawunansu.

Romawa a da sun yi gadaje daban-daban ga kowa

A zamanin Romawa na baya, kamar yadda yake cikin al'ummomi da yawa, wuraren da mutane suke kwana sun dogara da matsayinsu na zamantakewa.

Mutane marsa galihu a cikin al'umma, kamar bayi, suna kwana a kan busassun ganye, fatan dabbobi, ko a ƙasa. A nan ne wasu suka fi yin barci cikin kwanciyar hankali.

A shekarar 2021, masana tarihin ɗan'adam sun tono wani tsohon gida a Civita Giuliana, wani yanki na birnin Pompeii na Romawa, lokacin da suka gano wani ɗakin kwana da ba a yi amfani da shi ba kusan shekaru 2,000.

Akwai gadaje guda uku da kayayyaki, akwatunan katako, da sauran abubuwa, har ma da tuluna a ƙarƙashinsu.

A ɗaya ɓangaren kuma, masu kuɗi na da gadaje da suka wuce wurin kwana kaɗai.

Romawa sun ƙirƙiri nau'ukan gadaje iri-iri don dalilai daban-daban. Waɗannan sun haɗa da gadajen karatu, na sababbin ma'aurata, na mutane su taru su ci abinci, da kuma gadajen barci.

Sun kuma yi wasu gadaje na musamman don jana'iza. Waɗannan gadaje sau da yawa suna da wani dandali da aka yi da ƙarfe da katifa mai siririn gaske.

Irin katifun da aka yi amfani da su a Turai a da

A karni na 17, Turawa suna da gadaje iri-iri. Akwai gadaje na akwati, gadaje na igiya (wanda dole ne a danne igiyoyin a koyaushe), da kuma manyan gadaje ɗauke da gilasai guda huɗu, irin su Great Bed of Ware, wanda zai iya ɗaukar mutum 52.

Amma ɗaya daga cikin muhimman gadaje na farko na zamanin shi ne 'katifu'.

Ana samar da katifun ta amfani da kayayyakin saƙa. An cika su da abubuwa iri-iri, daga gashin fuka-fukai zuwa bambaro.

Abubuwan da ake amfani da su a gadajen na iya shafar ingancin barci.

A cewar wani littafi mai suna: A History of Night Time, wani matafiyi da ya bi ta ƙasar Switzerland a shekara ta 1646 ya yi ƙorafi game da yadda ƙarar ganyen ke shafar fatarsa ​​a cikin dare bayan ya kwanta a gadon da ke cike da ganye.

Waɗannan katifun sun kasance wurin haifuwar kwari da yawa. A zamanin da, mutane suna fama da cututtuka saboda sun raba gadaje da mutane da yawa, ciki har da baki.

Gadaje masu igiyoyi a Ingila

A ƙarni na 17, rashin daidaito ya kai kololuwa a Ingila. Masu aiki suna shan wahala wajen samun abin dogaro. Wannan haɗe da ƙaruwar al'umma cikin sauri, ya janyo mutane da dama rasa wurin zama.

A birnin Landan, ƙungiyoyin agaji sun ɓullo da wasu dabaru na daban. Ɗaya daga ciki shi ne "gadaje masu kama da akwatin gawa" - wanda mutane ke kwana a ciki da daddare wanda bai wuce fam huɗu ba. Wani kuma shi ne gadajen da ake yi da igiyoyi kan fam biyu.

A nan, ɗaruruwan mutane na zama a kan benci sannan su yi barci kansu a kan wani dogon igiya. Da safiya, za a yanka igiyar ba tare da la'akari ko da mutane na barci ba.

Wannan ne ya sa gadaje masu "igiyoyi" suka samo asali.